← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 139

Sashe 23

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*shettima*
cike da tunanni iri iri a ransa yaqarasa gida horn yayi ne gadi ya wangale masa gate shikuma ya danna hancin motar ya shiga ciki parking lot ya nufa bayan yagama daidaita parking ya fito yanufi cikin gidan yana shiga yaga babu kowa afalon yana qoqarin nufar dakin hajiyar sa sai gata tana saukowa daga upstairs tana ganin sa ta fadada fara'ar fuskarta tana sakin murmushi ganin tilon danta tanajin tausayin sa kodan rasa mahaifin sa dayayi shiyasa akullum sonshi yake qara nunkuwa cikin ranta ganin tana murmushi shima yasahi kawar da duk wani tunani da yazo dashi ya ajiye shi gefe da murmushin shima tunkan taqaraso yaqarasa inda take tare da yin hugging din ta sannan yace hajiya what happened ne naga kina ta smiling wani taqara saki tace ba dole inyi smiling ba nasamu 'ya mace wlh bakaji yanda naked jin dadi ba tunda muka dawo kasan me nayi mamakin yarinyar nan yanda ta saki jikin ta dani kai kace daman munsan juna sosai tare ma muka shiga kitchen mukayi girki nayi mamakin yanda naga ta iya abubuwa wani yau girkin kanwarka zakaci wani rin murmushi yake ta faman saki tunda tafara bashi labarin yake jin wani dadi na ziyartarsa cike da zumudin ganin ta yace hajiya tana ina hajiya tace ai har ta kwanta tayi bacci kasan jikin ta ba wani lafiya ne dashi ba shiyasa da tan tayani nace tayi wanka ta kwanta bayan taci abinci tundazu fa ta kwanta yace gaskiya banji dadin kwanciyar ta ba naso nadawo naganta kafin na kwanta dan hararar wasa hajiya tayi masa tace to meye abun damuwa aciki bayan muna tare inbaka ganta yanzu ba ai zaka ganta gobe ganin ta har sai kagaji ai tana rufe baki yace wlh hajiya bazan gaji da ganin taba nifa badan badan bama daki daya zamuna kwana idan natashi kuma mutafi aiki tare mu dawo tare baki hajiya tasaki tana kallon sa sannan tace nikuma sai abarni nikadai daman kwa bazan taba yarda ba nifa yarinyar nan koda komai ya daidaita zan roqesu subarta tace gaba da zama awajena har zuwa lokacin bikin ta shine kawai zai rabani da ita in sha Allah nasan bazasu hanani ba yace to Allah yasa ai hajiya ko tayi auren ma kuna tare ba inda zata tace dake shi mijin yace maka zai yarda yadawo nan da zama inama kataba jin inda a kai haka yace ai dolen sama ya zauna yana da inda yafi kusa dake ai ba inda zasu kuna tare dasu daga ita har mijin yana gama fada yace bari indan watsa ruwa inzo inci abinci baby sai yanzu ta dan fahimci zancen sa murmushi kawai tayi bata ce masa komai ba itama ta wuce kitchen abincin masa ta hado masa bata kai dinning ba kawai sai ta ajiye masa akan center capet din dan daddare befiya cin abinci akan dinning ba yafiso ya zauna aqasa yayi balance yanda zaifi cinsa da yawa yaci ya qoshi saboda baya wasa da cikin sa akwai cin abinci bare kuma idan ya kwaso yunwa ba a magana sai yaci abincin kusan mutum biyu shikadai tana gama jere masa ta zauna awajen tana jiran fitowar sa......

Sam & Ammah

Saida yadan qara gyara zama tare da miqa duka hankalinsa gare ta sannan yace Ammah wata tambaya zan miki ko Allah zaisa kin sani tace ina jinka yace yanzu idan akace na kusan kusanka wa ake nufi kenan saida ta dan numfasa sannan tayi murmushi tace yanzu wannan har wata tambayace kaima ai zaka iya bawa kanka amsa yace Ammah da nasani ai bazan tambayeki ba tace to idan akace na kusan kusanka kamar ace mahaifiyar ai kaga itace ta kusa dakai to ba ita sai ace hasanarta ko kuma mahaifanta kaga su sune nakusan ta ita kuma itace ta kusanka kagane dan jimm yayi yace eh nagane to amma idan akace kuma zaku hada alaqar jin fa kinga kamar ba mahaifiya ake nufi ba tunda ita daman already jininku daya ba wata alaka da zaka hada da ita tace eh hakane tode wannan tambayar taka bandan fahimcekaba kaimin bayani dalla dalla dan har kaqara rikitani gyara zama yayi ya fuskance ta da kyau sannan yace yanzu alal musali ace bansan kiba ke kuma kin sani sai kikazo wajena fuskarki a rufe amma da ace kin bude zan iya sanin ki tunda nasanki abaya saidai rufe fuskar da kikayi yasa bangane kiba sai kawai kika zomin da wata bukatar ki wacce kike tunanin bazan iya ba amma sai kikace zaki bani kudi makude atake alokacin kika turamin kudade nikuma tsoro yasa nace miki na amince sai kike cewa idan banyi ba kinsanni farin sani kinsa gidan mu idan na kuskure tofa duka family na sai sunshiga wani hali hakan yasa nace na amince amma kifara gaya min ko wacece ke sai kicewa ai nima nasanki kece ta kusan kusana wanda zamu hada alakar jin nan da 'yan wani watanni kuma kika gargadeni akan kar inzafafa tunanj wajen gano ko wace saboda shima zaizame min matsala gwara kawai inyi aikin da kikasani idan ina son kwanciyar hankali sai nazo zancire miki abun da kika rufe fuskar sanadin hakan danyi kuma bangama ganin kiba kuma banqara sanin inda kaina yake ba sai agadon asbiti to kinji yanda abun yake kin gane yanzu tace eh na fahimceka sosai amma wanna amsar taka kabari ba yau ba sai nayi nazari sosai dan marairaicewa yayi yace plss Ammah ki gayamin yanzu kawai abune emergency nasan zaki iya mekika fahimta acikin wannan maganar bakajin hausane abun da na fahimta dinne ai nace kabari idan nayi nazari zan gaya maka shiru tayi na dan wani lokaci sannan tace kafin ma ingaya maka kaiwaye yayi maka wannan tambayar ko a ina kaji labari dan shafa kansa yayi tare da dan cizan lower lip dinshi sannan yace Ammah wannan ba abun da yashafeki bane kawai amsa ake nema daga gareki idan komai ya tafi yanda akeso zakiji komai ta danji haushin maganrsa amma sai ta danne bata bari bacin ran yafito ba tace masa ok kawai sannan ta miqe tsaye tace sai kaji daga garene shima da sauri ya miqe tare da qarasawa gare ta yace dan Ammah na daga nan zuwa gobe ki taimaka kigama nazarin kigaya min kai kawai ta daga masa alamar to daga nan ta nufi dakinta shi kuma ya fita daga falon tare da nufar sashen Fulani inda zai kwanta saboda yaga dare yayi atunanin sa kowa ya kwanta shiyasa ma be tsaya wani yin nocking ba kawai yatura qofa yashiga kai tsaye hajiya sarah inason ganinki agidana tun lokacin da kika tafi ka barni cikin duhu haryanzu nakasa fahimtar inda maganar ki ta dosa tun alokacin nake taqara trying number ki amma bata shiga me yafaru ne abun da yaji fulani nacewa kenan itama jin kamar motsin mutum yasa ta dagowa daga kan kujerar da take idanunta suka sauka akansa bata jira amsar da za abata ba kawai ta datsi wayar tare da miqewa gabanta na dan dukan uku uku tana tunanin Allah yasade baiji abun da take cewa ba wata zuciyar tace to meyema idan yaji ai ba gane abun da take cewa zaiyiba tuna hakan yasata sakin murmushi tare da qarasowa kusa dashi tace tunyaushe kashigo daman kai naked jira shiyasa na zauna anan tunda naga alamar kwana biyun nan baka son zuwa inda naked be tanka Mata ba saima wani kallo me cike da ma'anoni da ya wtmatsamata da yasa saida takawar da idonta daga garesa bece mata komai ba ya raba ta gefenta ya wuce sashen sa yabarta agun atsaye tana takaicin kallon da yayi mata da kuma kin kulatan da yayi kamar wacce aka dasa agun haka ta tsaya tana tunani kala kala saida ta dau wajen minti uku agun batare da tayi wani kwakwaran motsi ba sannan ta girgiza kai tayi gaba tare da cewa dani kake zancen zan saita maka zama acikin gidan nan baka san halina bane labari na kake ji

cike da takaicin wulakancin da yayi mata naqin kulatan dayayi ta nufi dakin ta da tunanin abun da zatayi masa acikin ranta,
shikam anasa bangaren bema san tanayi ba dan dagaske bai fahimce me take cewa ba saboda tsakanin su da yar tazara shiyasa kawaide yaji tana magana amma baya tantance abun da take fada abun da yabashi haushi da har yagane duk yanda akai abun da take fada bana alkhairi bane dana alkhairi ne ai bazatayi saurin katse kiran ba daga ganin sa dalilin da yasa yaqi kulata kenan yayi wucewar sa daman yanzu ba wani dasawa suke ba tunda yagane take taken ta ya fit a harkarta gaba daya,
yana qarasawa dakin sa ya hau cire kayan jikin sa ya fada bathroom be dau lokaci ba yafito jikin sa daure da towel sai guda daya kuma da ya nannade gashin kansa dashi guri yasamu ya zauna gaban dressing mirror sannan ya kunce towel din kansa ya qara goggogewa sannan ya dauki lotion ya shafe jikinsa tareda turaruka nide tsaye nayi ina kallon ikon Allah sai kace amarya zata gurin me gida anaso aburge shi haka shima yake tafaman shafe shafe da murtsike murtsike yadau wannan ya shafa ya ajiye yadau wancan harda shafa wani abu akan lips din shi da nidai yau nafara ganin sa a hannun sa tunda akahaifeni aduniya ban taba gani ba saida yagama tsaf sannan ya mike yaje gaban slyzing drawer bayan ya bude ta yadauko wasu kaya marasa nauyi yasaka sannan yaje yadauko fresh milk a fridge din dak in ya dan sha kadan sannan ya mayar sannan ya haye kan tamfatsetsen gadon sa tare da jan lausassan blanket dinshi ya rufe duka jikin shi dashi amma banda fuska lumshe kyawawan idanunsa yayi ko addu'ar bacci beyiba yayi kwanciyar sa some times daman bata dameshiba abunde dana lura dashi kamar yana da dan qarancin yawan ibada ahaka yayi kwanciyar cikin qanqanan lokaci bacci yayi awan gaba dashi asuba tagari,

Washe gari
Chapter 23 · 0% Book details