← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 139

Sashe 89

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafin shettima yace wani abu sam yayi sauri ya  bude motar sa yashiga yana shiga kuma yasata a louck yana masa murmushi sannan ya zuge bakin glass din motar yana daga masa hannu tare da tayar da motar yaja yabarsa agun atsaye kamar gunki dan yau sameer yagama gaya masa maganar da baitaba ji yayi irin taba yabasa mamaki,

bossay ma saida yayi masa dariya sannan yace sai anjima ade bi ahankali kar awuce da abun kunya azo ana dana sani kar ka cuci yarinyar mutane de kabarta kuma kade ji ba dadewa zamuyi ba dan haka kayi ka koma dan nasan amatse kake dan ana kallon idon ka za agane ba lafiya kake va nidai inkara baka shawara kar awcu gona da iri ayi komai baya baya,

da sauri shettima yayi kansa zai kaimasa nausi yayi saurin matsawa tare da shigewa mota shima yana masa dariyar mugunta yacewa driver yasaka motar a louck sannan ya tayar haka kuwa driver yayi shima yana yar dariyar sa kasa kasa dan yagane hirar da suke yi yasan me suke nufi tayar da motar yayi yaja suma suka tafi bossay harda lokowa ta windo yana kara tsokanar sa,

shettima kamar ya nutse agun haka yake ji wai har bossay ma yasamu damar yi masa irin wanna zancen aikwa zasuyi bayani wallahi duk sai yarama abun da sukayi masa daya bayan daya sai yarama sai sunyi danasanin wannan abun da sukayi masa yau shi zasu gayawa magana irin wannan kuma sugudu yama fasa tafiya gida zai koma yajirasu su dawo takan sameer zai fara sai ya kunce mai zani agaban kowa da kowa bade yana da videon sa ba yana daukar mace to wallahi ha momma sai ya nunamata yaga karshen rashin mutuncin irin nasa shikuma bossay zai duba yaga ta inda zai rama dan shi nasa magan ganun ma sunfi na sameer zafi zai sanine shima sai yagane bashi da wayo in yasakasu gaba sai yasa duk sun tsani kansu dan bazai raga musu zai hada da karya da gaskiya da abun da yafaru da abun da bai faruba ma duk sai ya hada yagayawa mutane da sukeyi.....,,

yana wannan tunanin  har yakoma part din fulani yan shiga falon ya shiga rarraba ido ko zai ganta amma bai gantaba tunawa yayi da tashi ga kitchen dazu dan haka kansa tsaye bawata fargaba ya tura kofar kitchen din ya su biyu  ya gani aciki ita tana wanke wanke dayar kuma tana girki saida yagama karewa bayan ta kallo sannan yadan yi gyarab murya atare suka juyo suna kallon sa gaban Azeema ya shiga dukan uku uku shikenan yanzu ba damar guduwa yakata, dayar kuma tunda tasanshi kamar dan gida yake awajen kowa yanda za agirmama dan gidan shima haka suke girmama shi dan haka da sauri ta tsugunna ta gaidashi sanna ta shiga tambayar sa abun da yake bukata yace mata ba komai tana ta mamakin abun da yakawo sa kitchen din kuma yace babu abun da yake so to me yakawo shi har ta juya zata cigaba da aikin ta ya kira sunan ta tana amsawa yace mata in badamuwa kidan ban guri kifito waje,

da sauri tace babu komai ita duk tunanin ta bai bata gurin dayar yazo tayi tunanin idan ta fito zace Azeema ma tafito amma sai taga tana fita daga kitcshen din ya mayar da kofar ya rufe da mamaki tayi tayi tsaye abakin kofar tana tunanin to me zaiyiwa yarinyar aikwa bazata bari wannan labarin ya wuce uwar dakin taba da sauri ta juya ta nufi dakin fulani dan ta sanar da ita abun dake faruwa tazo ta ganewa idon ta da kanta gani da ido yafi abaka labari.......

Suna karasawa unguwar bossay  yace ya sauke sama akofar gida ya gode a kofar gida aka saukesa ya kwankwasa me gadi ya bude masa ya shiga ciki shikuma drivern ya juya yatafi,

da sallama ya shiga falon gidan nasu amma babu kowa afalon dakin Ammin sa yafara zuwa yana shiga kuwa ya tara da ita tayi wanka ta saka wani less me dan karan tsada da kyau taci uban dinki ga stone ta ko ina sai kyakyali take, tsayawa yayi yana kallon ta ko kiftawa bayayi har sada tagaji da kallon da yake mata tace kaiafiya ka kafe ni da ido haka tayi maganar tana danyi mishi hararar wasa murmushi yasaki yace Ammi ganin nai kindau wanka irin wannan kyau haka kamar baki ajiye irin mu ba kamar fa budurwa haka kika koma kinganki ku da kyau amma de wannan kwaliyar da walakin wai goro a miya kamar fa amarya haka kika koma kode angon ne zai dawo ba'asanr da muba muma munyi shiri,

murmushi tayi tace bana son iskanci yaushe nafara wasa daki mahaifin nakune ango to kamar akunne sa sai nagaya masa,

to Ammi tunda ga amarya anan kinga kwa wanda zaizo ai angone dan Allah Ammi dagaske yau zai dawo,

dagske kam yau zai dawo kagama iskancin ka zan sanar dashi daman da guntun haushin ka da yakeji kaga sai yaji dadin sauke maka,

lokaci guda mood din sa ya canza tunawa da sanadin abun da Abban sa zaiyi saboda shirye shiryen bikin sa da zayi wani irin haushi ne da ta kaici yazo masa wuya ya tsaya masa, "Ammi wai dan Allah bazaki saka baki ba abar maganar auren nan wallahi ina cikin tashin hankali  yanzu ko nutsuwar kirkima bani da ita kallon sa tayj cike da tausayawa dan nata ta kalle sa tace Aliyu babu yanda zanyi kasan halinsa tunada yayi magana babu wanda ya isa yasa afasa auren nan saidai kayi hakuri kabi umarnin mahaifin ka Allah yasa hakan shi yafi alkhairi kaci gaba da addu'a idan ba alkairi bane zaka ga sauyi kaga anfasa idan kuma da alkhairi acikin sa dole sai anyi shi babu wanda ya isa ya hana ka kwantar da hankalin ka nasan da wacce kake so amma hakan bazaisa kaki samun taba sai hadasu su biyun saidai kayj hakuri ka kwatanta adalci a tsakanin su kar ka zalunci kowacce daga cikin su nasan kana da hakuri amma ka kara akai ka saukewa kowacce hakkin ta tundade dukan su suna sonka  ina ganin hakan bazai baku matsala ba kade kaci gaba da addu'a itace kawai mafita,

sosai jikin sa yayi sanyi sai yaji kamar ma anriga da andaura da su dukan da yaji irin nasihar da take masa,

cikin sanyi jiki yace Ammi baki san abun dake faruwa ba ko,

kamo hannu sa tayi suka zauna akan gado saboda taga tsantsar damuwar a fuskar shi da kuma idon sa tasan yana cikin wani halin,

dan shafo fuskar shi tayj tana kallon sa tace gaya min me yake faruwa,

kamar zaiyi kuka yace Ammi sun sace tafa tun jiya muke nemanta bamuganta ba yanzu bansan halin da take ciki va taba raye ko tana mace bansani ba Ammi sun raba ni da ita Ammi bazan juri rashin taba wallahi ina sonta Ammi yana fada sai ga hawaye yafara saukowa,

cike da tausayawa tafara share masa hawayen sa tana cewa yayi shiru saboda ita batama kawo wacce yake nufi ba duk atunanin ta budurwar da yace yana so ita aka sace saida tagama goge masa hawayen sannan tace a wace unguwar take kuma garin ya akai aka saceta ina iyayen ta,

  kasake yayi yana kallon ta jin abun da tace tana nufin ma bata gane wacce yake magana ba,

"zuciyar sace takara karaya wata kwallar na kara taruwa acikin idon sa yace Ammi bakisan wacce nake nufi ba ko?

tace "eh mana" ai baka taba nuna min koda hoton tane bare ka kawota mungaisa,

Ammi Ameesha fa nake nufi,

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Aliyu me kake sanar dani abu haka ba dadin ji ya akai haka garin yaya kukayi sakaci har aka dauketa,

Ammi wallahi bamu bane daman ranar da natafi naje gidan sai akace antafi office da ita sai na bisi can daga can kuma muka tafi gidan su dayan wannan wanda akace agidan sarki yake bayan munje muka barta agidan muka tafi..........nanade ya kwashe duk abun da yafaru yabata labari,

Sosai itama ta tsorata da wannan labarin tayi mamaki,

nashiga uku ni Ameena yanzu in ba aganta ba taya zaku tari wannan baiwar Allahn ku gaya mata Allah sarki ashe batayi karya ba jikin ta yagaya mata gaskiya da har ina ganin rashin hakurin ta ashe ta fini gaskiya Allah sarki dadda amma bazanso taji wannan labarin ba kuma nasan muddin baku nemota ba ko ba dade ko bajima sai tasani bazata iya jure rashin taba nasan zata shiga mawuyacin hali inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un  gaskiya wannan abun baiyi min dadi ba bantaba kawo hakan zata faru ba yanzu ita dadda tana can gidan,

"Eh Ammi tana cen yanzude ansa yara suna ta hira dan adebe mata kewa karta tuna da ita dan tace sai ankaita har wajen sarki ta sanar dashi mun dauke mata jika da kyar de ta hakura ta zauna yanzude bansan halin da take ciki ba tana cen ko ta hakuran ko kuma de me yafaru oho sai na koma zanjiyo sode muke zuwa gobe idan munkoma gurin munsamo wata shedar to idan kuma bamu samu ahaka zamu daure kawai mu gaya mata halin da ake ciki tunda ko mun boye yanzu dole tasani nan gaba kuma abun dai yafi mata rashin dadi zata iya cewama bata yarda ba karya muke,

Ammi "tace aikwade ba abun da bazata fada ba bakaga yanda mukayi da itaba dazu da jiya itama labarin abun da yafaru da abun da dadda tace tabasa labari.........,

        ****************************

______*meeshmeer*______

cizo da ta dasa masa ahannu baisan loƙacin da yayi sauri ya sakar mata bakinba kuma yana saki ta ƙara fasa ƙara da saida ta karaɗe duk banɗakin hannu yasa ya toshe kunnuwansa jin tana niyar fasa masa dodon kunne,

tsawa ya daka mata ke wace irin marar hankali ce baki da hankali kinaso ki kashe min dodon kunne ne ko me kike nufi me nayi miki zakisani agaba nida kika cije ni bance komai ba sai ke zakiyiwa mutane ƙara akunne,

sauri tayi ta ta tsugunna tana karkare jikin ta tanayin kuka ƙasa ƙasa jikin ta sai faman ɓari yake,
Chapter 89 · 0% Book details