← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 139

Sashe 136

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

                     💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 99

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

____Haushi da taƙaici da ya ishe shi da dariyar da take masa yasa ya ɗaga plate ɗin hannun sa ya kifa mata shi gaba ɗaya a fuska...........,

___Ɗif tayi da dariyar da take masa ta fara ƙif ƙif da ido gudun kar ya shigar mata ido, take fuskar ta tayi dama dama da mai kamar a fuskar a ka soya ƙwan, duk da taji ƙarni kuma taji haushin kifa matan da yayi a fuska, amma itama dan ta ƙara masa wani baƙin cikin sai kawai tasake fashewa da dariyar ta ciga ba da yi masa dariyar,

Hannu ya ɗaga zai kai mata duka tayi saurin gocewa ya daki iska, ƙwafa yayi cike da ta ƙaici yana hararar ta yana kallon dankalin dake zube a ƙasa yana ƙara jin wani irin haushi na taso masa yanzu yarinyar nan dan ta gama ci masa mutun ci ya sha wahala ya dage ya taƙaƙƙare ya zuba basirar sa yayi mata amma yanzu shine zube a ƙasa gashi kuma taso tasa shi gaba tana masa dariya, dan tagama rainasa to kwa wallahi bata isa ba sai ta cinye sa tas duk da ya zuɓe a ƙasa sai taci sa da haka dan bazai yi wahala aban za ba,

Tana tsaye daga ɗan nesa dashi tana dariyar ta tana toshe baki bata ankara ba taji ya fisgota ta faɗa kansa saura kaɗan ta faɗi tayi saurin rirriƙe shi, hannu yasa ya ƙara riƙota da kyau kamar abun arziƙi a haka ya rungumo ta suka zauna a ƙasan gurin sannan ya rabata da jikin sa ya zaunar da ita agaban sa, Yunƙurin tashi ta fara yi yayi saurin riƙe ta ya miƙar da ƙafafun ta sannan ya ɗora nasa a kai ya danne su, sannan ya haɗa hannu wanta gaba ɗaya biyun ya riƙe su da hannu ɗaya ya matso da ita gaban sa sosai yanda ba yanda zata tayi ta tashi sannan yasa ɗayan hannun sa ya ɗebo dankalin tare da ƙwan ya matso dashi wajen bakin ta,

Cike da zaro ido ta fara girgiza masa kai tare da rufe bakin ƙam yanda bazai iya saka mata, dodana mata shi ya shigayi a bakin amma yaƙi shiga saboda ta rufe bakin ƙam,

haɗe rai yayi ya harare ta yace wallahi idan baki buɗe ba ranki zai ɓaci ba yunwa kike jiba nace kije kiyi kinƙi saurara ta kuma yanzu kinsa naje nasha wahala nayi kice bazaki ci ba wallahi baki isaba sai ki cinye sa,

Kuka tafara yi tana girgiza kai aranta tana ayyana taya zata iya cin ɗanyan dankali ita bana rashin soyuwar ne ma yafi damun ta ba ƙarnin ƙwan shi yafi ɗaga mata hankali, gashi tana so ta buɗe baki ta bashi haƙuri kuma tana tsoron kar ta buɗe ya danna mata shi,

Duk yanda yaso ya da tura mata taƙi buɗewa sai kokawa suke tana ƙoƙarin ƙwace hannun ta, da yaga dai abun nata ba easy sai kawai ya ajiye dankalin a ƙasa ya sakar mata hannu,

Nan tasamu damar buɗe bakin ta ta shiga basa haƙuri da yi masa magiya amma ko kallon ta baiyi ba sai ya ɗauko mayafin ta ya ƙara haɗa hannun nata duka biyu ya ƙulle mata hannu wan dashi sosai ya ƙulle yanda bazata iya kuncewa ba, saboda zafin da taji harda hawaye,

Ƙara jawo ta yayi yasa hannun sa ɗaya ga matsa mata bakin har saida ya buɗu sannan ya sa ɗayan hannun ya ɗebo dankalin dan mugun ta ciki hannun sa yayi dashi ya nufi bakin ta dashi,

Duk yanda taso ya kwacewa shigar dankalin bakin amma hakan ya gagara saidaya danna mata shi abaki, ƙin taunawa tayi, yace wallahi ko ta tauna ko yasa ta haɗiye shi ta dole,

Ba yanda ta iya haka tafara taunasa garas garas saikace ɗanye tana taunawa tana jera masa Allah ya isa tafi cikin kwando kuma tayi alwashin wallahi bashi yaci dan sai ta rama, inda Allah ya taimake ta ma bai haɗa mata da ƙwanba iya dankalin ne, tana hawaye saida ta gama taunesa tsaf, sannan yaƙara ɗebo mata wani yanzu kam har da ƙwan ga haɗo mata ƙwan ma kuma yafi yawa haka shima ya danna mata shi yace "oya cinyesa yanzu nan ai baima gama maganar sa ba tayi saurin furzar dashi tana kallon tace "wallahi bazan iya ciba dan Allah ka rabu dani ba cikina bane me yasa kake son yi min dole inci abun da kwata kwata babu daɗi kuma wanna kwan gishiri da maggi yayi yawa wallahi bazan iya ciba, kuma kaci gaji ga uban ƙarni da yake baka sa albasa ba Allah kuwa bazan iya ciba saidai ka kashe ni........,

Bam taji a bakin ta yasa hannu ya buge mata baki, Saida tasaki ƴar karamar ƙara sakamakon zafin da taji ga ya ƙulle mata hannu bare ta shafa wajen,

Bai dadda raba ya ƙara ɗebowa ya cusa mata shi a baki ta ƙarfin tsiya sannan ya toshe mata bakin ta yanda bazata iya fito dashi ba,

Maggi ne da yaji suka zagaya mata baki take taji zuciyar ta ta hargitse amai ya taho mata duk yanda taso ta riƙe sa abun ya gagara saboda yazo mata wuya, yana sakin bakin kuwa tashiga kwarara amai, yanda yayi ɗaiɗai da ƙafarsa ya danne ta haka aman nan ya wanke masa jiki gaba ɗaya akan rigar sa ta kwararo sa agaba ɗaya rigar jikin sa,

Damƙe idon sa yayi jin zubar amai ajikin, aransa kuwa nanata kalan man anan yake "amai amai ajiki na tabbb wannan yarinyar ta tagama dashi shida ko jin ana amai ma baya so yau shi akayiwa amai ajiki,

tana gamawa ta fara maida numfashi bazato ba tsammani taji ya ɗauke ta da wani irin gigitaccen mari har guda biyu, take jinra da ganin ta suka ɗauke saboda aman da tayi da kuma ƙarnin da yaje samun ta taje taji wani irin zazzaɓi ya fara ziyar tatta da kwa yaƙara mata da mari take ta sume awajen, tayi gefe zata faɗi yayi saurin riƙo hannun ta sai kuma yaji tayi nauyi jikin ta ya saki gaba ɗaya, tsaki yana yasake ta saboda ya gane sume masa tayi,

tashi yayi yana me ƙenƙamin jikin sa ji yake kamar ya cire duk jikin sa, haka yake ji duk ya tsani kansa, Tsaye ya miƙe yana so ya cire rigar amma yana tunanin ta inda zai fara saboda idan ya ɗaga ta zai taɓa masa fuska shikam bazai iya jurar hakan ba, da yarasa yanda zaiyi kawai sai ya ɓalle bottel ɗin jallabiyar ya kama tsakiyar ta da iya ƙarfin sa yajata Ya yaga  Tsakiyar ta tunda ga sama har ƙasa ya keta ta ya cire yayi wulli da ita gefe,sannan ya zare dogon wandon ma  ya rage daga shi sai gajeran wando shima na ciki skintight irin na maza da suke sakawa ta ciki kafin su ɗora gajeran wando,
wajen fridge yaje ya ɗauko ruwa me sanyi, yazo ya yayyafa mata kaɗan bata motsaba, saida ya sharara matasa bakin robar sannan ta kawo numfashi me nauyi, a zabure ta miƙe zaune saidai idon ta nayin ido biyu da santaleliyar surar jikin sa ba kaya, take ta haɗiye wani yawu me zafi da ya haddasa mata wani suman batare da ta shirya hakan ba ta tafi luuuu ta koma inda ta taso,

Mamaki ne ya kamasa ganin ta ƙara sumewa yana tunanin anya kuwa lafiyar ta ƙalau ita abun suma baya mata wahala, tsaki yaja tare da wucewa upstairs yaje ɗakin sa ya ɗauko wasu kayan ya saka ya fito yana tafiya yana sakin tsaki,

saida yazo daf da ita ya ɓalla mata wata uwar harara yaje inda ya ajiye muƙllin motar ya nufi hanyar waje har yaje bakin ƙofa ya tuna idan ya koma gida ba ita yasan dole sai an tuhume sa akan hakan, tunanin hakan yasa shi dawowa da baya ya ƙara ɗaukan ruwan ya watsa mata a fuska wani sanyayyen numfashi ta sauke saidai taƙi buɗe idon ta dan tana farkawa taje surar jikin sa ta sake faɗo mata duk da ta rufe ido amma bata daina hango ta ba a idon ta ƙara ƙanƙame idon ta tayi tana so ta manta da abun da tagani amma hakan ya gagara, 

Har ɗan leƙen fuskar ta yake yana mamakin abun da take shi tsoro ma ta ɗan basa har yafara tunanin to kodai aljanune da ita, ɗan dakewa yayi, sannan yayi gyaran murya, yace "ke meye haken kike kitashi mutafi ko inyi tafiya ta,

"wallahi bazan buɗe ba bana son ganin ka ahaka Please dan Allah katafi ka matsa daga kusa dani, tana faɗa tana sake rufe ido tana girgiza kai,

wani dogon tsaki yaja jin batun da take sai yanzu yagane dalilin suman nata tab aikwa tana ruwa zata mutu watarn kenan idan taga me duka lol 😂 injini fa ba inji saba ah to,
Chapter 136 · 0% Book details