← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 139

Sashe 101

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"gidan ubanki nace gidan ubanki zani kinji mu da ƴar iskar mata anshigo ɗin ko gidan nakine ke kaɗai bakisan manya ba bake yakamata kifara gaidani ba amma maimakon kimin magana mai daɗi shine zaki min hauka akai to ni nawa haukan yafi naki da kinbini ta lallami da kinsamu amsarki amma tunda tahaka kika biyo sai ki shaƙeni ingaya miki idan kina da ƙarfi, dalla malama sakarni kibari masu gidan suyi magana danni da ƴar aiki ma kikafi kama daman ance irin ku idan suka samu waje sunfi ɗan gida iya shege to wallahi kibini ahankali idan bahaka ba jikin ki yagaya miki danni bana ɗaukar hauka yanzu zan saitawa mutum hanya ya shiga taitayin sa, tana kaiwa nan ta fusge jikin ta daga hannun fulani tana shirin ta cigaba da tafiya inda tayi niyar zuwa,

da sauri fulani ta ƙara jawota a harzuƙe ta ɗaga hannun zata sauke mata shi afuska,

caraf dadda ta riƙe hannun ta tare da wurgi dashi da ƙarfi da har saida yasa Fulani tayi baya kaɗan kamar zata faɗi,

da yatsa dadda ta nunata wallahi idan kika kuskura hannun ki yataɓa jikina sai kinyi da nasani na rantse da Allah saina koya miki hankali,

azafafe fulani tace ke kinsan wacece ni da kike gaya min duk maganar da kika ga dama kizo har masarauta ta kice zaki gaya min magana kuma ki kwana lafiya to wallahi baki isa kinbar cikin gidannan lafiya ba yau sai kingaya min uban da ya tsaya miki kikazo kikewa mutane hauka anan dan naga alamar ina jin bakya cikin hayyacin ki kike wannan maganar kina buƙatar adawo dake hanyar daidai, sai ansai ta miki tunanin ki da ƙarfi ta kwalawa murja kira tana amsawa yafito da sauri hartana haɗawa da gudu gudun ta ta ƙaraso wajen tana zuwa fulani tace "je kikira min sarki dorina da bafade da Sarkin su duk kice suyi sauri suzo kiran gaggawa ne,

da sauri ta fice daga falon ta,

dadda ce ta kwamshe da dariya tace aikin banza ashe ma taƙamar taki ta banzace tunda bazaki iya ɗaukar mataki da kanki ba sai kinsaka an ɗaukar miki wallahi kinban mamaki tsohuwar banza kawai, ni banda loƙacin ki ba gurin ki nazo ba da harkike cewa nazo bara kalata da shiga ta tamiki kama da wacce ta nemi wani abun arayuwata ta rasa ko tufafina sun miki kama da hakan saboda tsabar wulaƙanci da cin fuska ne yasaki faɗar haka ko?

Azeema da tajidai hayaniyar tayi yawa yasa tayi saurin fitowa daga dakin ta ɗan leƙo tana leƙowa idon ta yasauka akan dadda zato ido tayi tana me mamakin ganin ta me yakawo dadda gidan nan inna lillahi wa inna lillahi raji'un Allah yasa ba mama ce ta turo taba da sauri ta koma ɗaki dan tana godewa Allah da bata fito gaba ɗayan ta ba tasan idan dadda taganta shikenan asirin ta zai tonu,

duk abun da suke shettima na kallon sa daga bakin ƙofa kawai so yake yaga yanda wasan nasu zai ƙare yasan halin ko wacce daga cikinsu dan haka babu wacce zata ɗagawa wata ƙafa kowacce ƴar kanta ce basu da haƙuri gaba ɗayan su ita fulani nuna isa da gadara da wulanƙan ci ita kuma dadda bata ɗaukan raini ko kai waye baka isa ka taka taba kuma ta taku dan haka yana gurin har dariya yakeyi ƙasa ƙasa saboda faɗan nasu ba ƙaramin ƙayatar dashi yayi ba zaiso yaga ƙarshen faɗan nasu yaga wace zata haƙura ta barwa wata,

a harzuƙe fulani ta buɗi baki zata mayar mata da martani aka turo ƙofar daka tawa tayi batare da tayi maganar da tayi niyya ba,

bata kalli ƙofar ba tace maza kufitar min da wannan mahaukaciyar daga nan gurin ku fita da ita ku koya mata hankali,

shiru taji sunyi basu yi abun da tace musu ba,

jin hakan yasa ta dago dan tayi musu masifa sai kawai taga wayam basu bane ashe sam ne yashigo ita kuma duk atunanin sune,

idon sa akan dadda ko bai tamabaya ba yasan abun da yafaru dan haka bai tanka musu ba kawai ya wuce zai tafi part ɗinsa dadda tayi saurin cewa kasan de ku nake nema zaka wuce kamar baka taɓa gani na bama,

"kiyi haƙuri ina zuwa, kawai yace da ita sannan yayi gaba tunkan ya ƙarasa ma yaga shettima a tsaye na dariya tsayawa yayi yana kallon sa yace kai kuma me kakeyiwa dariya da hannun shettima ya nuna masa su dadda sannan yace ya akai zaka katse min kallon da name dama kabarsu wallahi faɗan nasu nishaɗan tar dani yake,

mtsw bakada aikin yine shiyasa kana kallon su suna faɗan amma ka kasa shiga tsakaninsu kadai san halin waccen rikitar tiyar tsohuwar yanzu sai tajamana abun da zamuyi danasani kafito mu wuce gidan su bossay yace muje ana neman mu wai yarinyar nan tana gidan,

"habadai wacce yarinyar kake nufi kuma,

sameer yace yarinyar da muke nema mana shiyasa yanzu ai hankalina bai tashiba dana ga matar nan agurin nan dan haka tun kan su kacame azo asamu wata matasalar kazo mubar gidan arabu da ita lafiya dan ko gurin momma bazamu komaba mu wuce canɗin kawai daganan,

"to wai dan Allah taya ta koma abun da yaban mamaki wannan wane irin juye juye ne ansace ta awani waje anga alamar ta acikin gidan nan yanzu kuma ace anganta acan wannan lamarin fa ni yafara bani tsoro wallahi,

kadai zo muje kawai nima bansan ya akai hakan ta faruba sai muje zamuji,

"Ok to muje, atare suka juya suka ƙarasa wajen su Fulani da suka cigaba da cece kucen su irin nasu na manya,

suna zuwa sam bai saurare suba kawai yaja hannun dadda tana ƙwace tana cewa yasake ta sai ta koyawa fulani hankali itama fulani tana cewa wai a ina yasamo wannan mahaukaciyar matar yasake ta kar yasake tafita da ita daga cikin gidannan sai tasa an ɗaure mata ita,

kowacce dai da kalar maganar da take amma yaƙi sauraron ko waccen su yacigaba da tafiya da ƙyar dai aka samu aka raba su suna fita shettima yajawo ƙofar ya rufe fulani aciki sannan suka wuce suna zuwa suka danna dadda a mota suka rufe suma suka shiga sannan sameer yatayar da motar da gudun gaske yabar masarautar dadda sai surfa masa masifa take yayi mata bazan yace gaba da tuƙin sa ya ɗauki hanyar gidan su bossay........✍️✍️

                   💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[7/12, 9:47 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 87

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

*Ina masoyan dadda wannan page ɗin nakune*💃💃💃💃

______*Dadda*______

  "tunda suka fara tafiya dadda take surfa musu bala'i  kamar su sukayi mata laifin sunyi mata magana tayi shiru sun bata haƙuri amma duk da haka da haka taƙi sauraron su....,

Sameer da yagade abun nata bana ƙare bane da yaga ta damesa taƙi yin shiru sai kawai yafara yawo da motar kamar zai bugata da wani abun suyi accident aikwa tana ganin haka ta sakar musu ihu tana cewa kashe mu kake so kayi nashiga uku na yaron nan anya kana da hankali yace bani dashi ai shiyasa zan nuna miki rashin hankalin wallahi idan bakiyi mana shiru da bakin kiba sai buga motar nan da abu kin mutu daman kece abaya kuma idan na bugata ke zaki mutu bamu ba,
"wallahi bazan shiruba da bakin ka nake maganar,

jin hakan yasa yaƙara jan motar da ƙarfi sannan ya taka burkin da ƙarfi,

talau talau tayi zata faɗa gaba sai kuma tadawo da baya atake ƴaƴan hanjin ta suka motsa saida taji kamar zasu fito saboda tsabar tsurewa da tayi saida hawaye suka ta rar mata atake kwa tayi tsit kamar babu ita amotar,

atare suka juyo shida shettima suna kallon ganin yanda ta koma yasa suka saka mata dariya taƙaici da haushi yama hanata magana amma ita kaɗai take raya abun da zatayi musu ta rama wannan rashin mutuncin da sukayi mata tunda take babu wanda ya taɓa sata gaba yayi mata haka waccen akuyar ta gama ɓata mara rai shine suma yanzu suka zo suka ɗora akai,

sam yace "akaro na farko da yafara kiran sunan ta yace "hajiya dadda yadai bakin ya mutune ko kuma inƙara kashe shi da mota,

banza tayi dashi tare da galla masa wata uwar harara kamar idonta zai faɗo,

"Au bazakiyi magana ba kuma harda hararata to bari inƙara suma idanun in kashe su yana faɗar haka yaƙara sakin murmushin mugun ta sannan
ya juya ya tayar da motar yana shirin fara tafiya dadda datagade yaron da gaske bashida hankali kuma inbata dakatar dashi ba sai yaƙara yi mata itakuma ahalin yanzu ai bazata taɓa son ta ƙara jin abun da yayi mataba yanzu dan tasan tsaf zata iya rasa ranta idan yaƙara dan haka sai ta sauke makaman yaƙin ta tayi saurin cewa wallahi ya mutu bazan ƙara yin magana ba na rantse muku da sarkin gidan ku🤣

sosai sukayi mata dariya tare da kallon ta shettima yace "daman haka kike da tsoro yau naga logonki hajiya dadda,

Sam ya ɗora dacewa "daman tun can bata samu daidan ta bane nidaman bata taɓa shigowa hannu na bane da tuni na daɗe da saita wallahi duk iskancin nan nata tana sane take yinsu,

Allah sarki dadda yaudai da gaske bakin nata ya mutu dan bata da halin magana shiru tayi duk abun da suke mata bata tanka musu ba dan har ga Allah yauɗinnan ba ƙaramin tsorata tayi ba dan haka ta siyawa kanta zaman lafiya tasawa bakin ta saƙata,

sukuma sukaci gaba da tafiya suna ƙara yimata abun da suka ga dama suna mata dariya yau sun samu dama.....,
Chapter 101 · 0% Book details