← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 139

Sashe 121

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 95

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

   tsullum sai ga gwaggo ta fito daga bayan kujerar da ta ɓuya tazo gaban su kamar wata zararriya haka ta zube agaban sabreena ta riƙo hannun ta sai kuma ta ƙara tashi daga zaunen ta tsugunna tashiga goge mata hawayen..

tana ta faman tattaɓata da kyua dan taƙara tabbatar wa kanta itaɗin ce,

sai kawai itama ta fashe da kuka harda su majina sannan ta koma ƙasa tayi zaman dirshen ta fara cewa "daman nasani nima Saida nace bata mutuba akace min kin mutu shiyasa aka hanani ganin gawarki ai duk wani wanda ke cikin gidan banajin yaga gawarki saidai a lulluɓe  an hana kowa gani ki, miƙewa tsaye taƙarayi  sannan tace gaba da cewa,  "ashe ƙullalliya aka ƙula shiyasa akayi haka tokwa Allah ya kwashewa tanbaɗaɗɗu albarka tsinuwar Allah ta tabbata agare su wannan wane irin mugunta ce ashirya mutum arabasa da iyalin sa da mijin sa kuma ace ya mutu wai wane ɗan iskanne ma yafara sanar mana da mutuwar ta wallahi shi za akama aci uwar uban sa kowaye shi tsinanne marar albarka tana maganar tana ɗaga hannu harda su sakin mayafi  ya faɗi ƙasa masifa kawai take zazzago musu  kamar wanda yayi laifin yana gaban ta sai da ƙyar aka samu aka rarrashe ta ɗan dakata da abun da take cewa,

sannan waziri yacewa maama taci gaba da basu labarin abun daya faru da ita,

kuma sosai gimbiya sabreena take saboda jin yanda akace ta mutu bayan kuma da ranta hakan ba ƙaramin sosa mata rai yayi ba, saida papa ya rarrasheta sanan tayi shiru ta samu bakin magana amma duk da haka sai tace "abubuwa da dama sun faru waɗanda ni kaina ban san faruwar su ba  saidai zan wakilta wanda zai baku labarin abun dake faruwa tunda barina gidan,

ummy ta kalla sannan tace ga wacce suka tsince ni itace zata baku labarin abun da tasani kowa maida kallon da hankalinsa yayi kan ummy da maama ta nuna musu,

daga inda take ummy ta fara basu labarin ta yanda suka haɗu da ita tun loƙacin da aka kawo su asibitin su da abun da waɗanda suka kawota sukace nandai ta kwashe komai tagaya musu har zuwa loƙacin da tadawo cikin hankalin ta bayan malam yayi mata magani saidai bata gaya musu alaƙara dake tsakanin su ba na ɗa da uwa harda jika kawai ta tsaya musu zuwa inda suka baro garin abuja suka dawo kano suka kama gida anan ta tsaya da basu labarin tace ga iya abun da nasani yanzu wannan baiwar Allahn zata cigaba da baku labarin ta nuna musu dadda,

gyara zamanta dadda tayi sannan itama ta shiga basu labarin abun da tasani tunda ga loƙacin da aka bugeta a motar har baba yakai ɗanta gidan suka ci gaba da riƙesa hardai zuwa giraman sa da kuma waɗanda suka kawo masa farmaki............komaidai tagaya musu da yanda suka haɗu da su sam har suka fara taimaka mata akan zasu fara bincike sai kuma ga su maama sunzo suma loƙacin da Ameesha ta ɓata sai ta faɗa hannun ɗansu ya taimake ta daga maama ta gane cewar jikarta ce......., itama kuma bata gaya musu cewar Abu ɗan maama bane tadai sanar dasu Ameesha jikarta ce kuma ɗanta ma ana sa ran yana raye saidai ba a san inda yake ba abun da ake ƙoƙarin ganowa kenan tun kafin ma zuwan su Sameer Allah kuma baiyi ba sai yanzu da Allah yayi wannan haɗin cikin ikonsa na haɗasu guri ɗaya har sukazo nan yanzu suke bada labarin abun da yafaru,,

Kalamar inna lillahi wa inna lillahi raji'un kawai papa yake iya faɗa saboda ba ƙaramin shock ya shiga ba jin yanda ahalin sa suka kasance cikin ƙunci da wahalar rayuwa suna raye awani wajen batare da sanin saba,

bashi kaɗai ba gaba ɗaya ilahirin gurin babu wanda bai jinjinawa faruwar wannan abun ba kowa cike yake da ɗunbum mamaki tunda suke atarihin masarauta ba ataɓa aikata abu makamancin haka ba ba ataɓa mugunta irin wannan ba babu matar da aka taɓa yiwa irin wannan cin zalinci aka koreta daga gidan sarauta duk dade daman gidan sarauta yagaji irin waɗannan makirce makircen na asiri da makamancin su amma dai ba ataɓa aikata irin hakan ba,

hayaniya gurin ya ɗauka wasu na sharar hawaye wasu kuma na zufa saboda yanda hankalin su ya tashi da bayyanar ta wasu kuma na farin cikin wasu na baƙin ciki wasu kuma nayin nadama wasu kuma suna ƙara wani tunanin aransu yanda zasu ƙara tarwatsasu dan bazasu bari farin ciki yaci gaba da zama agurin su ahaka suke so su ƙare rayuwar dan haka dole su ƙarayin wani ƙyaƙƙyawan shirin akansu dan bazasu taɓa lamuntar zaman su aciki gidan fa duk da sun tsorata amma hakan baisa sun karaya ba sun saduda ba saima wani tunanin ma suke daban,

papa ne da idon sa yakaɗa yayi ja dashi saboda tsabar baƙin cikin da ya tsinci kansa ya kamo gimbiya dake kusa dashi yashiga bata haƙuri kamar shi yayi mata laifin, shi sai yanzu ma da aka bada labarin ya tuna ashe harda ɗa loƙacin da ta mutu tunawa yayi bai wanda yayi zancen ɗan tunda ta mutu kuma itama kanta aka manta da zancen ta bare kuma ɗanta kwata kwata babu wanda yayi zancen Sameer sai yanzu da aka bada labari kowa yatuna dashi anmantar dasu gaba ɗaya sai yanzu tunanin wasu yadawo,

  gwaggo cikin share ƴar ƙwallarta ta matso kusa da ita tace "Allah yasaka muku duk wanda yayi miki wannan mugunta Allah yasaka muku gaba ɗayan ku Allah ya toni asiri tsinannu wallahi duk wanda aka kama da sa hannu sa aciki Ni da kaina zan binne sa da ransa bayan angasa masa azaba in Allah ya yarda Duk dai an kama maku mugaye tsinannu waɗanda basu da imani shine bayan kunfitar da ita daga gidan hakan bai ishekuba shine kuka bi ta bayanta kuka bugeta da mota sannan kuka rabata da ɗanta shima baku barsaba kukabishi kuke azabatar dashi da ƴarsa saboda tsabar mugunta da ha'inci da son zuciya irin naku maitayi muku mai tsare muku tunda muke da sabreena bantaɓa jin kanta da wani ba kowa nata ne tana mutunta mutane kukayi mata haka dan cin amanar zama ko dan saboda kunga ɗanta shine sarki to ai bata ɓaci ba asirin ku zai tonu kuma gashi Allah ya nuna muku ishararku gasu sun dawo sai kukashe kanku dan baƙin ciki, kallon ta tamayar kan Ammah da fulani sannan tace wallahi wannan mugun zama irin naku ai ba wani ɓoye ɓoye ko rufa rufa da za a ɓata loƙacin gurin gano wanda ya koreta dole acikin kune dan haka wallahi ku za akama musamman ke ɗin nan ta nuna fulani sannan tace "ko rantsuwa ma nayi bazataci ni ba wallahi ni nasan kece ummul aba isin faruwar komai tunda gashi kinkawo mana wani ɗan kince nakine anɗau sarauta ambasa saboda ke baƙya haihuwa shiyasa kika kori mai haihuwar kika kawo wani daban akan cewar ɗankine saboda tsabar ƙwarewa da son kai da mugun ta to wallahi zakici ƙundugurin buhun ubanki sai an karkarya ki gunduwa gunduwa anbawa karnuka suncinye ki ahaka dan nasan ƙasama bazata karɓeki ba saboda mugun halinki shegiya ƴar kutumar uba mai kama tukunyar giya 🤣(oh ni ƴasu daman a tukunya ake dafa giya) tana faɗa ta ɗaga ƙafa zatayi kanta aka riƙota da daga abun da take shirin yi dan sunan idan suka sake ta sai ta kusa kaita lahira alhalin ba a tabbatar ba da zargin da take mata ba dan ahalin da suka ganta sunan halin ta zata iya aikata komai ma dan gwaggo haka take akwai zuciya bata iya fushiba idan ranta ya ɓaci bata ji bata gani tun ƙuruciyar tama idan abu ya haɗasu da wani to idan bata ganta akanka tana maka mugun duka to bata samun nutsuwa har saitaga ta ladaftar dakai da duka gata da ƙarfi kamar me aljanu haka take komawa idan tana dukan mutum shiyasa haryanzu halinta na nan ba raguba ba saima ƙaruwa da yayi ga faɗa kuma ga tsufa sai abun yake neman fin nada kunsan mutum ko baida faɗa idan ya tsufa sai kuga ya canza hali abu kaɗan zakayi masa ya hauka da masifa da bala'i duk kusan tsofaffi haka suke da zarar sun tsufa, bare kuma ita da daman can mafaɗaciyar ce ga tsufa kuma shiyasa abun yayi worse da yawa idan ranta ya ɓaci bata iya controling ɗin kanta saita koma kamar wata zararriya, abun har mamaki yake bawa mutane yanda take adore ƙashin ta da ƙwari har yanzu dan idan ta ɗaga hannu ta makama sai kaji ajikin ka ƙarfi gare ta kamar doki shiyasa har yanzu da sauranta bai gama tafiya ba,

Ammah nason yin magana amma takasa saboda tsoron gwaggo da yakamata tana tsoron tayi magana gwaggon ta dawo kanta dan haka ta ƙara jan jiki  ta takure gefe guda aƙasan kujerar san zaman kan kujerar ma ya gagareta tunda akace acikin su biyu sai sun fito da wanda ya koreta ta tsure dan bataso zargi yazo kanta dan tasan zasu iya wahalar da ita idan suka fara zarginta dole ko mai zasu ce bazasu yardaba kuma tasan Fulani ko da ita tayi bazata amsa ba nan kusa saitasa an wahalar dasu itakam ina zata tsoma ranta wannan tunanin ne yasata rawar jiki ta sauko daga kan kujerar ta koma ƙasa can lungu lungu ta zauna ta kama kanta guri ɗaya....,
Chapter 121 · 0% Book details