← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 139

Sashe 26

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dan numfasawa tayi sannan tace ya maganar da nayi maka tun kwanakin baya kamaida ni yar iska baka cemin komai ba tunda ban isa da kaiba bakai matsayin da zakace min ga yanda kukayi ba ko to ni nayi maka tunda ni nadamu shiru yayi na dan wani lokaci sannan ya budi bakin sa da kyar yace wacce maganar kuma namanta riqe baki tayi tana kallonsa da mamakin ranin hankalin sa dan zata iya rantsewa batare da rantsuwa tacita ba yana sane yasan wacce maganar kawai rainin hankali ne irin nasa cike da bacin rai tace kamanta to tashi kabarmin waje kar nasake ganin qafarka anan duk lokacin da ka tuna kazo tashi kabace min dagani ba kunya ba tsoron Allah kwa ya miqe ya tafi har yakai bakin qofa sai kuma ya tsaya tare da juyowa yana kallon ta ganin ta dauke kai daga gare sa yadan shafo gemun fuskar sa sannan yace tun lokacin nagaya miki kuma mun gama magana dake kaf matan garin nan ba wacce takai matsayin in kulatama bare in aure qarewa ma ni bana ra ayin aure yanzu saboda ba mace da ta isa ince inasonta nibanma ga abun so a mace ba da harkuke naniqamin wata kucaka wacce ake neman kai da ita ni koda zanyima ai bata irin wadanda zan kula bare kuma har takai in hada guri da ita amatsayin mata bazan iyaba kucewa iyayen nata suje su nema mata wani irin ta amma baniba dan ni ba class dinta bane ni wlh nama tsane ta da kinsan yanda na tsaneta da baku qara yimin maganarta ba,
yana gama fadar haka yasa kai yafice daga falon,
tagumi momma tayi tana tunanin maganganunsa sosai yabata mata rai itade batasan yanda zatayi da wanna yaron ba dan yafi qarfin ta zaman waje da yayi yasa gabadaya ba tsoron fadar duk kalmar da tazo bakin sa wajen wata bakwai kenan da tayi masa maganar tun awaya amma sai yayi mata banza yace shi ba yanzu zaiyi aure ba ta rabu dashi ta zuba masa ido daga baya taqara yi masa maganar akwai yar kawarta da ta nuna tana sonsa kuma iyayen tama suka goyi bayan hakan amma da yake shi be gaji mutun ci ba shine ya bijire ba a isa ayi masa magana ba sai yabarka da magana kuma ko ajikin sa yaqara gaba batasan yanda zatayi dashi ba wallahi kullum halayen sa gaba suke basa raguwa ko kadan tana cikin tunani kawai taji saukar ruwa akan fuskar ta ashe hawayen takaici take batasan ma da zuwansuba sai zubarsu da taji hannu takai zata goge taji wani hannun daban akan fuskarta an shiga share mata su dagowa tayi dan ganin me share mata dan tunanin tama yafi bata ko Amra ce saboda itakadai ce idan taga ta shiga damuwa take kwantar mata da hankali shiyasa duk tafi ji da ita saboda itama tana jin tausayin ta amma ga mamakin ta sai idanunta suka sauka akan wanda bata taba tsammani ba sam ne tsaye agaban ta ya zuba mata ido cire hannun sa tayi daga kan fuskarta tana harararsa tare da nuna sa da yatsa tace don't touch me again if not I will slap ur face tafada tare da mikewa daga gurin memakon ya bata hakuri ma a'a kawai sai yadage kafadar sa irin I don't care it's ur fault is not my fault sannan yadau wayarsa da yabari daman yazo dauka yana dauka kuma shima yayi ficewar sa yana fita drivern sa yazo ya bude masa qofa yabar masarau tar ma gaba daya yama manta da ance papa na nemansa,

*CIKIN MASARAUTA*
"shela akafara yi cewa ance duk wani ma aikaci kama daga manya da yara tsoho da yaro mace da na miji cewa uwar masarauta na neman kowa da kowa ya hallata a babban fili taro ba arage kowa ba har yaran masarauta zasu iya fitowa hakade me shela yake ta zagayawa yana fadar haka saida ya karade kaf masarautar yana fada kowa kuma yaji inda masu harama suka fara shirin fitowa danjin abun da zai wakana wasu kuma danjin gulma suke fitowa wasu kuma suna tsoro da fargabar fitowa kar wani abun suka aikata da za ayanke musu hukun ci agaban mutane saboda wataran baka san me kayi ba za ataraku ayimaka hukun ci agaban mutane shiyasa kowa de da abun da yake sakawa aransa.......✍🏿
[5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿21&22

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

CIKIN MASARAUTA*

   "shela akafara yi cewa ance duk wani ma aikaci kama daga manya da yara tsoho da yaro mace da na miji cewa uwar masarauta na neman kowa da kowa ya hallata a babban fili taro ba arage kowa ba har yaran masarauta zasu iya fitowa hakade me shela yake ta zagayawa yana fadar haka saida ya karade kaf masarautar yana fada kowa kuma yaji inda masu harama suka fara shirin fitowa danjin abun da zai wakana wasu kuma danjin gulma suke fitowa wasu kuma suna tsoro da fargabar fitowa  kar wani abun suka aikata da za ayanke musu hukun ci agaban mutane saboda wataran baka san me kayi ba za ataraku ayimaka hukun ci agaban mutane shiyasa kowa de da abun da yake sakawa aransa.......

    dan danan gurin yafara cika da mutane kowa inka gani inma bezo ba to yana shirin zuwa wajen adan qanqanen lokaci gurin ya cika kowa ya hallara agun dai dai kune kawai basu qaraso ba,
Mery dake kitchen tana so tayi sauri taqarasa aikin da takeyi tafita kar abarta abaya Ammah ce taqaraso cikin kitchen din zata dauki abu ganin yanda mary ke sauri tace ke lafiyar ki qalau kuwa inazaki haka naga sai faman sauri kike sada kanta qasa tayi cike da ladabi tace Allah yataimakeki uwargidan sarki ai anyi shela ne ana bukatar kowa ya hallara a babban fili shiyasa nake sauri taqarasa tare da qara sunkuyar da kanta jinjina kai Ammah tayi sannan tace to kibari idan kin dawo kya qarasa kar kijawa kanki laifi kamar ta zuba ruwa aqasa tasha saboda dadi shiyasa take jin dadin aiki a qarqashin ta matar tana da sauqin kai bata da jiji dakai yanda take mu'amala da bayinta da wasu mutanen sai ka rantse ba agidan sarauta take ba bare kuma matar sarki nomal take daukan kowa ganin take daidai suke da ita,
godiya tayi mata sannan tafita cikin sauri ta qarasa dakinta tana tura qofa sukayi karo da Azeema hakuri ta bata sannan ta cire kayan jikin ta ta canza wasu duk acikin sauri takeyi tana gamawa tabude qofar zata fita Azeema tayi saurin tsaodata da tambayarta ina zataje taga tana sauri cike da qaguwa tace mata ananeman ma'aikata cikin masarautar nan za ayi sanarwa ko kuma za ayiwa wani hukunci bakinta haryana karkawar sauri wajen cewa nima zan iya zuwa ko sai iya ku karkada mata kai tayi alamar sannan tace inkinso zaki iya zuwa mana amma de kibi ahankali tunda ke bakuwace kar kije kiyi wani kuskuren da zaisa a hukuntaki dan any mistake game over zaki iya jefa kanki cikin wani halin tana gama fada tayi gaba tace kisame ni awaje banaso inzama qarshen zuwa da sauri Azeema tace to muje ai ba abun da zanyi tare da jawo hijab dinta dake jikin wardrobe ta ruqoshi ahannu saida tafito taqarasa sakawa tana Allah Allah kar ta hadu da Ammah saboda tunjiya da tace tatafi bata qara fitowa ba dan haka bata qara ganin taba daman batason su hadun shiyasa taqi fitowa  Allah cikin ikonsa kwa basu haduba har suka fice daga part din suka nufi gurin tundaga nesa suke hango mutane a zazzaune wasu kuma a tsugunne kale kale Azeema ta shiga yaude gata tama yawo acikin masarauta tunda ta fito take addu'ar Allah yasa taga mahaifin ta cike da farin ciki aranta suka qarasa gurin suma suka samu waje suka zauna kamar yanda kowa ya zauna,
bayan zuwan su ma wasu suna ta qara fitowa inda Azeema take baza idanu lungu da sako duk wanda ya taho sai ta bishi da kallo amma Allah besa ta ganshi ba tunani tafara to kode baya gidan wancan mutumin qarya yake musu to amma akan me zaiyi musu qarya bama qarya bane wata zuciyar tata tabata amsa shiru tayi tana qara nazarin abun,
sunkai wajen minti goma agurin kafin daga bisani sarki yataho tare da muqarrabansa suna mara masa baya wasu kuma agabansa dukde ankare sa yanda ba kowa zai gansa ba suna tafiya suna yi masa kirari gyara kintsi da kyau gyara kintsi da kyau takawarka lafiya sarkin sarakai Allah ya kare gabanka da bayanka kafi qarfin makiya saidai kai kaga bayansu bade suga bayanka ba dan sarki jikan sarki uba ga sarki nan gaba kuma kaka ga sarki gaba sarauta baya sarauta muliki ajinin jikin ka yake babu me ja dakai duk wanda yace zai gwada saidai a haifi wani bade shiba sarki me adalci acikin masarautar adalai aikin ku na kyau komai kukayi daidai ne bakwa kuskure tsarin ku nadaban ne Allah yaqara maka lafiya da nisan kwana yabaka tsawon rai me inganci hakade suke tafaman zabga masa kirari har suka qarasa inda yasaba zama suka nufa duk wani wanda yake awajen saida ya miqe gaba dayan su suka miqe tsaye saboda sarki zai zauna dole sukuma sukasance a tsaye yafara zama tukunna su zauna,
suna qarasawa fadawansa suka baza masa babbar riga tare da juya masa baya dan yasamu damar zama (kunsan ba a ganin zaman sarki)
Chapter 26 · 0% Book details