← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 139

Sashe 85

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da sauri dadda ta dafe fuskar ta tace ke ni kuma bazan ɗauki hakan ba ɗaga nima wallahi da kwarina bazan bari ki nakasani  ba kinji da ƴa to yaseen ɗagani na ba gwaggo bace idan kina mata ta ƙyaleki to ni duka nake bana wasa da yara, dan haka maza ki ɗagani kar na mazgeki anan dan dukana zafi gare sa zaki iya yin bunga dariya Amra tayi ba ita kaɗai bama su momma saida suka ɗan dara jin yanda take magana da iya gaskiyar ta ta kuma haɗe rai amma hakan baisa Amra ta ɗagataba cikin dariyar tace dadda meye kuma bunga,

mutuwa mutuwa itace bunga idan kuma kinso kiyi to kici gaba da abun da kike min nikuma zansa kiyi bunga ɗaga ni nace,

maƙalƙaleta Amra ta ƙarayi tana dariya tace Allah kam bazan tashiba sai kinsa nayi bunga ɗin indai kinga na ɗagaki to nayi bunga ta ƙarasa maganar tana jan gashin kanta da yaɗan leƙo waje,

da sauri dadda ta riƙe mata hannu tace Allah kam yarinyar nan da sauranki yanzu gashin zaki cire min dan kina baƙin cikin na fiki ko wai duk kuna ganin ta abun da take min amma bamai hanata to wallahi kar kuganni baƙuwa danni ban iya baƙunta ba zan cire kunya in zane muku yarinya tunda kuna kallon ta kun kasa hanata wannan ai rashin mutun cine,

momma tayi yar dariya tace wayake shiga tsakanin jika da kaka ai idan kaga suna abu ido ake zuba musu idan ka shigama kai zakaji kunya dan haka ke da ita babu ruwan mu aciki,

gashin Amra ta ƙara jawowa wanda na yanzu yafi na da zafi da sauri dadda itama ta cire hular dake kan Amra taja mata itama da ƙarfi to fa uwar tsokana saigashi tafara hawaye saboda ta tsani ataɓa mata kai shiyasama ko kitso batayi kanta sai yafi kwana nawa a ɗaure sai anyi da ƙyar wataran ma yake samun ataje shi sai gashi dadda ta kama kan da iya ƙarfin ta taja mata shi,

  tun tana kwalla har tafara fitar da kuka me sauti sannan dadda ta sakar mata kan tace ashe ba daɗi kai ai ba fin kai yayi ba ni da kika jamin kan robane dani da bazan ji zafin ba to kaɗan ma kika gani ɗagani,

  " cikin turo baki Amra ta sauka daga kan dadda tana ciccin magani ita adole tayi fushi da ita,

Hamra ce tayi saurin riƙe Amra tace haba sister yaza ayi kibari tsohuwa tayi galaba akan ki har tasaki kuka kuma kika rabu da ita wallahi idan nice bazan yarda ba kije ki rama kar ki rabu da ita,

ƙaton filo dadda ta ɗauka ta makawa hamra tace to mazigiya ina ganinki tun ɗazu shiru shiru ashe kema baki da mutunci to ke kizo ki rama mataɗin kiga yanda zanyi dake kema bana gaya mata dukan yara nake ba bata yarda ba ni wallahi ma har tasa kaina yafara ciwo kawai daga zuwa sai afara cin zalina to kwa bawanda zan ɗagawa ƙafa,

dariya sukayi mata gaba ɗayan su sameer de da yaga abun nasu ba ƙarewa zaiyi ba sai yayi ficewar sa yana jin daɗin hakan da sukeyi har ya fitama dadda bataga fitar sa ba,

share hawayen ta Amra tayi tare da ƙara juyawa kan dadda da sauri tana zuwa ta sauke mayafin dake kanta ta tare da ɗan kwalin daman dadda batayi kitso ba Ammi ce keyi mata kuma ta tsife shi jiya yau za ayi mata kitson kuma saiga abun da yafaru hakanne yasa kanta yakasance a tsefe,

Amra naganin gashin ta a tsefe batasan loƙacin da tasaki dariyar mugun taba kafin dadda tayi wani yunƙuri har ta danna hannuwan ta akan ta fara ya mutsa mata gashi tare da jansa da ƙarfi duk yanda dadda taso ta kwaci kanta taka sa idon ta har ya kaɗa yayi ja saida Amra ta tabbatar da ta rama sannan ta sake ta tare da guduwa bayan momma tana ɓuya,

numfashi sadda tashiga sauke wa na wahala tana dafe kanta ita kaɗai tasan abun da zatayiwa yarinyar idan ta tashi,

"Hamra na dariya ƙasa ƙasa taje wajen dadda tana bata haƙuri ayya tsohuwa kiyi haƙuri bari in ɗaura miki ɗan kwalinki ke kuma Amra gaskiya baki kyauta ba yanzu abun da kikayi ke idan akayi miki zakiji daɗi tana maganar ta ɗauko ɗan kwalin dadda zata ɗaura mata dadda ta kwace abunta tana ture ta tace to munafuka bake kika zigata ba yanzu zakizo min da wani guntun munafurcin ki ai wallahi zaku gane baku da wayo daga ke har itaɗin bade ni kuka yiwa hakaba zakuyi bayani,

Amra ce ta leƙo daga bayan momma tace kinga dadda na ɗagowa tayi mata gwalo tace in kin isa taso ki kamani yanzu in ƙara wahalar dake wallahi,

  "hararar ta kawai dadda tayi batare da tace mata komai ba ta jinjina kai irin zan kamaki ne yarinya,

hakade sukai tasaka ta gaba suna tsokanar ta suna kunna ta ita kuma tana biye musu tunanin su momma yayi aiki dan bata ƙara zancen zuwa gun sarki ba ko ganin Ameesha ta biye musu suna ta faɗa su tsokane ta ta rama hakade suke ta abu ɗaya.....,

sameer na fitowa falo yayi musu magana suka tashi ga ɗayan su suka fita aƙafa suka taka har zuwa wajen me gadin,

yana ganin su ya taso da saurin sa yana gaida su babban mutum ne,
  dan haka suma sai sukayi saurin mayar masa da gaisuwar ya amsa yana ɗan sunkuyar da kai,

bossay ne yafara cewa yau baba magana zamuyi kuma muna so ka faɗa mana gaskiya kar ka ɓoye mana komai kanaji ko,

da sauri mutumin ya karkaɗa gaban sa na  faɗuwa  da ya ɗan tsorata da ganin su sannan"yace in sha Allah

  "yauwa muɗan ƙarasa can gurin sameer yafaɗa yana nuna musu wani waje da ba mutane,

gurin sukaje suka tsatstsaya sameer ne ya gyara tsayiwar sa da kyau sannan yafara magana idan zaka iya tunawa ajiya tundaga safe har dare zaka iya tuna adadin motocin da suka shigo kuma suka fita,

ɗan jimm yayi kafin yace gaskiya bazan iya tunawa ba saboda da yawa wannan yashigo wancen yashigo bazaiyiyu insan adadin suba,

to daga magariba fa zuwa dare eh to wannande zan iya tunawa akwai motar matan mai martaba da suka fita ana daf da magriba sai kuma suka dawo bayan an idar da sallah sai waziri da ɗan sa shima yafita gaba ɗayade baifi motoci huɗu bane suka fita suka dawo ba aciki harda taku yauwa sai ta su yarannan ƴan biyu suma sun fita amma su tunkan la'asr ma suka fita kuma sai dare ma suka dawo bayan nan kuma sai motar tasu ta ƙara dawowa tafita yana fita ku kuma kuka shigo to nide inajin abun da zan iya tunawa kenan,

  bossay yakalle sa yace bakaga wata baƙar motaba bayan sallar magrib,

  gaskiya bangan taba amma bansaniba ko loƙacin bana gurin ta shigo natuna ma aloƙacin naje karɓo abinci wataƙil ko anan yashigo bansani ba,

"daman ana iya buɗe gate idan baka nan ko akwai wanda yake fansar ka idan bakan? cewar shettima

a'a gaskiya ni kaɗai ne wallahi ba wanda yake karbar min amma  wataƙila ma ko ba wanda ya shigo ɗin daman tunanin  hakan nayi tunda de nasan nabar wajen shiyasa nayi tunanin hakan zata iya faruwa,

  "Sameer yace to munji wannan baka sani ba to ɗazu da asuba fa tabbas inma baka ga shigowar suba to kaga fitar su tundade asubace babu inda kakeje ko,

"tobbas ɗazu dana fito daga masallaci naga gate abuɗe alamun anfita nayi mamakin ganin sa ahaka sai nayi tunanin ko fitar gaggawa ce takama ko babu lafiya shiyasa aka buɗe aka fita kuma aka barsa ahaka saboda saurin da akeyi, kawai sai na rufe naci gaba da harkar gabana,

wayyo gaba ɗayan su babu wanda yaji daɗin wannan labarin shikenan yanzu inda suke tunanin zasu samu wata shedar yanzu ta ruguje gaba ɗayan su jikin su yayi sanyi duk atunanin su wannan abun bazai basu matsala ba sunso wanda yafita daga motar da shikenan bazasu sha walaha ba amma yanzu koman su ya dawo baya,

*dukan su jiki babu kwari haka suka sallame sa suka juya suka tafi part ɗin fulani suka nufa dan bazasu ƙara komawa gurin dadda ba ayaude baza ta ƙara ganin suba,

suna ƙarasawa da sallama ɗauke abakin su suka shiga ciki sameer ne yafara shiga yana shiga yayi karo da mutum kafin kace me ta tafi luuuuu zata faɗi yayi saurin riƙo hannun ta saboda ruwane awajen idan takai ga ƙasa zata ji ciwo,

mopping take yi afalon tana jin sallamar su kuma ta rikice ruwan ya zube a ƙasa zuyowar da zatayi kuma sukayi karo dashi ta zame zata faɗi yayi saurin riƙo hannun ta,

saura kaɗan numfashin ta ya ɗauke yin tozali da fuskar sa,

dagota yayi ta tsaya da ƙafafuwan ta amma saboda ba nutsuwa a tattare da ita  sai ta ƙara yin baya zata faɗi yaƙara riƙe ta yana mamakin wannan wacce irin yarinyace haka da bata da nutsuwa atare da ita kallon ɗaya yayi mata yagane ba nutsuwa atare da ita,

sakin ta yayi batare da yace komai ba ya ratsa ta gefen ta ya wuce bossay ne abayan sa kallon ta yatsayi yana tunanin inda yasanta yana kallonta yaga yasanta amma kuma yarasa a ina yasan ta ɗin,

  ahankali ya nunata da yatsa yace amma kamar na sanki ko ɗagowa tayi ta kalle sa atake ita kuma ta tuna inda tasanshi amma sai tayi saurin girgiza kai tace a'a tana sunkuyar da kai yace oh sorry kamace kawai wataƙil yana faɗar haka yayi wucewar sa shettima dake tsaye  ya harɗe hannuwan sa ya kafeta da ido yana jiran sugama shi yama manta da ita sai yanzu da suka haɗu,

kwata kwata batasan da tsayiwar sa ba agun amma jin kamar ana kallon ta yasa ta ɗago kanta caraf idon su ya haɗe waje guda cikin duburbur cewa tayi saurin janye idon ta ta juya zata bar wajen yayi saurin riƙo hannun ta tsayawa tayi cak batare da tajuyo ba dawowa yayi gabanta tare da kallon fuskarta,
Chapter 85 · 0% Book details