← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 139

Sashe 28

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan abu nagaba shine daga yanzu za ayi canjin aiki kowa zaibar akin da yake acanza masa da wani hakane zai qara bamu damar gano me yi mana sa ido....dan haka yanzu nan za afara ba tare da bata lokaci ba,
nan ta umarci dogare da fadawan sarki da sufara kiran mutane daya bayan daya aka ringa kiran su suna fitowa za atambayesu abun da sukeyi da kuma inda suke aikin idan suka fada sai ace to daga yanzu ga inda zaka koma haka aka ringayi har aka kai qarshe duk wadan da aka kira suna gefe,
gaban Azeema ne yafara dukan uku uku gani ita kadai tsulum aguri guda ba a kirata ba saboda ba asan sunan taba gashi mutane duk sunbi sun zuba mata ido suna kallon ta saboda kaf gurin in kacire mary babu wanda yasan da zaman ta agidan dan me gadin ma da yabarta ta shigo zuwa yanzu ya manta da fuskarta bazai iya gane taba,
duk sai take jinta atakure gashi ba ace mata ta tashi ba kuma tanaso ta tashi amma tana tsoron jawa kanta wani laifin sai da nasani fitowa take dama bata fito ba haka take ji gashi kuma wanda ta fito saboda shi bata gansa ba,
babu wanda yabi takanta har aka gama warwarewa.
wanine yaje kusa da fulani murya qasa qasa da ni kaina bansan me yace ba bayan yagama kitsa mata ya matsa gefe ya koma inda yabaro,
girgiza kai fulani tayi cike da qara tamke fuska sannan tace ina sarkin dorina matsowa yayi jikin sa na bari yace Allah qara miki lafiya Allah.......
   zai fara yimata kirari ta dakatar dashi cike da bacin rai tace aje afito min da Hamza da kuma wannan mutumin da suke tare har yanzu basu rabuba kenan aje afito min dasu yau za akoya musu hankali tunda basu dashi tafada tana ta faman hura hanci
da gudu sarkin dorina ya tafi wajen da yasan suna can,
bayan tafiyar sa fulani tasa aka kirama ta A Azeema jiki asanyaye ta tashi tazo kusa da ita tare da durqusawa kamar yanda ta ga anayi saida fulani tagama qare mata kallo kamar me son gano wani abun sannan daga bisani tace daga ina kike da iznin wa kika shigo gidan nan batare da sani naba tafada tana qara zuba mata idanu ,

itade Azeema tashiga tashin hankali batasan wane abu zatace dan jitayi jikin ta gaba daya ya hau bari kar taje ta fadi wani abu da zaisa agano qarya take gashi kuma  ko sunan wacce take zaune awajen tama bata sani ba bare tace ga gurin wace ta tazo,
tana cikin tunanin abun da zatace kamar daga sama taji ance maryama bakuwatace jiya tazo gaba dayan su suka juya suna kallon Ammah da ta qaraso wajen daman tasan za arina shiyasa tunda ta duba dakin taga batanan tunanin ta yabata watakil tace zata bi mary shiyasa ma hankalin ta yakasa kwanciya ta taho gurin da sauri gudun kar wata matsala ta faru ilai kuwa tana tunkaro wajen taji abun da fulani kecewa kuma bisa ga dukkan alamu bakuwar tata take tuhuma shiyasa tayi saurin katse ta ta bata amsa,

gaban fulani ta qaraso suna fuskan tar juna sannan tace ayi min afuwa ban sanar dake tun jiyaba daman bari nayi sai daddare sai inzo da kaina ma insanar dake,
kallonta fulani tayi sannan tace bakuwa daga ina nidai nasan ban taba ganinta a dangin kuba bare kice min yar uwarkice tafada tana qara maida hankalinta tana jiran taji amsar da zata bata,

dan murmushi tayi sannan tace ayya ai ba yar uwata bace daman kawaide wata qawata ce da muke mutun ci da ita shine tace min in taimaka inne mawa yar me aikinta aiki anan saboda ita bata da halin da zata riqe uwar ta riqe yar ga dan qaramin yaro agaban ta idan kuma tace yarinyar tabar mata gida to batasan inda zataba gashi kuma suna buqatar taimako dan me gidan ta ya rasu sannan kuma dangin ta bamasu hali bane name taimaka mata shiyasa tayi min magana nace mata ba matsala ta kawota baza arasa ba to kinji dalilin da yakawota gidab  kamar me nazarin wani abu haka ta tsaya tana kallon su suduka kafin da ga bisani tace to shikenan amma akiyaye nan gaba kafin wani ya kwana acikin masarautar nan yakamata ace ansan da zaman sa bawai kawai inganta ba Ammah tace in sha Allah za akiyaye yanzu gata nan idan da aikin da za abata sai abata in kuma babu sai inzauna da ita ashena tana taimakawa mary da aikace aikacen shiru tayi tana buqatar jin abun da zatace,

itama fulanin shiru tayi kamar bazatayi magana ba sai kuma can tace a'a da akwai daman yanzu ancanzawa kowa me aiki kema wacce take miki da ba it zata ci gaba da yimiki yanzu ba,

dan murmushi Ammah tayi duk da bahaka taso ba aranta amma afili sai ta nuna halin ko inkula fuskarta asake sai kawai tace to ai shikenan duk yanda kikayi ai daidaine ni zan wuce idan angama sai tazo ta kwashi kayanta ta fada tana juyawa tare da barin wajen,
da wani irin kallo fulani ta bita tana hararar ta dan haka kawai bata yarda da ita aranta tace basai in kin qara ganin ta ba zata zauna dani zan saka ido akanta inma qarya kike zan ganoki nan bada jimawa ba,
tana gama tunanin ta maida subanta ga Azeema sannan tace wannan amaida ta party dina anan zatana aiki daga nan kuma tace kowa yakama gaban sa kai tsaye kar wanda ya nufi inda yabaro yanu fi inda aka canza masa duk wani abu da yake buqata acan zata sa aje a amso masa daga baya amma bata yarda wani yake inda yabari ba,
haka aka ga ma yanke hukuci zama yatashi kenan amma ko A sarki bece ba sunan yana gun azaune amatsayin sarki saboda inde tana gurin bashi da bakin magana dole yayi shiru sai abun da tace dan koda wani abun yayi masa ba daidai ba to beda ikon tanka mata dande kawai kar ace masarautar ba sarki shine amfanin sa amma baya ga haka bashi da wani amfani aciki komai a hannuta yake sai yanda tace akeyi....

Kamar yanda tace hakan kwa akayi kowa ya nufi inda aka canza masa tare da raka ko wannen su saboda ba kowane yasan ko inaba aciki shiyasa tasaka akayi wa wasu jagora zuwa inda basu sani ba,
gurin yazamana babu kowa duk sun watse daga ita sai sarki sai muqarrabansu da zasu mara musu baya idan sun tashi tafiya saida taga kowa yatafi akan idonta sannan suma suka miqe dan barin wajen.
suna shirin tafiya kenan saiga su sarkin dorina tare da Hamza da baba suna qarasowa wajen dakatawa sukayi da tafiyar suna kallon su dan ita har tama manta dasu sakamakon maganar yarinyar nan da sukayi shine ya kawar mata da hankalinta akansu tama manta dasu gaba daya,

suna zuwa gabansu suka zube agabanta baba na gaida ita amma banda hamza ko motsa bakin sa beyi ba bare tasa ran zai gaida ta,
wani abune yazo mata wuya ya tsaya mata cikin hargagi da masifa kamar zata rufesa da duka tace kai gaka isasshe damai ko waikai dan gidan ubanwaye da uban me kake takama naga take taken yayi yawa agidan nan kullum rashin mutun cinka qaruwa yake naga alamar baka jin duka ko uban me ya hanaku fitowa saboda ba a isa daku ba hardaki tsofe tsofe dakai baka gudun abun da zai tabaka to kasani ko kadan baza kaban tausanyi da zansa a horaka ba cikin rawar murya baba yace wallahi banji ba lokacin da aka sanar ina bacci sai yanzu da akasa akiramu aka tasheni amma bada gangan nayi hakan ba kimin afuwa agafarce ni bada son raina hakan ta faruba yafada yana sunkuyar da kansa qasa,
banza tayi masa sannan ta mayar da dubanta ga hamza da duk abun zancen datake masa ya nuna kamar ma badashi take ba ko kallon inda take beyiba,
dubanshi ta qarayi tace kai kuma uban me kakeyi baka fito ba ko isarce tasaka qin fitowar,

sai alokacin tasamu yadago yana kallon ta ido cikin ido sannan yace bana jin dadine shiyasa banfito ba yana gama rufe bakinsa tace qarya kake shiru yayi be tanka mata ba qara harzuqata yayi tayi gaba kawai tacewa maidorina ya hukun tashi da dorina sannan sukashi dakin qasa tana gama fada ta tafi fuuuu kamar zata tashi sama sarki ma gaba yayi abunsa be saka musu baki ba,

Sarkin dorina matsowa yayi kusa da hamza amma yakasa daga dorinar bare ma yakita jikinsa saboda har yau tabon da yayi masa bai goge ba yana nan shiyasa yake tsoronsa kuma tunda ta tafi kwa ba abun dazaisa yadake sa gwara yabarsa zaidai kaisa godan qasan shima saida yace yaje amma bazai yarda yabisa ba gudun kar yaqara mazgesa a hanya
cikin lallami da lamana yafara yimasa magana kaga nifa ba dukanka zanyiba kawai katashi kaje inda tace din ni nabarka lafiya yafada yana saurin barin wajen gudun karma yayi masa wani jawabi tashi baba yayi yace ni bari intafi yaro kai kuma kaje inda yace maka din kar ka kuna jawowa kanka matsala tashi yayi shima yace baba muje ba inda zani inta isa tazo ta jani ta kaini wallahi matar inba bata bini ahankali ba sai na koya mata hankali(🤔uwar masarutar guda zaka koyawa hankali lalle wanga mutum akwai tsaurin ido yaseen nidai ba ruwana🤐 idan tajika),
Chapter 28 · 0% Book details