← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 139

Sashe 49

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"hmmm kawai tayi masa reply"
   baƙaramin haushi reply din nata yabashi ba amma ba yanda ya iya tunda shi yake nema haka yaƙara hauƙuri yace "zaki fito din?
  " a'a tace masa,
Why ? ya tambaye ta abun haushin kawai sai yaga tama sauka a online din,

mutuwar tsaye yayi agun tare da tsurawa message din da yatura mata ido  lalle ma yarinyar nan mai ta maida shi suna magana tasan kuma basu gama ba amma tasauka karkada kai yayi tare da cije bakin sa aransa yana ayyana kalar rashin mutun cin dazai mata batasan ko shi waye ba 🤔,
haushi kamar yakasheshi haka yake ji zuciyarsa har wani zafi zafi take masa da radadi,
kashe wayar yayi ya mayar aljihu yana tunanin irin wulakan cin da zaiyiba su shettima dan duk su sukajawo wannan yarinyar take wulakan tasa dabasu turo shiba da tuni hakan bata faruba da girmansa da komai amma yazo wata banza can tanayi masa abun da taga dama,
babu wanda baiji haushin sa ba acikin su musamman ma su bossay  sai kace su sukayi masa abun da tayi masa din,
cike dajin haushin yajuya dan bazai ƙara yimata magana ba tafiya zaiyi gwara yaje subi ta wata hanyar amma ba wannan ba,

juyawa yayi yafara tafiya har yadan yi taku waken biyar kawai yaji ƙarar bude ƙofar amma takaici bazai barsa ya juyo ba dan haka kawai yaci gaba da tafiya ya nufi wajen da sukayi parking,

  "tsayawa tayi tana kallon bayan sa farace doguwar bata da jiki kyakkyawa ce ajin farko  sanye take da wani maroon din hijabi har ƙasa dan hakama ganin kalar kayan da yasaka saboda ya rufe mata har ƙafafun ta,
tunda yajuya yafara tafiya take bin sa da kallo tabbas ta yarda kuma tana zaton shine wanda suke chart dashi yanzu daman ta fito ne dan ta tabbatar kuma ta tabbatar din batayi masa magana ba itama ta daga ƙafarta ta fara bin bayansa,

loƙacin data ƙarasa wajensa yasaka hannu ajikin motar zai bude,
" sai tayi sauri  ta danyi gyaran murya tare da cewa nace ba... tsayawa yayi da ƙoƙarin buɗe motar da yake yi sannna ya shiga juyowa ahankali   har yaƙara sa juyowa gaba daya yana fuskantar ta ƙurawa juna ido sukayi na ƴan daƙiƙu ita tafara janye nata idon daga garesa,
ahankali tace kaine wanda muke chart yanzu?
tayi maganar batare da ta kalle saba har yanzu kam shi baidauke idon sa daga kanta ba ,
  jin shiru baibata amsaba yasa ta dago dara daran idon ta takalle sa ganin ita yake kallo yasata sauri ƙara kawar da nata dan bazata iya jurar kallon sa ba,

juyawa tayi da niyar barin tunda yaƙi magana,

"eh nine'  taji ya bata amsa juyowa tayi ta kalle sa tace to gani  idan kuma baka da abun cewa intafi,
  "wani abu yaji yazo masa wuya amma sai yadaure tare da basarwa harda ƙaƙaro murmushin dole yayi mata tare da cewa agafarceni sarauniyar mata kallon kine yasani manta a inda nake dan Allah inbaza ki damuba mushiga daga ciki sai mu tattauna ingabatar miki da abun da ya kawo ni gareki gimbiyata,
tundaga kan ƙafarsa tarar kallon sa har kansa masha Allah tace aranta tare da fara kokonton anya kuwa wannan ba batan kai yayi ba kyakkyawa dashi amma yace yana sonta to a inama yasanta itade tunda take bata taba ganin saba ko a mafarki to komade meye gaskiya fa ya hadu iya haduwa tunda taganshi taji yamata ya burgeta yagama tafiya da imanin ta(tabb kina ruwa kam) saidai tasan ba class din tabane dan ta tabbata yafita komai kyau da kudi tunda alamu sun nuna hakan ajikin sa da kuma kalar kayan dake jikin sa gayen yayi ta ko ina baida makusa,
amma fa saidai duk da haka bazata bari yagane hakan ba gudun kar ajinta ya zube gara itama ta nuna mishi tana da class kar yarainata,

      "Hy yace mata tare da daga mata hannu asaitin fuskarta,
hakan yasata dawowa daga tunanin datakeyi ,
      dan kallon sa tayi sannan tace a'a duk maganar da zakayi kayi ta anan inajin ka basai mun shiga ba,

"hmm yace aransa tare da watsa mata kallon banza afakaice batare da ta gani ba,sannan yace "haba gimbiyata ai ba girman kibane ace kintsaya anan kowane yana wucewa yana ganin ki hakan be dace dake ba yakamata mushiga ciki hakan sai yafiye mana safe ko ya kikace ammafa idan bakyaso shikenan bazan takura miki ba duk abun da kike so shi za ayi kawaidai cancanta na nuna miki gimbiyar mata,

har cikin ranta taji dadin kalaman sa da fasa mata kan datayi tabbata wannan muƙamin da take ganin batakai matsayin nan ba,
  jin tayi shiru yasashi cigaba da cewa kyakkyawa ta bakice komai ba nifa inason inji kina magana domin ba ƙaramin dadi nake jiba idan naji muryarki yakamata  ace kitausayawa wannan baƙon naki wanda yagama mutuwa akan sonki dan Allah karkice a'a kitaimaka mushiga ciki muyi magana nazo da alkhairi gare ki,
yana ƙarasa maganar bai jira cewar taba kawai  ya bude mata back seat yace Bismillah sarauniya ta tafaɗa yana kafe ta da ido da yasata takawa batare da ta shirya hakan ba kamar wacce ake control din ta haka taji gaba daya yagama kashe ta da kalaman sa batasan lokacin da ta shiga cikin motar ba kawaide ta ganta aciki,
  tana shiga ya rufe ƙofar tare da sauke boyayyiyar ajiyar zuciya ahankali ya furta Finally mungama dake,
sannan yazagaya ta dayan barin inda take ya bude ya shiga yana shiga ya rufe ƙofar tare da kafe ta da idanu hadi da sakar mata wani irin murmushi me cike da ma'anoni da ita bata gane hakan ba,
murmushin da yayi har cikin can ƙasan zuciyar ta taji shi juyar da kanta tayi tana kallon window tare da sakin nata murmushin da bata san tanayin sa ba,

shikuma hakanne yabashi damar zaro hanki din dake gefen kujerar ya lallaba yasakama ta a hanci kafin ta juyo ta kalle sa har ta sume luuu tayi zata fada jikin sa yayi saurin janyewa yana wani ya tsina fuska kamar yaga abun ƙyanƙyami haka ya kwantar da ita kan kujerar,
kallon fuskarta yayi na yan sakanni sannan ya kawar da kansa  tare da buha tsaki sannan yabude murfin motar ya fita daga ciki yazagaya yashiga driver seat tare da yiwa motar key yayi reavers ya nufi inda su shettima suke jiran sa..........✍️✍️

💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓
[6/2, 11:30 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

         *💖the talent troupe💖*

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                         🅿45&46

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

        "kallon fuskarta yayi na yan sakanni sannan ya kawar da kansa  tare da buha tsaki sannan yabude murfin motar ya fita daga ciki yazagaya yashiga driver seat tare da yiwa motar key yayi reavers ya nufi inda su shettima suke jiran sa..........✍️✍️

  Yana ƙarasawa bakin kwanar sai yaga baigansu ba hange hange yafarayi daga cikin motar amma baigansuba wani haushinne yaƙara kama shi tsaki yaja aransa yana tunanin kuma ina sukayi, cike da takaicin rashin ganin nasu yadauko wayarsa yakira shettima, ,,"kuna ina ne? yatambayesa bayan yaɗaga wayar,
bayan yabasa amsa kawai ya kashe wayar tare da jan motar yayi gaba yana cikin tafiya ya hango su can wajen titi atsaye,
   agabansu yayi parking din motar tare da yi musu horn atare suka juyo gaba ɗayan su ganin shine yasa shettima saurin bude gaban motar ya shiga tunka yagama shiga yake tambayar ta ina?
shigowar sa  idon sa ya sauka akan ta hakanne yabashi damar samun amsarsa batare da sam yabasa amsa ba,
bossay ma bude bayan motar yayi ya shiga  inda take, bayan ya rufe sameer yaja motar batare da ya kula kowaba ko kallon inda sukema baiyi ba saima ƙara hade rai da yayi shi adole bazai kulasu kar su samu damar yin wata magana shiyasa ya ɓata fuska gudun raini, saidai abanza dan hakan da yayi bai isa ya hanasu tambayar saba,bossay ne yafara yi masa magana dacewa  gaskiya aikin ka na kyau kace har ka ƙwmus ta kenan yafada yana kallon fuskarta da dan fara'a a fuskarsa yaƙara dacewa wannan ai tsaf zaka iya kidnaping mutane batare da bata lokaci  dan naga alamar zaka iya fiya da hakama koma waye zaka iya kwamishewa,
da sauri yajuyo ya kalle sa sannan ya mayar da hankalin sa ga tuƙin sa da har zai tanka masa saikuma ko me yatuna sai yayi shiru kawai yacigaba driving din sa,
    jin yayi shiru yasa shettima cegaba da cewa kai da angaya maka shidin nawasane ai tunda yaje dolene ta mutu akansa musamman ma da yayi mata kalaman sa nasan baiwani sha wuya ba wajen shawo kanta amma de abun tambayar anan shine dadewar me kukakyi tundazu kabarmu muna jira wallahi ƙafata har tafara ciwo saboda tsayuwar da kabarmu muna yi,
dan gayamana abun da kace mata ta yarda ta shigo motar da wane kalami kayi alwala kadan bamu musha(murmushi yayi tuna inda yasan kalmar dan bamu musha)

wani irin harara ya aika masa da ita can ƙasaƙasa da murya yace me ya hanaku zuwa kugani daga nan yayi shiru yasan idan ya biye musu ransane zaita ɓaci  dan ba barinsa zasuba agaba zasu sashi suyi ta tsokanar sa saboda yaga alamar sungama rainasa,

     cigaba yayi da tuƙin sa tare da ƙarawa motar gudu,
    yana jinsu sunata tsokanar sa suna dariya amma yaƙi ya kulasu duk abubsu dole suka hakura sukayi shiru da magana saboda sukai kiɗan su suke rawar su,
Chapter 49 · 0% Book details