← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 139

Sashe 123

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

saida suka gama nunawa kansu farin ciki sannan kowa ya koma ya zauna dan aƙarasa maganar saida suka samu nutsuwa sannan papa ya gyara zama ya ƙara yiwa Allah godiya da bayyanar ahalin sa sannan suma su maama yabasu labarin abun da ya faru na halin fulani duk abun da ya faru tundaga A har Z yabasu labari,

sannan ya ɗora da cewa Maryama muna sauraron ki muna buƙatar ƙarin bayani daga gare ki, ki matso kiyiwa kowa bayanin yanda hakan ta faru batare da sanin kowa ba kika yaudareni da ɗan da banaki ba koma ince kika yaudari duka masarauta,

shiru gurin yayi ba wanda yayi magana Fulani kam ta sunkuyar da kanta ta kasa ɗagowa ta haɗa ido da kowa duk da idanun su nakanta suna jiran jin ta bakin ta,

saida papa yaƙara yi mata magana cikin daka mata tsawa sannan tayi saurin ɗagowa da jajayen idon ta da suke ta zubar da hawaye ajere ajere ta kalle sa tare da kawar da kanta gefe saida ta ƙara ɗaukan loƙaci...,

sannan ta rarrafo jiki ba ƙwari tazo gabansu saikawai ta fashe da wani kukan me sauti kowa cigaba yayi da kallon ta ganin taƙin yin shiru yasa Meer cewa Kee... kishiga hankalinki kin ishemu da haukan kuka in ba hakaba wallahi zanyi ball dakeeee... yayi maganar cikin daka mata wata gigitaciyar tsawa da saida fadar ta amsa gaba ɗaya wasu daga cikima da badasu akayi wa saida suka firgita bare kuma wacce akayi wa ai saura kaɗan ta sakin fitsari agun,

ba shiri kuwa ta buɗi baki tafara magana....., "dan Allah kuyi haƙuri ku yafemin wallahi sharrin sheɗanne duk yasa na aikata hakan ba bada son raina ba ina mai baku haƙuri abisa cin amanar ku danayi amma wallahi wallahi bansan komai ba game da fitar gimbiya sabreena ba babu saka hannun aciki kamar yanda kuke tuhumata wallahi bani nace yanzu zan faɗi duk wani abu da nasan na taɓa aikatawa, shiru tayi na ƴan mituna sannan ta cigaba da cewa,

"tabbas wannan ɗa da nake dashi bani na haifeshi ba kamar yanda hajiya sarah tafaɗa muku haka zancen yake,

shekarun baya tun kafin gimbiya sabreena tabar gidan Hajiya sarah tazo min da wannan maganar daman ƙawatace tun kafin inyi aure maƙociyar muce muna shiri da ita, to bayan nayi aure ma tana yawan zuwa gidana ranar wata lahadi tazo gidana sai tace mushiga ɗaki tana da wata shawara da zata ban muna shiga tafara tuntuɓata akan rashin haihuwata nace mata nima abun yana damuna gashi munje wajen likita ance bazan taɓa haihuwa ba shine tace yanzu hakannan zan zauna bani da ɗa babu abun da zan samu idan sarki ya mutu shine tace to wallahi in tashi tsaye insan abunyi dan idan na zauna kallon kwaɗo zai miki ƙafa ga wata shawara da zan baki kiyi tunani akai ta hakan kawai zakibi kisamu wani abun koda bayan ran sarki,

gyara zama nayi nace ina jinta tagaya min shine take cemin mai zai hana muje wajen malami yabani abun da zaisa kowa yaga ciki ajikina alhalin babu shi kawai za arufewa kowa ido yaringa ganin ciki ajikina har zuwa loƙacin da watan haihuwar zaiyi sai muje asibiti sai abiya likitocin kuɗi subamu wani ɗan sai anunuwa kowa cewar na haihu kuma yaron koda yayi wani kammanin da ban babu wanda zaiga hakan babu mecewa komai akai ,

da farko ƙin amincewa nayi haka taita jan ra"ayina har na amince washe gari mukaje wajen malam babu ɓata loƙaci muka gaya masa buƙatar mu nanda nan yabamu magungunan da zamuyi amfa ni dashi sannan yaban wata ƙwarya yace aɗakina akwai wani guri da yake kamar ɗaki inje insan yanda zanyi inyi haƙa in zura ƙwaryar akai sannan yaban wasu jajayen kaya yace kullum idan na tashi inshiga ciki inyi fitsari akai sannan duk sati idan zan shiga gurin in tafi da dubu ɗari in ajiye agun sannaan in fito, nace har sati nawa zanyi ina ajiye kuɗin agun yace haka zantayi har ƙarshen rayuwata nace masa a ina zan ringa samun kuɗin Ni da ba sana'a nake ba kuɗin gurina kuma ko shekara ɗaya bazaikai ba sai yace min kar in damu da wannan akwai inda mijina yake ajiye kuɗin sa aɗakina dan haka daga nawa sun ƙare inci gaba da ɗaukan nasa ina ajiyewa konawa na ɗauka bazai taɓa ganewa ba kuma ya sheda min inda nayi hakan ɗan da zan haifama zai iya kasancewa shine sarki idan mijina ya sauka shi zaibawa sarautar dan haka sarauta zata dawo hannun sai yanda nayi da kowa duk abun da nafaɗa shi za ayi, nikuma wannan zancen da yayi na sarautar zata dawo hannun gaba ɗaya yasa nayi saurin amince masa zanyi duk abun da yakeso daga nan nabiyasa kuɗin da yake buƙata aloƙacin sannan yayi mana bayanin duk yanda zamuyi komai muka baro gurin sa muka dawo gida tundaga nan kuma nafara duk abun da yace min inyi ba daɗewa kwa na sanar da sarki ina da ciki tun baifito ba mukaje wajen likita aka dubani aka tabbatar wa da sarki eh ina ɗauke da ciki wata ɗaya muka dawo gida aka sanar da kowa nan da nan aka fara tayani murna loƙacin kuma da nake da cikin gimbiya sabreena har ta haifi ɗan ta sameer kuma Ammah ma ta haifi ƴan biyun ta mata ni duk danaga gimbiya ta haifi namiji banji cewar wai ɗan ta zai iya zama sarki ba bare har inyi tunanin koren ta daga gidan, tunda malam yasanar min na yarda dashi ana haka kuma tun kafin in haihu muka wayi gari babu gimbiya ba ɗanta aka neme ta aka rasa, nikuma bayan watan haihuwa na yacika Hajiya sarah tazo mukaje asibiti tun kafinma muje tace angama komai tayi magana da likitan da zaibamu wani ɗan haka muka shirya komai kamar haihuwar gaske muka tafi asibitin mu biyu nandai tasan cuku cuku ɗin da tayi ta samo yaron ta kawo min shi ina zaune awani ɗaki dan bansan ma ta yanda ta samo shi ba anan muka sanar da dangi da ƴan uwa cewar na haihu ga mamakina sai naga abun da malam yace ya tabbata dan yaron kwara kwata baya kama da kowa amma babu wanda ya iya cewa wani abu game dashi har muka dawo gida akayi suna aka saka masa SALAHUDDEEN...,

bayan girman sa kuma da sarki zaiyi murabus akace shi za aɗora akan karagar mulki ranar har kyuata nayiwa Hajiya sarah da malamin saboda farin ciki,

har ranar naɗasa akai tayi aka basa sarauta Saida abun da bansani ba shine tunda ya hau sau halayen mu daga shi har ni suka sauya kawai sai jnringajin zuciyata na ingizani ina yawan samun kaina cikin ɓacin rai daga bayama sai kawai Masarautar ta sauya min gaba ɗaya aka dawo cutar mutane da zalintar su wasu basuji ba basugani ba haka zansa ayiwa mutum hukunci fiye da laifin da ya aikata ni kaina abun yana damuna idan na zauna ina tunani ammafa maimakon inji abun yaragu saima inji ƙaruwar sa araina har takamam hakannan mutum baiyi laifi ba hukunta shi daga bayama har zubar da jini nasa aka farayi amma ni bazan taɓa hukunta mutum da hannun naba saidai insa ayi idan akayi kuma zuwa dare sai abun yafara damuna amma zuwa safiya zan cigaba da abun da nake bana saurarawa kowa ko shi mijin nawa sai abun da nace masa yakeyi idan ya kwatanta yimin magana akan abun da nake ba daidai bane sai raina yaɓaci kuma shima sai inga yakwanta yakama bacci sannan nake jin daɗi har zuwa yanzu da asirina ya tonu amma wallahi wallahi iyaka abun da nasan nayi kenan banda saka hannun wajen cutar das.........,bata ƙara sa maganar ba taji tasssss taji saukar mari afuskar ta bata gama tantance zafin ba aka ƙara mata wani ta ɗayan ɓarin bai dakata ba saida yayi mata wajen mari biyar ajere sanann su waziri suka tashi suna rirriƙesa da hannu ya nunata cikin ɓacin rai yashiga nunata da yatsa cikin ɗaga murya yace ƙarya take mu zata rainawa hankali kusake ni in ɓaɓɓalla ta mai yasa zaku tsaya kunajin wannan banzan labarin ƙaryar kusake ni inyi nece yafaɗa yana ɗaga musu murya sama tare da yin watsi dasu ya ƙwace daga riƙon da sukayi masa cikin zafin nama yaƙara nufar inda take, a zafaffe cikin zafin nama shima Abu ya miƙe tsaye tare da ɗaga murya da ƙarfi yace "MEER.......!!!!!!

   '
                     💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
     👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
       by(ster lady)

*2,GIDAN AUNTY*
       by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
      by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
      by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
       by(mum Sayyid)

*6,BABY  
      by(mhiz innocent)
[27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️ 96

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

     'Cak meer yaja burki yatsaya baiƙarasa  gurin taba sakamakon tsawar da Abu yayi masa hakan yasan yashi dakatawa bai ƙarasaba,

maama ce ta taso ta matso kusa dashi tare da kamo hannun sa tajasa ta zaunar dashi kusa da ita tace "ya isa haka kowa ya zauna, sannan sauran ma da suka tashi tsaye suka koma suka  zauna papa dai yana gurin sa azaune ko motsawa baiyi ba,

shiru gurin yaƙara ɗauka sannan gwaggo tace "nimadai bazan taɓa yarda bake bace tunda har kika  iya aikata haka babu abun da baza ki iya aikatawa ba bazamu yarda da wannan ƙazon kuregen labarin ba ke kika fitar da ita dan haka dole kifito kigaya mana ta yanda kika koreta daga gidan yanda kika faɗi wannan shima haka mujeso kigaya mana ki amsa laifinki tunwuri kar ki wahalar da mu da ki wahalar da kanki,
Chapter 123 · 0% Book details