← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 139

Sashe 110

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gaban sa taje tare da dago da kansa tana kallon sa tare da sakin wani shu'umin murmushi tace to karamin dan iska ina cika bakin naka yaje waye yau agaban mutane cikin mawuyacin hali kuma yanzu zan saka arabaka da duniyar ma gaba daya bance kafita hanyata ba bance karka sake shiga gonata ba amma bakajin magana kullum cikin nuna isa da takama kake kaidin waye me kake dashi me katara me ka ajiye me ubanka yatara me na kasa yaci bare yaba na sama kaidin asararre ne kazo a asara kuma zaka koma asara,

tana gama fadar haka ta mike tare da canza kalar fuskarta ta koma ta marassa imani ta kalli sarki tace amatsayina na mahaifiyar ka ina umarrar ka da kakasheshi da hannun ka so nake kasa wuka ka fillemin kansa anan gurin kafin kafara ina so wani ya fito ya fara saukewa tsohon nan kansa a fille masa kai agaban sa in ya isa ya hana sannan ga budurwar sa nan tunda ita yakeso ina so itama akashe ta agaban sa sannan adawo kansa sarki da kansa nake so yayi min wannan aikin hakan sai yafimin farin ciki inaso dan da nahaifa acikin cikina ya daukar min fansar cin zarafin da wulakan ci da rainin da yake min inga jinina ne zai kashe shi ina fatan kungane,

"bamu gane ba muna bukatar karin bayani maryama,

da sauri fulani ta juya jin muryar da bata taba tunanin jintaba agurin,

kafin fulani tace wani abu matar tayi saurin dakatar da ita tare da cewa kisa akunceni,

cikin tsawa sarki yace baza a kunceta ba mama yanda za akashesu itama yazama dole asauke kanta anan gurin,

fulani ce tayi saurin daga masa hannun tare da cewa ya isa haka kar nakara jin muryar ka anan,

da kanta taje ta kunceta tana cewa wai ya akai waye yayi miki haka me kike yi yaushe ma kikazo bansaniba,

banza tayi da ita tana kunceta ta mike tsaye itama cikin bacin rai ta kalli fulani tace ki gaggauta sawa akunce wadannan mutanen gaba dayan su,

fulani itama cikin bacin ran tace akan wane dalili zakice haka,

kedai kawai kiyi hakuri akan abun da yayi miki acikin rashin sanine baidan matsayin ki awajena bane amma hakan kar yasa wai kice sai ansakesu wannan hukunci ne da nariga na yanke tun wuri kuma dole a zartar dashi babu wanda ya isa ya hana tayi maganar cikin daga murya, kuma hurumin ki bane meye alakar ki dasu kima canza magana wadannan mutanen dakike gani ba mutanen kirki bane basu da mutun ci ko kadan basu sansaba musamman wannan dan iskan yaron da yagama rainamin hankali yau dole ya karbi abun da ya dade yana aikatawa,

ko kuma ke ki karba ba nace masa kisake shi wallahi aka kashe shi sai namiki abun da baki taba tunani, matar take fadawa fulani tare da kada mata hannu afuska,

bakaramin mamaki fulani tayi ba da jin batun ta aikam cikin bacin rai tace sarki afara takansa yanzunnan tagani agabanta,

dariya matar tasaka tace da kwa kin tafka babban kuskure arayuwar ki ko kina tunanin alakawarin da na daukar miki yakai karfin da bazan iya karyawa ba to kiyi abun da nace miki inbaha ba kuma hmmm kinsan mai zaibiyo baya, dan dagatawa tayi sannan taci gaba dacewa ko dayake karfin alkawarin ne yasa nakai har yanzu ina danne wa to kar kibari ki kaini karshe da hakan zai gagara rikewa agareni yanzuma ba karamin kokari nayi ba wajen danne duk abun da yafaru agaba na batare da na dau mataki ba amma daman nafiso inma rashin juriyar ne da daukar mataki to yazamana agabanki ne kuma gaki dan haka idan baki dakatar da komai to nimafa kisani zanyi abun da yadace ina fatan zaki gyara barnar da kike shirin yi domin idan baki gyara wannan ba to waccen ta tashi daga gyaran da take kina bata wannan waccen zata baci gaba dayanta ina fatan kin fahimce ni da kyau, takarasa maganar tana watsa mata wani irin kallo me cike da gargadi,

cike da bacin rai da fulani ta dade batayi irin saba muryar hardan dasdaskare wa take ta daga murya da iya karfin tare da tsawa tace HAJIYA SARAH.....!!!!! batare da ta sausauta murya ba tace yakamata ki iya bakin ki kisan abun da yakamata kiringa fada anan gurin domin nan bada gani sai ke bane awajen ki gaggauta janye wannan bukatar taki saboda ba mai yiyuwa bace ki canza wata bukatar taki amma ba wannan ba,

juyowa hajiya sarah tayi cikin sanyin murya tace "ni kuma wannan bukatar nake so kuma dole ayi yanda nake so,

kamar fulani zata rufeta da duka ta kara daga murya kamar zata cire mako garon ta tace SABODAME DOLE SAI WANNAN......?

itama hajiya sarah cike da daga murya kamar yanda tayi mata itama tace SABODA DANA NE...!!!

dif gurin yayi bakajin motsin komai sai can daga baya fulani ta dan saki murmushin mamaki sannnan cike da rashin fahimta fulani DA kuma bangane ba yi min bayani yanda zangane kodai kinsha wani abunne kafin ki taho inaga,

babu abun da nasha wannan dai yaro dakike gani dana ne inbaki yarda ba kuma ki kallesa ki kaleni zaki ga kamar da muke indai kuma ba dusace a idon ki ba ko dayake naga alama da dusa acikin idon ki shiyasa tun wuri kika kasa gane hakan duk tsawon zaman da mukayi dake kuma kukayi dashi amma baki iya ganewa ba kinga kwa bazaki taba ganewa ba,

kamar yanda tace ai bama iya fulani ba gaba daya mutanen wajen sai da suka shiga kallon su ba karya kam suna kama kana gani zaka gane hakan,

jin fulani takasa magana yasa ta shiga zagayata tare da cigaba dacewa "duk wani abu da yake miki ninake sakashi kuma kamar yanda nagaya miki baisan komai ba to baisani ba din nice na dorasa yaringayi miki duk abun da kika ga yanamiki kuma ni nacire mishi tsoron ki sannan nasa karyaji tsoron kowa daga ciki hardake idan kuma kika zafafa ta kura masa yace miki zai tona miki asiri idan yace miki haka zaki daina takura mishi sannan yana da damar dazaiyi duk abun da yaga dama zaiyi sa batare da an dakatar dashi ba ke kinsan baisani bane dan da yasani wannan wahalar da aka bashi da tun kan afarata ma zai kunce miki zani sanin shi yarone bazai iya rikewa ba yasa naki gaya masa saboda ban taba tunanin irin wannan ranar ba amma da tuni na sanar dashi ke kinsan ko ni wacece duk abun da zanyi a lissafai nake yinsa shiyasa nasa aka kawoshi nan tun yana yaro inbaki saniba kisani duk zuwa gidan nan da nakeyi bawai dan ke nakeba dan shi nake kuma nayi hakane dan insakashi yasaka min ido akanki duk abun dakike yi akan idonsa ko wannan ranar batazo ba daman daf nake da toma miki asiri sai kuma gashi kin jawo lokacin da kanki dan haka lokaci yayi dole kowa yasan abun da kikayi tsawon lokuta,

jikin fulani ba karamin sanyi yayi ba kuma ta tsorata sosai da maganganun hajiya sarah duk da tana tunanin duk barazana take mata ba iya fada zatayi ba kawai kurarine amma saboda kar yan gurin suyi zargin wani abun sai kawai ta basar tashiga dariyar borin kunya tare da cewa au sharri kuma zaki min ni nake da wani siri to in baki fasa fada ba ba kya tsoron Allah,

"au haka kika ce?
"eh haka nace,

girgiza kai hajiya sarah tayi tana so ta fada amma idon wani dake kallon ta a filin wajen cike da gargadin ta kar tafada yasa tayi shiru taka sa fada amma da dan fulani ne da tuni ta dade da fada amma idan aka kaita karshe wallahi sai ta fada saidai duk abun da zai faru yafaru amma sai ta fada,

ganin tayi shiru yasa fulani sauke ajiyar zuciya a boye tasan daman bazata iya fada ba kurarine kawai amma saboda kar taje ta fada din idan tasa akashe mata da tasan dole zata fada dan haka ta juya kamar ba ita ba ta kara hade rai sai tace yanzu adakata da hukun ci akan yaron nan sai nakara bincike akan sa kafin azo ayanke masa nasa hukuncin mai muni da yafi kisa tare dashi da mahaifiyar tashi abisa kazafin da tazo tayi min agaban ku wani satin irin rana tayau za ku dawo azartar musu da hukun ci agaban ku,

maida dubanta tayi ga sarki da ya riga da yazaro wuka jira yake kawai takara basa umarni yakaita kan hamza sai kuma yaji wannan batun ransa yaji yayi mummunar baci dan haka tunda yazaro ta bazai baza ta koma ba sai tasha jinin wani,

yanda take kallon sa shima haka yake kallon ta tasan ne yake shirin yi dan haka tsce masa "ka kwantar da hankalin ka ai ga wasu nan ka dauki daya acikin su kabawa wukar ka abinci nasan tunda tafito sai tasha zata koma,

kawar da idonsa yayi daga kanta tare da matsawa kusa da Azeema har yadaga wuakar zai sauketa akanta sai kawai maganganun hajiya sarah suka shiga dawo masa maganganun da tayi masa akan baba hakanne yasa yafasa da Azeema yanufi inda baba yake saboda yana so ya kasheshi yaga abun da ta isa tayi masa,

yana zuwa yadaga ta zai sauketa yaki anrike masa hannu da mamaki yashiga bin hannun da kallo mamaki ne yakara kamasa wai mai wannan matar take nufi dashi ne duk inda akace za ataba sai ta hana,

bashi kadai bama kowa kallon ta yake cike da mamaki sarki guda ta rikewa hannu lallai ta wuce gona da iri wuyan ta ya isa yanka,

shikam baba yarufe ido dan har yafara kalmar shahada ya riga da yagama saddakarwa ya mutu,, sai kuma yaji shiru,

Azeema kam jikinta sai rawa yake muryart ta dashe tanaso tayi ihuma amma miryar ta taki fita sai uhm uhm take hawaye ma rahama ne amma sobada tsabar tashin hankali sun kafe sunki zubowa so take tayi ko zata samu sassauci Amma suma sunki fitowa,

fulani ce tace hajiya sarah wai lafiyar ki kalau me yake damunki me yasa kikeyin irin waddannan abubuwan kinsan kwa wa kika rike,
Chapter 110 · 0% Book details