← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 139

Sashe 15

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta yace lallema tsohuwar nan ke har kina da bakin cewa wani tuzuru bayan ga qaton gardin tuzuru nan agaban ki kibari idan kika fara kawar dashi saiki cewa wani tuzuru koda yake ma wanna ai a tuzuran ma riqaqqe ne ya ruqa kamar dan yar kubewa kinsan kubewa ce idan ta riqe ko yankuwa ma batayi saidai a jefar dan bata da amfani to shima haka yake dan ko tsohuwar bazawara aka bata sadakar sa ma bazata karba ba saidai ko kinemo masa wata yar tsohuwara ahadata da Allah da kudade sannan tadan lallaba tayi maleji dashi dan sai tayi hakuri in kwa bahaka ba to saidai ya mutu ba aure, be ankara ba yaji saukar filo afuskar sa da qarfi zai dago kenan yaqara jin wani haka sameer da yabarsu agun tun dazu yakoma kusa da papa yazaun yana jinsu da bayi niyar tanka masa ba amma yaga abun nasa yayi yawa shiyasa ya dauki filulli kan yafara jifansa dashi saida yaga sun qare gaba daya sannan ya dakata, Ammah ce ta daga hannuta itama tana kaima sa duka ta ko ina tare da cewa bakin ka ya sari danyan kashi saodai kagani akan ka amma bade akansa ba nan da watanni ma zaka gansa da zankadediyar budurwa kai kuma saidai ka qare a tsohuwar bazawarar daman dasu ka dace ba budurwar da zata kulaka inda tana da hankali saidai ko in makauniya ce bata gani sai acuceta ahadata dakai amma me lafiyade cikakkiyar me hankali bazata yarda ta aure ka tana fada tana dukan sa a qirji, Shikam ko ajikinsa dukanta ko kadan bajinsa yake ba yana ta faman dariyar sa saida yaga dan kanta tagaji da dukan sa ta cire hannu tare da yin kwafa zata bar wajen yayi saurin ruqo hannun ta tare da kafeta da ido yana dan murmushi yace kema kinsan fade kike dan kinganni dan saurayi dani kinga kwa yanda 'yan mata suke rubibi akaina hmmm ba a magana zan kawo mikima kizaba min danni sunyi min yawa narasa wacce zan dauka aciki shima yagaya miki wace macen ce take sonshi duk wace ma yace yana so sai ta gudu tace bata son tsoho ita saurayi take so kamar ni fisge hannun ta tayi daga riqon da yayi mata tana galla masa harara sannan tajuya batare da tace masa komai ba saboda ya kaita qarahe bata da abun da zatace kuma tarama cin fuskar da yakewa sameer qarasawa tayi wajen sameer itama ta zauna shima shettima man yana dariya yabiyo bayan ta inda ta zauna ya zauna kusa da ita yace yana satar kallon ta sannan yace madam nifa yunwa nake ji kitashi ki bamu abinci musamman ma tuzurin ki ba inda zaije abashi abinci sai wajen ki nikam banda matsala yanzu ina nan ma idan na dau waya nayi kira nace akawo min ana rawar jiki za akawo min har inda nake Allah sarki shikuma saida taimakonki sai kun hada masa da li'ilafi wannan baqin jinin yayi yawa yana fada ya dubi inda sameer yake azaune ya hade rai kamar anyi mishi albishir da wuta ganinsa yayi yana nannade hannun rigar sa yana shirin tashi daga gurin alamar de zaiyo kansa yana ganin hakan yayi saurin tashi ya koma kusa da papa yana buya agefen sa yace papana kayi masa magana kar yatabani inzo in karyashi dan inya tabani ba barin sa zanyiba saboda ni ba sa'an sa bane nafisa qarfi dariya papa yayi yace to ai shikenan tunda kafishi qarfi kuma yasani ai rabudashi kawai yazo sai ka koya masa hankali ko a'a papa ai banason kuzo kuce naci zalinsa ne shiyasa bana son indake shi papa yace mun yarda ba komai mu sai mu bar muku ma wajen kudan dan batu kaga daga yau baze qara tunkarar ka da fada ba to nide a'a Ammah to ke kisa baki tunda papa yaqi ji itama tace bazan ba din nima nagoyi bayan sa to shikenan zaku gani tunda duk kunqi yimasa magana yana kaiwa nan sai yatashi yayi saurin komawa kusa da sameer akunne yarada masa yi hakuri nifa bada kai nake ba da waccan tsohuwar nake ture sa yayi daga kusa dashi yace to ni ina ruwana ko kaji tunda kafara nace wani abun yace a'a to amma meya nade hannu riga yace ganin dama yafada yana hararar sa tare da kada kai shi kadai yasan ta inda zai rama wannan abun da yayi masa shiyake cewa tuzuru zai kamasa ne nan gaba yanzu beda lokacin sa, ganin kowa yayi shiru yasa Ammah tashi tace dan lelena rabuda shi bari inkawo maka abinci kai kadai shikuma yatafi wajen bazawarar tasa yaci tafada tana tafiya shettima ya bude baki kenan zaiyi magana sameer ya maka masa harara hakanne yasa shi yin shiru be tanka mata ba, har takai bakin qofar kitchen din sai ta tuna da mari jiyowa tayi taga har yanzu ashe tana gurin takasa tashi daga gurin kiran ta tayi tace mari wai wai har yanzu baki tashiba ki tashi daga nan ba abun da zai miki miqewa tayi jiki babu kwari har ta nufi qofar dakin ta sai kuma ta tuna da aljanar dazu sa sauri tayo baya Ammah da bata qarasa shiga kitchen din ba ta juyo tace ke lafiyar ki qalau kuwa meye hakan kikeyi sunkuyar da kai tayi tace Allah taimakike Allah ya qaraja da ranki yake uwar dakina Allah......dakatar da ita tayi tace fadi maganar ki kai tsaye qara sada kanta qasa tayi tace daman abun da zan gaya miki wannan yarinyar da tazo wacce take dakin ashe ba mutum bace aljana ce da sauri Ammah tadawo kusa da ita tace aljana kuma kamar ya bangane ba nufin ki ta gudu taya ma kikasan aljanace inkawo mutum kiringa cemin aljana cikin rawar murya tace wlh aljana ce ni na ganta da idona bayan nagantane na gudo shiyasa har nayi karo dashi ban kula ba gaban Amma na faduwa tace amma bata nuna ba tace yanzu hakan tana cikin dakin tace mata eh tana ciki juyowa tayi tana kallon su papa da suma sunzuba ido suna jin abun da suke cewa Ammah tace kai kunji me tace wai aljana a cikin gidan papa ya mike ts aye yace kamar ya aljana taya akai ta shigo kuma hartabari aka ganta daman aljanun haka suke Ammah ce tace yarinyar fa danake baka labari dazu wai itace aljanar gaba dayan su suka miqe tsaye papa yace to muje mugani ko watakilma shirmeni irin nata me sunan baba muje gaba dayansu tsayawa sukayi sukaqi tafiya saida yasake yi musu magana sannan sameer yadan shafa kansa yace papa aljana fa akace kuma sai kace muje idan tayi mana wani abun fa nide bazan jeba kuje ku gano papa baki yasaki yace tofa kai yanzu qato dakai kace wai tsoro kake ji ko kunya baka jiba to kaifa ko kaima tsoron kake ji yafada yana kallon shettima shimade ba kunya yace eh papa aljani ai ba abun wasa bane dade mutum akace to koma waye zamu iya dashi amma banda mutan boye papa kawai yanzu yanda za ayi mufita daga gidan gaba daya sai aje akirawo malami sai yazo ya duba yagani papa da mamaki yagama kashewa yace amma de kunban kunya wlh nibansan haka kukeba ashe duk matsorata na tara to wlh ba malamin da za akira kuma sai kunje idan aljanar ce inma wani abun zatayi muku ai da tun shigowarku zata yi muku kuwuce muta yafada yana turasa Ammah ma qarasowa tayi tace a'a bekamata kayi musu dole ba kabari kawai ayi yanda sukace aje akirawo malami hakan sai yafi duban ta papa yayi yace kinsan Allah na rantse kuma wlh sai munje kuma hardake dan haka kuwuce muje duk son bijerewar su amma papa yaqi ya dage akan sai sunje ba yansa suka iya haka sukayi hakuri suka tafi yasaka su agaba sai da sukaje daf da dakin sai kuma suka fara dawowa baya wannan yace wani yayi gaba wannan yace wani yayi gaba Ammah tace kunga kune maza kuyi gaba ni sai in zauna abaya shettima yace ai wlh kece agaba kinga ke kin tsufa daman kinkisa mutuwa mukuma kinga yanzu muke tasowa kinriga kin gama cin zamanin ki muma kibar muci namu tsohuwa kawai kiyi gaba yafada yana turata gaba dalla kadena turani daman angaya maka ita mutuwa zaba take duk da na tsufa sai kaga kai ka mutu kabarni yace eh na yarda amma de ai bata wannan hanyar ba da zamu mutu lokacin mu beyi ba papa ne yadaka musu tsawa yace banason shirme anan kuwuce yafada yana bude qofar dakin amma baigama budewa gaba daya ba sai yatsaya yace suzo su shige aikam kowa yaja burki daga inda yake shima kuma be shiga ba ashe shima aranshi yana danjin tsoron kawai dakewa yayi ganin sun tsaya yaqara yi musu magana wai baza ku wuce ba dan matsowa suka farayi ahankali Ammah ce agaba da shettima ya turota sai sai shi shima kuma sameer ne ya turosa sannan ya tsaya abayan su yana jiran yaga sungama shiga idan lafiya lau sai ya shiga idan kuma yaga sun dawo sai yajuya daga inda yake, Azeema dake dakin tana zaune take jin murya sama sama kamar aqofar dakin yasata tashi tayo wajen qofar dataji anturo tasa hannu taqara budewa tana budewa sukayi ido hudu da papa,papa naganin ta yaja baya da sauri amma be bar wajen ba ya tsaya itama Amma sai ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda tagane yarinyar ce dai kawai kwaliya tayi ta lalata fuskarta tun ganin da sukayi papa yadan ja da baya ai basu tsayabama bare susan me za ace har sunjuya sun nufi hanyar waje aguje har suna 'yar rige rige wajen bude qofar qofa kuwa kamar tasan halin da suke ciki sai taki buduwa tsayawa sukayi suna kokarin janta Ammah da ta juya bayan ta zatace su kwan tar da hankalin su sai taga wayam babu kowa awajen maida dubanta tayi ga Azeema tace fito waje kinga ki tsorata min 'ya'ya wannan wace irin kwalliyace kikayi jin hakan yasa papa ajiyar zuciya danshima yafara tunanin ko aljanar ce dan shi betaba ganin anyi kwaliya irin wannan ba matsawa yayi yace nima ai ta kusan tsoratani ina wadannan
Chapter 15 · 0% Book details