← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 139

Sashe 50

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

unguwar da suka kaisa nan suka nufa adan ƙanƙanan lokaci suka ƙarasa gidan da suka ajiye sa yanzuma bossay ne ya fito yaje ya bude musu gate din sukuma suka shiga ciki bayan yagama yin parking duk suka fito,
sameer ne ya bude bayan motar inda take kwance har yanzu bata farfaɗo ba ɗagowa yayi sai kawai suka hada ido da shettima dariya shettima yayi masa dan yagane abun da yake shirin yi,
dan ƙaramin tsaki sameer yaja tare da kawai da idonsa daga kansa amma yayi tsaye yakasa taɓuka komai kuma bayaso wani yadauke ta acikin su shikuma bayaso ya dauketa suyi tunanin wani abun shiyasa yakasa tabata,
ahaka bossay da yagama rufe gate yaƙaraso wajen yasamesu,
shima tsayawa yayi ya kalli wannan ya kalli wancen ganin duk sunyi carko carko kamar nonuwan maza,
   shettima ne yadanyi gyaran murya sannan ya kalli bossay yayi masa alama da ido akan sutafi, gaba sukayi suka barsa awajen,
binsu yayi da kallo yama rasa me zaiyi har suka shiga cikin gidan bai motsaba daga inda yake ba,
ganin tsayiwar baza takai shiba ya tsugunna ya shiga cikin motar yana ta wani taɓe fuska da yatsinata sai yasaka hannu zai taɓata sai kuma yafasa yajanye hannun sa yayi hakan wajen sau biyar amma yakasa tabata daga ƙarshema sai kawai ya fito daga cikin motar yana ƙara binta da kallo,
ajiyar zuciya yasauke tare da furzar da iska me huci daga bakin sa tare da cije lip dinsa na ƙasa yana dan jijjaga kai,
wata zuciyar ce tace masa wai meye hakan kake yi kashiga kawai kadauko kana ƙara ɓatawa kanka loƙaci wai sai kace kai bana miji ba wannan yarinyar zaka zauna kana wani jin shakkar tabata,
  cike da dakewa yakoma cikin motar gadan gadan zai tabata sai kuma yafasa rintse idon sa yayi tare da dukan kansa yaƙara jan wani tsakin,
da ƙyar ya runtse idon sa ya daure ya cize yasa hannun sa akanta bayan ya dora hannun nasama akanta kasa ɗagota yayi sai da yaja lokaci sannan ya ciccibofa ya fito da ita tare da ɗorata akan kafaɗarsa yadafe ta da hannu daya dayan hannun kuma ya rufe ƙofar da ita sannan yafara tafiya da ita aransa yake ayyana bata da nauyi juyayi kamar ba abun da yadauka haka yakeji saboda rashin nauyin ta,
    ahaka yana zancen zuci yaƙarasa bakin ƙofara sannan ya tura ya shiga ciki yana shiga yayi karo dasu abakin ƙofa ashe duk abun da yake suna leken sa suna masa dariya da suka ga yakusa shigowa ne yasa su matsawa daga jikin ƙofar,

tunda ya shigo suke binsa da kallo suna so yakalle su amma shikuma yaƙi yarda su hada ido ɗin,

ganin zai sauketa yasa shettima saurin cewa dan Allah dan tsaya inyi muku hoto wallahi kaga kyaun da kukayi banza yayi masa saidai kafin yakaita ga kwantarwar har shettima yadauke su a hoto loƙacin da yakai ga dan durƙusawa zai kwantar da ita yaƙara yimusu wani aƙallade saida yayi musu wajen guda biyar kafin ya ajiyeta,

bayan ya kwantar da ita yajuyo yana kallon sa wayar yazo zai kwace shettima yayi saurin janyewa tare da mayar da ita aljihu yana yimasa dariya,
hade rai ya kuma yi sannan yace wai ku dan Allah me yake damunku yanzu loƙacin wasane bakusan abun da ya dace ba da wanda baidace ba kunzo sai faman shirme kuke to wallahi last warning kufita daga idona be for I losing my temper wallahi bazakuji da dadi ba yafada yana nunasu da yatsa alamar gargaɗi,

    "Shettima na yar dariya ciki ciki ya ƙame kamar soja yayi salute dinshi tare da cewa  sorry sir bazamu ƙaraba,

ciki ciki yace mutum sai shegen son girman tsiya duk de hade ranka bazan gogeba wannan hoton sai yaje har gaban Ammah,

me kace cewar Sameer yana kallon sa ,
tabe baki Shettima yayi sannan yace mekwa nace ni ba magana nayi ba,
jijjiga kai yayi kawai yana girgiza kai sannan yayi gaba batare da yaqara tanka musu ba shiga dakin da suka ƙulle mahaifinta tura ƙoafar yayi da ƙarfi, yana shiga yaganshi a tsaye yana faman rarraba ido naushi yakai masa abakin sa atake bakin ya kuma fashewa, ya ɗago kenan zaiyi magana ya qara kai masa wani sosai ya shiga dukansa kamar an aikosa kuma yaƙi bari yayi magana shima kuma ko A baice masa ba sai duka kawai,
su Shettima ne suka shigo cikin dakin ganin yana niyar kaisa lahira,
yasa su saurin dakatar dashi suka shiga tsakanin su,
tsugunnawa yayi agurin tare da dafe kansa hakannan yaji yana mugun jin haushin shi da yagansa maganganun wancen mutumin ne suka shiga dawo masa cikin kwanyar kansa sosai yake jin zafi da ƙuna a zuciyar sa,
mahaifin sumy kam yana gefe a yashe yajigata kana ganin sa kasan ya daku ba ƙarya, dan numfashin sa har daukewa yake yi idon sama duk sunyi ciki ciki baya ganin su sosai yajigata ko motsi yakasa yi,
"sameer tashi yayi daga tsugunen da yake ya ƙarasa gaban shi tare da durƙusa gabansa yana kallon ɗago fuskar sa yayi da kyau yanda zaifi ganin sa cikin amon murya yace zaka fadi inda yake ko sai na karar da numfashin ka agurin nan waye shi kagaya min yafada cikin tsawa da daga murya kafada nace waye shi?
"shiru ba amsa jin yaƙi basa amsa yasa yaƙara daga hannun zai kai masa duka yaji an riƙi masa hannun,
bin hannsa yayi da kallo har zuwa kan nata hannun ahankali ya shiga bin hannun nata da kallo har yazo kan fuskarta hawaye yagani a fuskar ta, saurin kawar da kansa yayi tare da kwace hannun sa,yana maida shi kan mahaifin nata zai dake shi tayi saurin shiga gaban mahaifin nata ji kake tass akan fuskarta dafe kunci ta tayi tana wani sakin marayen kuka cikin kuka tace kadake ni kaci gaba da dukana mai mukayi maku nida mahaifina daman sato ni kayi shine zaka yaudarene maiyasa zakayi mana haka mai wane irin zunubi muka aikata maka da muka cancan ci wannan hukuncin daga gareka kallifa yanda ka maida mahaifina kuma hakan bai ishe kaba kake shirin ƙara masa wani,
kai wane irin marar imani ne baka da tausayi me ya aikata maka takarasa maganar cikin daga murya tana share hawayen da suke rige rigen zubowa,

cak ya tsaya yakasa motsawa saida tagama maganar tata sannan yasa hannun sa yajanyeta gefe taga taga tayi zata fadi yayi saurin tarato da hannu daya saida tagama daidaita sannan ya sake ta,

ƙara riƙo mahaifin nata yayi sannan yace idan kana son ranka da na ƴarka kafada min kai bama ita kadai ba har matar ka da mahaifiyar ka duk nasan inda suke dan haka kazaɓa rayukan ku ko wancen azzalumin da kake karewa,
ƙara matsowa tayi kusa dashi tace maizai fada maka? "banza yayi da ita baikalli inda take ba yaci gaba da tambayar sa amma yaƙi magana,
shake wuyan sa yayi da kyau yanda zaiji ƙanshin rahila,
cikin kuka ta riƙe hannun sa tana jansa amma ko gezau takasa juyawa tayi tana kallon su Shettima da sunyi tsaye suna kallon su sun kasa saka hannu kuma sun kasa cewa komai,
dan Allah kuzo kuriƙeshi kar yakashe min mahaifi wallahi idan yakasheshi duk sai na shigar daku ƙara tunda kuma baku da imani kuma ganin za ayi kisan kai amma babu wanda yayi yunkurin hanawa, komawa tayi kansa taci gaba da jan hannun sa tana dukan sa tana kai masa cizo amma yaƙi saki daga ƙarshe ma sai yasa dayan hannun sa ya riƙe mata duka hannuwa biyun,
da ƙarfi tace abbaaaa kafada musu abun da suke buƙata zasu kashe ka dan Allah kafada musu Abba kafada musu na roƙeka tafaɗa tana ƙara sakin wani kukan muryarta har tafara dashewa saboda tsabar kuka,

kukan da take ni ya dami sameer yasa shi sakin mahaifin nata,
yana sakinshi yafara tarin wahala harda amai ga jini da yagama bata masa fuska duk yayi gaja gaja dashi kuma yakasa magana duk da zuwa yanzu ya fara saduda musamman ma da yaga ƴarsa ahannun su,
zaka fada din ko incigaba? cewar Sameer,
cikin kasalalliyar murya da kyar ya iya bude baki yace
yana ABUJA................✍️✍️
[6/4, 1:34 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

               💖NEW TEAM💖
   💖*the talent troupe writer's*💖

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*

                        🅿️47&48

✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨

✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨

Bismilah............✍️

   cikin kasalalliyar murya da kyar ya iya bude baki yace yana ABUJA....

         Abuja a ina?
Shettima da yazo wajen ya tambaya,
   "cikin mawuyacin halin yaƙara cewa nima bansani ba nade san kawai a abuja yake saidai kuje kunemo shi nikuma kusake ni in koma wajen iyalina,

   "idan kaga munsakeka to yazo hannun mu cewar Sameer yana wani binsa da kallon tsana,

mahaifin sumy yace nifa bansan komai ba akan case ɗinku meyasa kuma zakace baza kusakeni ba bana gaya muku abun da kuke buƙata ba kuma me ƴata tayi muku bani nayi muku laifi ba meyasa zaku saka ta aciki yaƙarasa maganar cikin sanyin murya,
Chapter 50 · 0% Book details