← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 139

Sashe 80

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ina shiga ina zan zauna ko akansu kake so in zauna Ammar ne yayi saurin buɗe ɗayan barin ya fito sanaan yace ta shiga bari shi yaƙarasa ciki aƙafa shiga tayi ta zauna tana ta faman cika tana batsewa tunda ta shiga take makawa bossay harara Sarai yaganta amma sai yanuna baima san tanayi ba yanzu Sameer ne yajasu zuwa cikin masarautar zuciyarsa cike da tarin damuwa yanzu kuma ina zaikaita da yaɗauketa wata zuciyar ce kawai tace kugaya mata gaskiyar abun dake faruwa wata zuciyar kuma tayi saurin kwaɓar sa akan karya kuskura Yahaya mata idan kwa tasani abun nata sai yafi haka dan haka gwara ma yakaita wajen momma ta riƙe mata ita ahanata fitowa sukuma sai su fito suci gaba da aikin su da wannan shawarar ta zuciyarsa ya samu kwarin gwiwar ƙarasawa cikin gidan...

_______hamza

Yaron nan wai me yake damun ka a yan kwanakin nan duk kabi kazama wani iri baba ne yakewa hamza magana dake kwance kan yayi ruf da ciki kamar me bacci,

dagowa yayi tare da tashi zaune yana fuskantar baba sannan yace baba ciwon sone yake damuna kataimaka kaje kayo min bikon yarinyar nan wallahi ta shiga raina ta zauna amma duk sanda zamu hadu duk maganar da zan mata bata kula ni narasa ya zanyi da ita amma gaskiya ina sonta baba yazanyi da sonta,

baba ne yayi dariya irin tasu ta manya sannan yace hamza kenan bakajin magana yanzu duk iya tsarin naka da dauriya irin taka amma kake son mace ta canzaka ai bai kamata kana jin shakkarta ba kawai kaje gadan gadan kasame ta ka gaya mata abun dake ranka idan taga zata amince dakai to idan kuma bata amince ba sai ka hakura ai ba awa mutum dole akan soyayya,

baba wallahi masifaffiya ce kuma ina ganin kamar tainani tayi shiyasa taki kulani saboda na lura kamar ba baiwa bace saboda jikin ta bai nuna wata wahala ba ranar fa dana fara shan gabanta zan mata magana saura kiris ta kwashe ni da mari nayi saurin matsawa amma badan hakaba sai ta mareni saboda na tari gabanta kawai sannan ta gargadeni akan ko a hanya naganta kar nasake na kara yimata magana amma ni bana ji sonta ya rufe min ido duk sanda naganta sai na kuma yi mata magana baba wallahi kai kadai zaka iya taimakamin,

dariya baba yayi sosai dan har hakuran sa saida suka fito cikin yar dariyar yace ni kuma dame zan iya taimaka maka da girmana ina ni ina yiwa yarinya magana akan soyayya wanna yakin kai kadai zakayi shi ba ruwana aciki,

to wallahi baba indai baza ka taimakamin ba zansan yanda nayi na sace yarinyar nan in boye ta inta kallon ta ina yimata abubuwan da dole sai ta soni,

"Au daman anayiwa mutum dole akan so taya zaka ta soka bayan ka saceta to wai ta inama zaka saceta kuma ka kaita ina idan kasace ta din?

"kai baka jin tsoron akamaka wane irin hukun ci za ayi maka idan ka aikata hakan,

Baba tsorofa kace ai wallahi cikin gidan nan babu wanda ya isa yasa inji tsoron sa kaf cikin gidan nan baba nifa ko fita nayi niya babu wanda ya isa ya hanani kawaide saboda inma nafita bansan inda zani ba kuma anan din ina samun yanda nake so amma bana zaman gidan nan saboda wani dan haka ka ajiye maganar tsoro ma agefe ni hamza bana tsoro saidai inbada tsoro,

"eh baka jin tsoron mutane amma ai ga mace nan zata saka ka agaba tunda hartayi yunkurin marin ka ka kasa komai kaga kwa ai kasamu wanda kakejin tsoro din,

Dan shafa kansa yayi sannan yace baba itama ai dan ina sonta ne shiyasa na daga mata kafa amma badan haka ba kaikasan bata isa ta mareni ba ko niyar da tayi ma sai na koya mata hankali amma dake sonta nake nakasa yi mata komai kuma ahaka naci gaba da son nata,

yana gama maganar ya kara gyara zama sannan yace baba nifa taimako daya zaka min muje tare kawai sai kace mata kai mahaifinane kana neman min auren ta tayi maka magana da manyan ta nasan de kai babbane baza tayi maka abun da take yi min ba,

daga nan nikuma nasamu dama sai in kuma tsarata har ta amince dani ka yarda baba,

baba yace nidai ba inda zani da girmana kasa yarinya ta dena ganin mutun cina idan wani abun ya hada tunda tace bata sonka to bata sonka din ka hakura da ita kawai,

"Wllahi baba bazan iya hakura da ita ba kawai kayi hakuri muje tare ni inaji ajikina idan mukaje tare Allah zata amin ce idan taga da gaske nake de sonta nake kuma auren ta sai tafi yarda dani,

  "nifa ba inda zani kaje can kai kaɗai amma babu ruwana,

baba wai yanzu haka zamuyi dakai tunda muke bantaɓa neman wata alfarma ba awajen ka amma yau ɗaya na nema amma kaƙi amincewa shikenan baba nagode,

yana gama faɗar haka ya tashi yana niyar fita, yazata baba zai dakatar dashi amma yaga har yakai bakin ƙofa baba baice komai ba,

sai kawai yadawo yashi ga yin murmushi tare da tsugunna wa agaban babba yafara roƙon sa akan dan Allah ya taimaka suje tare baba kuma yaƙi amincewa de da haka baiyi ƙasa agwiwa ba yaci gaba da lallaɓa baba da haka har yasamu yayi nasara baba yace zaije ammade shi bazaije can ɓangaren wajen Fulani ba saidai yasan duk yanda zaiyi idan yarinyar ta fito sai su haɗu amma shide bazaije can ba wannan matar ta gansa tasaka aci mutuncin sa shiyasa duk wani abu idan zaiyi yake taka tsantsan baya yarda su haɗa hanya da ita indai ba dole ba wani abun ya haɗasu ba shima bada son ransa ba shiyasa yanzuma yace bazai je can ba saidai ita yarinyar idan tafito sai su haɗu,

Sosai hamza yayi murna da hakan ma yace ni baba ai indai zakayi mata magana to koma tayayane zakaganta yanzude bari in shirya sai mufita tare inyaso sai ka tsaya daga ɗan baya ni kuma zanje har inda take in taho da ita ko agaban wa take,

Allah ya shirye ka nidai na matsu inji abun da yasa ka raina matar nan baka jin tsoron ta kwata kwata abun naka har mamaki yake ban wallahi gashi kullum abun naka gaba yake ba ya raguwa baka shakkar ta ko kaɗan,

  "Hhhhh baba kenan kabari very soon zakaji komai ka kwantar da hankalin ka so nake ta kaini ƙarshe inci mutun cinta agaba kowa wallahi nifa ahakan ma ni nake haƙuri da abun da take min nake daga mata ƙafa amma akwai ranar da zan danneta tagane bata da wayo,

"to Allah ya kyauta ni ai yanzu kafi ƙafina Hamza saidai kawai inci gaba da yi maka addu'a Allah ya shiryeka sannan kuma inci gaba da zuba ido inga ƙarshen wannan cika bakin naka,

"Wallahi baba ba cika baki bane amma de shikenan kawai abar kaza cikin gashinta abar wannan maganar bari inji insake wanka saboda gudun raini kaima kuma baba sai canza kaya dan baza muje dakai ahaka ba,

Kade san idan aka ganni da wasu kayan ba kayan aiki ba kuma ina yawo akwai matsala dan haka kabarni inke ahaka ni bana ƙarya kaide da kake da ƴancin canzawa sai kai ta canzawa amma nidai kabarni haka sai nafi jin daɗin fitar ma inkuma baka yarda shikenan sai inyi kwanciyata ince adawo lafiya,

"A'a baza ayi haka bama shikenan muje ahaka ɗin nidai kam sai na canza yana gama faɗar haka yashige cikin bandakin,

bai jima ba ya fito jakar kayan sa ya ɗauko yazaro wani yadi fari tass me laushi daga gani ma me tsadane ya ɗauko ya saka aka dauko hula itama aka saka yafito dos dashi kamar sabon ango,

Shidai baba yana zaune ya zubawa sarautar Allah ido duk inda yayi sai yabisa da kallo har yagama shirya wa yaɗauko turare ya feshe jikin sa dashi take ɗakin ya kauraye da ƙamshi,

saida yagama shirya wa tsaf sannan ya kalli baba "yace baba ya kaganni zan burgeta idan taganni,

"Ah ba dole ba irin wannan kyau haka a ina kasamu kayan nan nidai tunda muke bantaɓa ganinsa ba,

wata ƙayatacciyar dariya hamza yasake sannan yace lalle baba kana wasa dani iya haɗuwata da ita nasa aka ɗin ko min su baka gansuba sababbi ai yanzu nafara ɗinkuna agidan nan tunda na haɗu da ita kuma ai magana ta ƙare yanzude duk ba wannan ba baba kar kwalliya ta 5a fara samun mushkila taso mutafi,

shide baba yau yana ganin abun mamaki da farko in akace masa Hamza zai iya yin irin waɗannan abubuwan bazai yarda sai gashi yanzu nema yake yafi ƙarfin tunanin sa,

Miƙewa yayi yana riƙe baki ganin irin takun da hamza yake yana dariya suka fito daga ɗakin atare suka nufi hanyar can cikin masarauta saboda tsakanin su da ɓangaren masu gida da tazara dan haka dole sai baba yaƙara gaba sosai kafin yasamu inda zai tsaya ya jirasu,

________Azeema

tana zaune gaban Fulani tana yi mata tausa zuwa yanzu tasaba da gidan amma akullum cikin kyalla ido take ko zata ga mahaifin ta amma shiru bata taɓa haɗuwa dashi ba dan hartafara fidda rai da ganin sa kuma yanzu ba koda yaushe take samun loƙacin kantaba ko da yaushe suna tare da fulani tana yi mata bauta wataran ma idan papa baya ɗakin kusan kwanan zaune take wajen yi mata bauta itace ɗauko wannan ɗauko wancen share nan goge nan duk wani aiki ya dawo gurin ta girkine kawai ba abarta tayi ba saboda ba ayarda da ita ba sosai baza a iya bata girki ba saboda tsaro,
Chapter 80 · 0% Book details