← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 139

Sashe 2

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan na dan kwana biyu sai nayi tunanin gwara inbar gidan saboda zuwa lokacin nadena yarda da kowa tunda ko basu fadan ba dukkan alamu sun nuna yar sandar nan da tace intaho kano itace tagaya musu inda nake alhalin kuma itace tace intafi amma kuma daga baya ta ci amanata shiyasa nake ganin duk inda ma naje duk bakin su daya ba wanda zai taimakeni saboda Allah,
bayan barina gidan bansan inda zan dosa ba sai kawai na nufi kasuwa sai na tambaya inda sabon prison din yake sai aka kwatan ta min amma da naje sai akace ba wanda aka kawo haka naqara dawowa jiki babu kwari har zuwa dare bansamu mafita ba ina tavgarari a bakin hanya aranar de a wani harabar masallaci muka kwana ina ta barci har mai ma sallacin yashigo bansani ba saida yatashi ni yace baiwar Allah lafiya kuwa kika kwanta anan adan takaice de nabashi labarin nace masa wasune suke bina zasu kasheni gashi sunkashe min mijina shiyasa na gudo nazo nan na kwanta kaji dalilin kwanan nawa agun shine ya taimaka min ya nuna gidan sa yace inje idan an idar da sallah zai shigo incewa mutanen gidan shi ya aikoni dana shiga ba kowa haka naita yin sallama amma ba wanda ya amsa sai kawai nasamu waje daga gefe na tsaya ina jiran shigowar sa ina gurin ba wanda ya fito har aka idar da sallar ya shigo yaganni awajen ya metasa na tsaya nace nayi sallama ba amsa ba yace to shikenan muje ciko yana tafiya ina binshi abaya muka shiga wani daki wata mata na salla saida ta idar sannan yace uwani ga bakuwa tazo tana ta sallama baku amsaba tace bakuwa kuma da asuba daga ina nande shima yayi mata bayani amma fuskarta ba walwala tace to barkan ta da zuwa ga guri ta zauna ta nuna bakin gado sai mutumin yace baiwar Allah ki ajiye yar sai kiyi salla kafin da gari ya qarasa wayewa ko nace masa to sannan na ajiye yarinyar ya nuna min inda bandaki yake naje yi alwala na fito bayan nayi idar na gaisar da matar amma sai naji ta masa min ciki ciki tunda ga nan nagane cewa matar bata son zamana dan haka nayi alkawarin gari nayin haske zanbar gidan zama nayi adakin saboda zuwa lokacin mutumin har ya fita daga dakin ina gurin har gari yayi haske ina shirin  fita kenan saigashi ya shigo dakin ganina a tsaye yace ina zani nace masa zan tafi ne yaca a'a ba inda zani idan na tafi ina zani bayan ba wanda nasani nace masa yayi hakuri yabarni intafi yace a'a saboda banason mitayin jayayya sai kawai nace masa to zan zauna zuwa gobe kafin insan yanda zanyi yace to haka na koma na zauna shiru kamar ni kadaice adakin danko inda nake ma matar bata sake kallaba kamar ma batasan da zamana acikin dakin ba,
inda nayi sallah na kwanta agun dan bacci nake ji wanda nayi be ishe niba ina kwanciya kuwa bacci yadauke ni,
kukan Ameesha ne yatasheni ina tashi naga tana tafaman kuka amma matar nan tana kallon ta bata dauke ta ba kuma bata tasheni ba haka natashi nadauke ta na rarrasheta nabata madara tasha saidaga baya na lura da kwanon abinci agefena saida nagama bata sannan nasamu tayi shiru nikuma daman yunwa nake ji dan haka kawai nahau cin abincin da nagama kawai sai ban kulata ba  nafitowata mutanen da nagani na shiga gaisarwa duk suka amsa amma suma mata daya ce naga fuskarta a sake dayar kuma ko amsawa ma batayi ba dayace tazo kusa dani ta karbi Ameesha dake hannu na tace kintashi ai malam yace muzo mu gaisa sai muka tarar kina bacci sai lokacin na danji dadi danaga ita ba irinsu bace dan haka kawai nima nasake da ita muka dan yi hira na lurama kamar adakinta yake ita take aikin dan haka na taya ta adan kan qanen lokaci muka saba da ita sauran kuma ba waccce na qara bi takanta tunda sun nuna basa sona nima sai nafita daga harkarsu sai da muka gama komai sai nace mata dan Allah taimako nake nema inason inkama gida dan madaidai ci ba me tsada ba sai inzauna tace bazan zauna anan ba nace mata eh nafison in zauna nikadai zama agidan wasu be kamace niba da girmana tace to shikenan bari zatayiwa malam magana idan yadawo sai aduba nace to shikenan shiru de inajira inga yadawo amma be dawoba sai dare yana dawowa kuwa tayi masa magana yace zaiyiwa wani abokin sa magana da yake harkar gidaje amma sai zuwa gobe anan muka bar maganar zuwa goben,

Washe gari ma yace yama sa ana cigiya amma kamar na nawa nake so sai nace masa me sauke de yace kamar na dubu talatin ko ashirin ya isa tunda ni kadai ce nace masa eh ya isa ni koma bekai haka ba inaso duk tsufansa kuma dan nama fison tsohon gida me sauki sosai ko daki dayane ya isheni yace to ba matsala za asamu intakaice mukude saida mukai wajen wata ba asamu gida ba saida kyar akasamu shima ance sai andan yi masa gyara kuma ba anan bane awata unguwar ne nace ba matsala yanzu zuwa yaushe za agyara din yace inbada kamar nan da sati daya nace to alokacin nahada kudin da na ciro a pos da kuma wanda Ammi tabani nabashi dubu a shirin da biyar yakarba yaje yakai musu akallade sada nayi wajen wata daya da sati biyu sannan na tarkata yan kayan da na siya mana nabar musu gida dan banajin dadin zaman gidan kwata kwata agurin mutum daya nake samun sauqi duk tsawon lokacin da muka dauka dasu bawanda nasamu sauyi daga garesa kuma  hatta yaran gidan basu da kunya ba wanda yake girmamani ita kuma wacce muke mutuncin da ita bata da da ko daya shiyasa na matsu inbar gida,
mu uku muka nufi unguwar dani da limamin da kuma abokinsa wanda zai kaimu gidan ranar da muka bar gidan tunkan mukarasa unguwar aka kira limamin awaya daya daga cikin matansa ce ta kira shi wai yadawo tare dani wasu mutane sunzo nemana ko mudawo ko mufadi inda muke duk ina jinsu sai nace masa yakashe wayar kawai karyace komai sai ya kashe wayar sai yatambayeni ya za ayi dayan abokin nashine da shima yasan komai sai yace kawai ai mafita dayace shine liman ya koma yace musu ya riga yakawoni gidan da yakama min inyaso sai ya kwatan ta masu gidan sai yace nikuma yanzu mutafi gidan sa kafin yasamo min wani gidan daban yanda bazasu iya sanin inda nake ba munji dadin shawarar sa dan haka muka yarda tun alokacin muka saukeshi ya juya mukuma muka nufi gidan wannan abokin nasa inda yake unguwar kurna banyan mun isa sai naga banbanci da wadan can mutanen gidan liman nan gidan mace daya ce sai 'yayan su mace da namiji suma duk yarane namijin nema me wayo amma macen bata da wayo hannu bibbiyu matar ta karbe ni ko jin wacece nima bata tsaya tambayar mijin nata ba kawai yace mata ga bakiwa nan kafin asamo mata gidan haya zata zauna anan saboda bata san kowa ba anan tace to ba komai ai sai muzauna sosai take kula dani duk danasan tama girmeni ko bada yawa ba amma yanda take kula dani tana bani girma kamar nice gaba da ita haka muka zauna da ita yatanta ma sai faman daukar Ameesha suke naji dadin zaman gidan sosai cikin kwanciyar hankali harnayi kwana biyu,
bayan kwana uku aka samomin gida bamu da nisa da su badan taso ba muka bar gidan dan yaranta harda kuka macen ma cewa tayi sai ta bimu da kyar de suka bari muka tafi kudi naqara cirowa nasiyi duk wani abun amfani da nasan zan bukata da kayan sakawa da na daki komai de babu abun da bansiya ba dan zuwa lokacin ma kudin da na rage basu fi dubu goma ba dasu bayan 'yan kwanaki kuma sai nafara saro kaya inakaiwa wata makaran ta ina siyarwa saboda banason inzo in kashe kudin gaba daya shiya sa nafara juyasu ta hanyar kayayyakin yara haka naci gaba da rayuwata nikadai sai Ameesha amma wataran ina kaita gidan mutumin nan wajen 'yayan sa wataran kuma akawosu harma suka fara zuwa da kansu shakuwa ta shiga tsakanin su me qarfi har Ameesha tayi wayo sosai ta girma tama fara magana da tafiya ga tsiwa da take da ita lokacin da tayi shekara biyar sai nasakata makarantar su Azeema inda shakuwa taqara shiga tsakanin su duk inda kaga daya sai kaga dayar har takama ma wataran gida daya suke kwana ga halayen su yazo daya basaji a makaran kullum cikin kai qararsu kaf makarantar ba wanda besan Azeema da Ameesha ba kamar ya da kanwa wadanda suka fito ciki daya haka suke.................✍

*to anan nakawo qarshen Free Page na sarki sameer book 2 duk wanda yake son ya cigaba da karantawa yabiya ya karanta cikin kwanciyar hankali da salama 👌👌*
[4/26, 8:13 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤

💅SARKI SAMEER...💅
             (wasa farin girki)

                 *Book 2*

    *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526,
Chapter 2 · 0% Book details