← Book details Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 139

Sashe 25

Sarki Sameer Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Miqewa yayi jiki babu kwari sum sum sum kamar wani munafiki haka ya tashi ya fice daga falon da tunanin ganin wannan lamarin da yabasa mamaki  ganin yanada matar sata shiga tashin hankali abun da baitaba gani ba kenan yasan tsayayyiyar macece ita baka taba gani alamun tsoro atattare da ita kuma bata karaya awajen magana amma yau wandata raina tayi jika dashi ma yazo ya gaya mata maganar da har damuwa ta bayyana a fuskarta  qarara takasa boye shi kuma bata tanka wa sam ba har yagama ya fice yabata waje amma kuma yanzu zatazo ta sauke akansa amma bari yasa aje akira masa sam yatambaye shi shin abunda yake fada gaskiya ne ko kuma qarya yake dan ya tura mata haushine kawai yasa shi yi mata hakan da tunani ka fal cikinsa har yaqara sa part din Ammah tunda daman adakin ta ya kwana yazone su gaisa da fulani sai kuma wannan abun yafaru aka rabu bata dadin raiba yana qarasawa yatarar Ammahn bata falo sai kawai yayi zamansa akankujera yana qara tunano magan ganun sam da shi kwata kwata yakasa gane inda suka dosabe dadeda zaman ba sai ga Ammah ta fito fuskarta dauke da murmushi ta qarasota zaunakusa dashi tace har kadawo kenan da wuri haka yace eh wlh dakegurin maryama nafara shiga daga nan kuma nayo nan kallonsa ta danyi sannan tace a'a to bakaje fada ba kenan yace eh fasawa nayi zanje anjima tace to shikenan Allah yakaimu jimawar yace Ameen yauwa dan kiramin me sunan baba awayarki naga har ya fita dan bansameshi a part din may arm a ba naga harya fita kitashi inji yatafi wajen aikine ko kuma yana cikin nan baikai ga fita ba tunkan yagama rufe baki ta amsa masa da to sannan ta dauki wayar tana cewa nima daman ina neman sa bari in kirasa taqarasa maganar tare da dannawa number sa kira bugu biyu ya daga yanadagawa ua gaida ita bayan ta amsa take sanar dashi cewa yazo papa nakiran sa ok kawai yace daga nan suka katse wayar ta maida duban ta ga papa tace yace gashinan zuwa yace to daga nan suka ci gaba da hirar su ko kadan be bata labarin abun da yafaru ba kawai wata hirar suka cigaba dayi...

*FULANI*

bayan fitar papa hannu ta dora akai tashiga rarraba idanu cike da tashin hankali da bata taba tsintar kanta aciki ba a fili tafara cewa na shiga uku me yaron nan yake nufi da duk wani takuna ana gaya masa waye munafikin da yake akusa dani yazama dole incanza taku agidan nan to taya ma akayi nayi sake har wannan dan qaramin alhakin yasan me nake aikatawa acikin gidan nan kalamansa ba qaramin tayar mata da hankali yayi ba dan rabon da tashiga irin wannan tashin hankalin har ta manta shiru tayi nadan lokaci sai kuma can tayi zunbur ta miqe tsaye tafara zagayawa a falon tare da saka hannuwan ta duka abaya tana zagaye tayi can tayi nan abun duniya duk yabi ya isheta tama rasa tunanin da zatayi kamar wannan yaron har yakai girman da zai zo yana gaya mata magana son ransa lalle dole tayi maganin sa inyasan wata ai besan wata ba sai ta nuna mishi shidan qaramin kwaro sai ta juyar masa da tunanin sa yanda baya zato sai ta koya masa hankali fiye da tunanin sa sai ta gasa masa aya atafin hannun sa haka tai ta faman surutai ita kadai da ayyana abubuwa iri iri da zatayiwa sam kala kala daga yau zai gane shayi ruwa ne daqarfi tace qarya kake wallahi nafi qarfinka kai ka isa kasani shiga damuwa yaushe kazo duniya to wallahi qaryane koma waye yasaka sai nakoya muku hankali sai na nuna muku kuskuren shiga gonata ba atakani in kyale sai nasaku kunyi nadama sa min ido da kukayi cikin rayuwata taqarasa fada tana fitar da wata iska me zafi daga bakin ta tare da cije baki tana karkada kai kujerar ta koma ta zauna tare da dauko wayar ta takira wata number ana dagawa ta tashi daga falon ta nufi dakinta ranta amugun bace dasauri sauri take tafiya kamar zata tashi sama tana zuwa bakin qofar ta turata da qarfi kamar zata ballata tana shiga tabugo qofar da qarfin gaske......

Sam

Ransa fess yake jinsa dan yasan ko banza de yasanya mata tsoron sa aranta duk dade yasan bata da gaskiya amma de babu abun da yasani akanta kawai de yayi mata hakane dan yagano abun da yake zargi kuma zarginsa ya kusa zama gaskiya yanzu tunda yagano logonta yanzu zai qara saka mata ido har Allah yasa yagano komai da wannan tunanin yaqara sa shoga falon Ammah da sallama abakin sa momma ce ta amsa masa sannan yaqarasa shiga cikin falon ya samu kujera ya zauna yana facing dinsu sannan ya shiga gaida momma din ta amsa masa fuskarta asake tana qara duban dan nata da kyau abun alfaharin ta Amra dake kan cinyar momma tana buga game awaya batasan wanda ya shigo ba tade ji anyi magana amma bata tantance muryar waye ba saboda hankalinta kacokan yana kan game din datakeyi shiyasa takasa dagowa taga ko waye shima kuma hankalin sa nakanta yana kallonta ganin har yanzu hankalin ta nakan game yasashi ce ke me yahana ki zuwa makaranta yafada da dan daga murya saura kadan tasaki wayar hannun ta Allah ya taimaketa tayi saurin tare ta tare da mikewa zaune tana muzurai da idanuwa sannan tashiga kame kame tana marairaice murya tace bani da lafiya fa yau kwanana biyu a kwance wani kallo ya watsamata da yasata yin shiru bata gama fadar abun da tayi niya ba shiru tayi tana turo baki tana qara matsawa kusa da momma qasa qasa tace momma kice masa banda lafiya bayan bezo ya dubani ba amma zaizo yana wani zare min ido ni wallahi ma na matsu yatafi harar wasa momma tayi mata sannan itama qasa qasan da murya tace au hakama kikace to bari ingaya masa da sauri tace rufamin asiri momma so kike yakarya miki ni tace asuwa yaza ayi inso a karyamin auta ta momma sauri nake in kuma intafi to nazo kuma kintsaya kina biyewa wannan sakarar yarinyar muryar sam takatse musu zancen da sukeyi qasa qasa dagowa momma tayi tana kallon sa sannan tace to inbazaka iya jiraba ai qofa abude take mutum dai bakin halin jaraba maganar momma ba qaramin sosa mishi rai tayi ba amma ba yanda zaiyi tunda itace dole yayi hakuri da ita miqewa yayi yace fine kawai yadaga qafa zai tafi tace wallahi idan kabar gurin nan sai na mugun saba maka har inkira kazo kuma shine zakatafi saboda gaka isashe da mai ko to bismillah jeka cak yaja ya tsaya shi be tafiba shi be zauna ba jin gakan yasa Amra tashi daga gurin ta tafi dakin su saboda duk rashin mutun cinta da rashin kunyar ta inde za ayiwa mutum nagaba dasu fada ko kuma za ayi wata maganar da bai kamata suji ba to zasu tashi subar wajen wanna tarbiyar momma ce ita ta dora su akai dan hakan yanzuma jin zata fara yimasa fada yasata tashi tabat wajen kuma daman da biyu ta tashi tasan ko ta zauna ma daga qarshe zai iya sauke fushin sa akanta shiyasa tayi saurin guduwa,

ahankali yadawo ya zauna awajen da yatashi yayi shiru tare da qara murtuke fuska ya hadeta waje daya kamar an ajiye kunu yakwana haka fuskarsa ta koma bata damu da ganin fuskarsa hakaba saboda inda sabo tasaba ganin ta ahaka dan haka tayi shiru tana binsa da kallo tare da yimasa addu'ar Allah ya shiryeshi yadena wannan dabi'un da kwata kwata bata qaunar taga yanayi duk datasan abune me wahala yadena saida tagama jan lokaci batare da tace masa komai ba shima kuma ko dagowa ya kalleta ba beyiba kawai yazauna tare da cusa lip dinsa abaki yana ciciza da qarfi daman da wani fushin ya fito gashi kuma yazo itama taqara masa wani,
Chapter 25 · 0% Book details