← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 128

Sashe 98

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 6 min read

Addua Daddy ya umurta ayi, a tare kowa yayi suka fara cin Abinci, kasancewar duk Abinci da busasshen kifi da kuma gasasshen kifi akayi, in ba ci kayi ba ba zaka gane kifi bane, yafi kama da Nama.
Ko Cokali biyu ba suyi ba numfashin Zaid da Najwa ya fara daukewa, sama sama Numfashin ya fara, AbdulMajeed da ya kafa Najwa da ido ya lura da abunda takeyi yayi saurin ajiye spoon yace "PureHeart are You OK?" Zaineema ta kalli Najwa tayi saurin mikewa tsaye Hajia Aynarh ma haka, Najwa me ya faru? Abu takeyi kamar mai neman shidewa, Ziyada ta dan waiga ta kalli Zaid, gabanta ya fadi, irin abun Najwa yakeyi, numfashin shi samasama, fuskarshi yayi ja, da sauri ta karasa gunta "My Forever, lafiya" Hankalin Mairo ya tashi ta mike ta ci kwalar Aunty Aynarh "Munafuka Algunguma, me kika sa ma Abinci? Me kika sa ma sirikina? So kike ya mutu" Aunty Aynarh ta tsure sosai tana girgiza kai tace "Wallahi bansa komai ba, Wallahi ba abunda na sa, mukai su Asibiti" Najwa ta riko hannun Hajjo tana bankarewa kamar zata mutu, Zaid ma hannu ya sa ya rike wuyanshi yana jan numfashin dake fita da kyar, fuskar nan tayi Ja, Daddy yayi saurin fita don taro A daidajta sahu a kaisu Asibiti, yana fita ya ci karo da Convoy din Zaid, Ziyada Hawaye kawai takeyi hankalinta tashe, Abdulmajeed hankali a tashe ya kalli Aunty Aynarh yace "Aunty kinsa Kifi a abincin nan?" da sauri ta gyada kai tace "duka abincin da Kifi nayi shi" Abdulmajeed ya ruga kitchen a guje, Ya shiga bincikar Kayan Miya da ya siyo dazun Tomatoes ya dauko, ko wankewa beyi ba ya fito ya mika ma Ziyada 1 yace ki bashi, lokacin sun fara fita daga hayaccinsu, fasawa yayi da bakinshi ya juye ma Najwa ruwan tumatirin a baki, haka Ziyada ta ma Zaid, a hankali a hankali numfashin su ya fara dawowa daidai, daidai nan Idi da wasu Yaran Zaid suka shigo sukayi kan Zaid wai zasu kaishi Asibiti, daga musu hannu yayi yace "i'm fine" Ziyada tace "me ya faru da kai?" Zaid yace "ina tsammanin Abincin nan akwai Fish, and i'm allergic to Fish" daidai lokacin da Najwa ta ke ce ma Hajia Aynarh "Dama bansan da kifi a cikin Abincin ba, shine naci?" Hajia Aynarh tace "I'm So Sorry, wallahi bansan ba kwa son Kifi ba, Abincin ba wanda ban sa Kifi ciki ba, kuyi hakuri donAllah" Najwa tace "Laah Aunty ba wani abu, ni in na samu irin attack dinnan da na sha tomato zanji normal, ai farkon zuwana Nigeria na taba samun attack din" Abdulmajeed yace "shiyasa na tuna Tomato ne first Aid treatment din" Zaid ya kira Idi ya zo kusa dashi, ya rada mai abu a kunne, da sauri ya fita, Aunty Aynarh duk tayi wani iri, gani take laifinta ne, Zaid ya kalle su Daddy da sukayi cirko cirko suna kallonsu yace "Baba Abba ku zauna ku cigaba da cin Abincinku, Ni kifin ne bana so, yanzu zaa kawo min wani Miyan sai in ci" Daddy ya sage yana kallon Zaid, wani abu ke bin zuciyanshi, dunia Zaidun Sada kadai ke ce mishi "Baba Abba" jiki a sake ya zauna, yace da Muhsin su cigaba daci, Daddy ya kallesu yace "sai kuka tuna min da k'anina Marigayi, kunsan shi ko kanshi Kifi ya ji sai ya fara sheshek'a?" Hajjo ta chabe tace "haka ne, ko abinci nayi da Man kifi in ya fara Amai kamar zai zazzago kayan cikinsa" Zaid ya runtse idonsa yana tausar zuciyarsa. Abincinsu su ka cigaba daci banda su 3, Zaid da Najwa da Mummy, su kadai ne basu cin Abincin, gaban Mairo ke dukan uku uku, ta kalli Najwa a kalli Zaid, tunanin da bata son yi ta fara yi, Sada be cin Kifi, Zaid din Sada be cin Kifi, Wannan dan Sada ne. Da sauri ta girgiza kanta ta tashi kamar mahaukaciya ta shige daki, daidai nan Idi yayi Sallama da Cooler a hanayensa, Gaban Oganshi ya Dire, Ziyada ta bude Miyan Kubewa danya ne da yaji Jan Nama, ta bude wani Amalan ta sa mai da miyan Kubewar, ta kalli Najwa tace "in sa miki ko? " kai Najwa ta daga, Ziyada ta zuba mata suka cigaba da ci, Hajia Aynarh ta saukar da Ajiyar zucia ganin basuyi zargin ko tayi poisoning dinsu bane.

I N D I A

Duk wasu Process na tafia sun gama, Jirginsu zai tashi Gobe zuwa Dubai, washegari su tafi Nigeria inda zasu isa Lagos daga nan suyi Kano, Paapa da Maama sunyi Resigning a wuraren Aikinsu, an basu kudin Sallama me tsoka, harta Motocinsu da Gidan da suke zaune sun saida, Paapa ya samu wani Agent dan Kano suna communicating, nan ya tura mishi kudi ya siya mishi dankareren Gida a Tarauni, don shi baya tunanin zai koma Gidanshi na da, yafi karfin ya tada Yayanshi a gidan da yake, ya bar mai Gidan nan har abada, Maama ta dinga shiga Gidajen Neighbors dinsu tana musu sallama, Vijhay Bhaiya yayi kuka sosai, Maama tace "InshaAllah zasu zo wani lokacin" bayan sun mishi Alheri me yawa, ko da ta shiga Gidansu Kaveri nan suka bata lokaci da Maman kaveri suna jimamin rabuwansu, Kaveri kuwa bata fito ba tana daki tana cizgar Kuka.

N I G E R I A.

Rigima Ziyada ke ta ma Zaid tun tashin su yau da safe don ya sanar da ita Tafiar gaggawa ta kamashi zuwa Taraba, zai biya Kaduna ya ga Gidan Marayu kafin Jirginsu ya tashi zuwa Taraba's state. Ziyada tace ya tafi da ita, hakuri ya bata cewar tayi hakuri, ya dawo, da ya dawo zai musu processing Visa suje any country of her choice, sannan in sun dawo Gida zasu yi Parking su koma Gidan Babanshi na Asali a Kaduna, dolenta ta hakura amma taso ta bishi don bata son yayi nisa da ita. Alfarma ta rokeshi da ya barta a koma Gida har sai ya dawo, da farko k'i yayi, yace tayi hakuri ta zauna har randa zai dawo, tace "itadai aa, ba zata iya kwana ita kadai ba " ba yanda ya iya ya amince mata da taje Gidan, a daren da zai tafi, makale suke da juna kamar cingam, baya so ta bishi sabida bussiness zaije yi, da wuya ya samu time dinta. Washegari da kanshi ya rakata har Gida bayan an musu siyayya a Shoprite, sunfi Minti 20 a gaban Gidan cikin Mota suna manne da junansu kamar kar su rabu, shagwaba take ta zuba mai, shi ko yayi ta biye mata, "i'll miss you i'm My Forever" rungumeta yayi yace "i'll miss you more" sun dade a haka kafin daga baya ya rakata har Cikin Gidan, suka gaisa da yan Gidan banda Mairo da ba wanda ya lura be gaisheta ba. Daddy ya masa godian Hidiman da yakeyi dasu. Ziyada a boye ta share hawayenta da zai tafi, shima duk yaji ba dadi, ta zama wani bangare na jikinshi.
****
Najwa sunyi waya da Su Maama sun gaya mata Jirginsu zai tashi a ranar da daddare, but zasuyi transit a Dubai washegari su iso lagos, dadi ya ziyarci Najwa, ta musu fatan a iso a lafia.

B A Y A N K W A N A B I Y U
Chapter 98 · 0% Book details