← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 128

Sashe 108

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan wasu Mintuna suka iso Airport,聽 nan suka iske Idi yana jiran zuwansu, cike da girmamawa Idi ya gaidasu,聽 ya matsa kusa da Ziyada ya mika mata wasu Envelop yace "inji Oga" ta karba tace "tohm nagode ko?" Paapa yace "Oya Abdulmajeed je duba kaga inda ake sayar da Tickets kaje kaga nawa ne na Yola?"Idi yace "Erhm, Tickets din na hannun Madam" Ziyada ta kalli hannunta, Idi yace "karamar Envelop din ta sama" ta zare babban ta mika ma YaMajeed,聽 ya bude ya ga tickets guda takwas,聽 ya kalli su Daddy yace "Toh Su Paapa sai ku sama inlaw dinku Albarka,聽 ya siya tickets din 168k 21k per one" nan suka shiga sama Zaid Albarka,聽 Ziyada kuwa girman Zaid ya karu a idanunta.
Idi yace "Madam jirginku zai isa 15mins to 12" Akwai wanda zasu tarbeku da Motan ZSA,聽 Allah ya kaiku lafiya" godia suka ma Idi,聽 suka wuce inda Jirginsu zai tashi.
****

Y O L A

Kamar yanda Idi yace hakan ne,聽 Motoci uku suka zo don tarbansu Ziyada,聽 sai da Majeed ya musu magana a tabbatar su din ne kafin聽 suka shiga Sienna su duka,聽 Yan tarbansu suna musu sannu da zuwa,聽 Driver din yace "wani Unguwa zaku?" Paapa yace "bari muga Yesmeenah zaki tuna suna Unguwan naku? " dariya tayi tace "kai dai kace ka manta,聽 Mallam Jimeta zamu" ya ja mota suka fara tafiya.
Gaban Maama na ta fadi,聽 bata san me zata iske a gidan nasu ba,聽 komai ya chanza na daga da garin,聽 da aka kara karaso unguwansu kuwa hawaye ta fara yi,聽 kasancewr gidansu kan hanya ne,聽 daidai gidan tace "Ya isa,聽 anzo" Driver ya ci birki,聽 suka fita,聽 ba ta jira kowa ba ta isa Gidan da sauri, a Soro suka ci karo da Baffa rike da chasbaha,聽 da alama masallaci zaije,聽 tsohon dan fulani amma da karfinshi,聽 chak ya tsaya yana kallon Matar da ke gabanshi tana haki kamar tayi聽 gudu,聽 Inallilahi wa ina ilaihir rajiun yake maimaitawa kamar ya ga fatalwa,聽 bakinta na rawa tace "Baffa" bakinshi na rawa shima yace "Aisha Yesmin" da sauri ta isa gareshi ta rungume Mahaifinta,聽 da fullanci yake cewa "kece wallahi,聽 baki mutu ba" nan su Paapa suka聽 iso,聽 Bapha yace "Sada,聽 Wai ya akayi na ganku raye? ku min bayani?聽 Sada ya karaso ya dafa Baffa yace "Massalaci zaka ai?" muje duka, muna nan baffa har sai ka gaji da ganin mu,聽 yace "ku kuma ku karasa ciki,聽 nan suka shiga sukuma mazan suka bi bayan baffa,聽 drivers suka shigo da kayyayakinsu,聽 Yesmin da sauri ta shige cikin babban gidansu tana kwada sallama,聽 wasu yanmata suka amsa sallaman,聽 da alama bata san su ba,聽 su ma kallon su kawai suke,聽 suna cewa "sannunku da zuwa" yesmin tace "ina mutan Gidan" Nene Asibi ta fito tace "baki ne a gidan namu?聽 Sannunku da zuwa" Yesmin ta tashi ta rungumeta, "Nene Asibi" ta dagota ta kalleta tace "yau na shiga uku,聽 jamaa ga fatalwa a gidan Ardo" Maama tace "wallahi ba Fatalwa bace nice, Yesmin dinku,聽 ban mutu ba" mamaki suka tsayayi,聽 tace "wai ina Umman Shehu, ko tana Sallah" Nene Asibi tace "hmm,聽 Yesmin,聽 saidai hakuri,聽 Allah ya ma Mahaifiyarki Rasuwa Shekaru 12 kenan" wani irin juyi gidan ke mata,聽 kamar zata fadi,聽 gabanta na fadi,聽 da sauri Naajwa da Zaineema suka riketa,聽 da kyar a ka zaunar da ita,聽 kuka takeyi a hankali,聽 ba rabon su gana da Mahaifiyarta,聽 nan dai Hajjo ta shiga bata baki, har aka samu ta shiga toilet don yi alwala tayi azahar.

A GURGUJE

Abu na waya,聽 tuni aka kira Yanuwa da abokan Azziki aka sanar dasu Yesmin bata mutu ba gashi ta dawo gida da ita da Mijinta da kuma diyarta,聽 kafin dawowar Masallacin Jumaa,聽 gidan Baffa cike,聽 da murna,聽 da yasa basu santa ba,聽 lokacin da take nan ba a haifesu ba,聽 wasu kuma basu da聽 wayau,聽 nan aka shiga yi mata ta'aziyar Mahaifiyarta.聽 Nan fa aka shiga cikasu da abincika kala kala,聽 da su Ardo suka dawo daga masallaci a ka taru a parlornshi,聽 Daddy ne ya musu bayanin duk wani abu da ya faru,聽 kuma be boye musu cewa Matarshi ce sanadi ba,聽 nan aka jajanta wa juna,聽 Baffa yace聽 InshaAllah zai basu maganin kariya.
****
Kwanan su Takwas, suka dawo Kano,聽 sunji dadin zamansu Yola,聽 sun saba da mutanen chan. Zaid ma ya dawo Jiya, tun da Idi ya zo taryansu Paapa yace mai "Mijin Ziyada ya dawo ko?" Idi yace "eh ya iso,聽 yaje dai wani aiki ne" Paapa yace "Oya ka maidata Gidanta" batayi musu ba don tayi kewan Mijinta sosai.
Aka Maida Ziyada Gidanta,聽 Daddy ya sa su Paapa komawa gidan da ya siya a Tarauni,聽 Gidan Paapa yayi kyau Sosai,聽 ba wani katon Gida bane,聽 3bedrooms ne,聽 da Zaineema da Najwa suka tafi,聽 Hajjo ta k'i yarda ta bisu,聽 ya zamana Gidan su Uku ne daga ita sai Daddy sai Majeed, duk gidan yayi wani iri,聽 Sada ya ma Abba maganar dawowa da Mairo,聽 ya nuna mai bacin rai,聽 ya nuna be son maganarta,聽 nan yayi shiru,聽 yace bayan an dan kwana biyu zai sake bijiro mai da maganar.
*
聽聽 Tana isa gidan ta fada wanka,聽 ta ci kwalliyarta cikin Riga da Skirt na atamfa ta zanzara kwalliyarta tayi kyau sosai.
Shikuma Ogan Niyyarshi ya gama aikin da yake ya wuce Gidansu Majeed ya dauko matarshi,聽 don ya mayi kokari da be bita chan yolan ba,聽 sosai yayi missing dinta,聽 Idi ne ya sanar dashi cewa matarshi na Gida,聽 haba kamar jira yake ya ruga da gudu mota yace a kaishi Gida,聽 dokin ganinta yake,聽 yayi missing dinta da yawa,聽 ana isa ya fita da sauri,聽 tana jin shigiwanshi ta fita itama da gudu,聽 ba su damu da maaikatan Gidan ba,聽 ta rungumeshi shi kuma ya dagata sama yana juyi da ita yana jin dadi,聽 daukarta yayi har cikin dakinsu kafin ya direta,聽 nan fa suka fara gwada ma junansu yanda sukayi missing din junansu,聽 ta mishi godian abubuwan聽 da ya musu tun daga ranar tafiarsu Yola har dawowansu,聽 nan ya hade bakinsu yana shaida mata cewa su abu daya ne,聽 ba godia a tsakaninsu.

B A Y A N聽聽 K W A N A聽 B I Y U

Maama ta dafa Abinci ta zuba a cooler tace ma su Zaineema su tashi su kai ma su Daddy Abinci,聽 dama sun shirya,聽 suka dauki Basket din ita da Najwa suka fita bayan ta basu kudin Keke Napep.聽聽 Suka fita suka tafi gidan hajjo, Abdulmajeed da Daddy聽 basa nan ko da suka isa,聽 Najwa tace "Didi,聽 kizo muje gidan Zuzu" Zaineema tace "Aa ba zanje ba" "Haba didi, kizo muje please,聽 ba dadewa zamuyi ba" Zaineema tace "ke ni ki kyaleni,聽 ina Yaya,聽 ba zan dinga bin gidan k'anwa ba" Najwa tace "Oh,聽 nikam na tafi,聽 tace sai kin dawo" Najwa tama Hajjo Sallama,聽 ta fita ta tsaida keke Napep don yanzu ta zama yar聽 gari,聽 Gidan Ziyada ta nufa.
***
Ziyada na kwance jikinshi Wayarshi yayi k'ara,聽 tsaki yayi kadan,聽 ya janyo wayan,聽 ganin me kiranshi ya sa shi sake buga tsaki,聽 Ziyada tace "Yadai My Forever?" yace "takura min suke sonyi daga gurin Aiki" yayi karya,聽 tace "ka dauka mana" ya mike yace "ina zuwa" ya fita rai a bace,聽 zai bata ma Na'ilah rai,聽 meye zata ding damunshi?聽 Salan ta ja mai matsala da Ziyada,聽 fita yayi daga Parlorn yayi bayan Gida inda da yakanyi waya lokacin yana matsayin Nura.
Shigowanta聽 Gidan kenan,聽 da yake Zaid ya janye tsaron nan bata samu wahalan shiga gidan ba,聽 hango shi tayi yayi baya yana latsa wayar,聽 a ranta tace "mugu,聽 muguntan zakayi ko?" ta so ta share ta shiga gun Ziyada, amma sai ta samu kanta da bin bayanhi.

聽聽 聽聽 "Na'ilah,聽 whats your problem wai,聽 meyasa zaki dameni,聽 na gaya miki ba zan iya aurenki ba, i've told you not once not twice cant you get that to your head? Haba!聽 Naci na meye?" don kin taimakeni nayi achieving goal dina,聽 ai ban sa ki dole ba,聽 you chose to help me willingly" bata ji me Nailahn ke cewa ba taji yace "aiko tona min asiri will be the last thing you will do, ba ruwanki da zuwa kusa da Matata balle ki gaya mata abubuwan聽 da nayi, Na'ilah kar ki sake"
Chapter 108 · 0% Book details