← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 128

Sashe 126

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowa yayi dakin inda take zaune,  ya yaye mayafin kanta,  ya dago fuskarta suka k'urawa juna ido,  murmushi suka sakar ma junansu yace "taso muje" ba musu ta sauko daga kan Gadon, hannunta ya rik'e ya sauko da ita daga Kan Gadon, janta yayi,  ya dinga nuna mata daki daki, da kitchen, ya gabatar da masu aikinta guda biyu,  da haliey er niger,  da wata bilki,  su ka zube kasa suna kwasan gaisuwa, haka yace "kuna iya komawa dakinku sai da safe" a ladabce suka musu sallama suka tafi baya inda dakinsu yake.
Abdulmajeed ya kalli Ziyada yace "PureHeart, ina jin yunwa" ta kalleshi tace "barin dafa maka wani abu" hanyar kitchen ta nufa yayi saurin kamo hannunta ya gyada mata kai ya jawota ta fado k'irjinshi ya matseta yace "wa ya ce miki Amare na shiga kitchen?" turo baki tayi tace "but you are  hungry" jawota yayi yace "zo muje" ba gardama ta bishi daki,  mayafin da ya aje ya sa mata,  ya ja ta ya fita,  mukullinshi ya dauko na daya daga cikin motocinshi,  hannunshi rike da nata ya jata suka fita daga gidan,  ya bude mata mota ta shiga yayi horn maigadi ya bude musu suka fita.
Abuja ba bak'on garin Abdulmajeed bane, a nan yayi samartakanshi,  KFC ya nufa dasu,  Pizza suka ci da kaza, suka sha drink,  kafin tace "Muyi ma su Bhaiyy take away" Abdulmajeed ya daga kai sama yace "da sukaci dadin su sun tuna da ke?" shagwabe fuska tayi tace "haba Jaan" yace "OK Ok" nan ya bada order aka kawo musu cikin wasu lokkutta suka karba suka koma Gida,  har isha'i suna hanya,  suna isa Maitama me makon su shiga gidansu sai suka shiga na Zaid,  Suna Parlo rungume da juna,  suka shiga da Sallama,  Ziyada zata tashi Zaid ya matsota ya girgiza mata kai,  maskewa tayi suka karaso inda suke,  Najwa tace "Bhaiyy,  we bought you Pizza and chicken" Zaid yace "Awwwn Thanks Baby,  mungode though yanzu muka ci dinner,  amma zamuci ko da safe sai muyi microwaving" Abdulmajeed  yace "Kin gani? I told you" Zaid yace "Mallam munce mungode,  dama nasan baby ta saka siyo mana" Ziyada tace "ni wallahi ina jin marmarin pizza" Zaid ya bude baki yace "MyForever yanzu fa kika gama cin Abinci har kina cewa cikinki kamar ya fashe" Ziyaa ta sake gyara kwa ciyarta jikinshi tace "Now i want to eat "Abdulmajeed ya kalli Ziyada yace "Zuzu baki da kunya ko? Kina ganina kin tsaya jikin Mijinki ko? Kina ta shishige mai! " kunya ya bata ta rufe fuskanta cikin k'irjin Zaid tace "YaMaji" Zaid yace "A'a A'a,  ba zaka zo Gidana ka takura min ba,  Baby ja Mijinki ku tafi mungode,  byebye" Najwa ta turo baki tace "Bhaiy niko?" Zaid yace "Baby baki ga zai takura ma Ziyaa ba" Abdulmajeed ya jawo hannunta tare da cewa "muje my forever" Zaid yace "pizxa din fa?" Abdulmajeed be juyo ba yace "je ka siyo mata" da sauri Zaid ya tashi ya sha gabansu da sauri yace "Please big bro,  ka bamu, Zuzun ka fa zataci bani ba" Abdulmajeed ya tabe baki jin yanda ya fadi zuzu kamar wata zazu ya mik'a  mai package din yace"Zuzu ake cewa" Zaid  yayi dariya daga chan Ziyada tace "Goodnight YaMaji and Najwa" Majeed yace "Dont talk to us" daidai k'ofa Zaid yace "sai munzo da safe" Abdulmajeed yace "kar na ganku a gidana" sukayi daria gabaki daya ya ja matarshi suka wuce nasu gidan.

Suna isa Gida Najwa ta fada toilet,  shima dayan dakin ya shiga ya watsa ruwa,  sai gashi ya fito cikin farar jallabiya,  itama Alwala tayi har tayi Sallah,  ya shigo da sallama, sanye ya ganta cikin Night gown doguwar riga Ja,  ta mai kyau,  komai indai nata  ne na mishi kyau, yace "PureHeart,  kinyi sallah?" tace "eh nayi" yace "oya taso mu k'ara wani" ba gardama ta tashi ta matso kusa dashi,  ya tada musu sallah,  rakaa biyu sukayi,  Abdulmajeed ya dade yana musu addua da larabci da kuma hausa,  har suka shafa,  tambayoyin Addini ya fara mata,  nan ya fuskanci Najwa ta na da Karatun K'urani duk da ba hadda ba,  amma tana da rauni wurin Fiqh da sauran litattafai,  though dai ta karanto mai yanda akw wanka haila,  ta kuma san cewa duk wanka iri daya ne,  niyya kawai ya bambanta,  gyara ya mata akan tambayoyin da bata san amsarsu ba, ya kuma ce mata kar taji kunya yana tare da ita, ta tambayeshi duk abunda ya shige mata duhu,  kuma kafin lokacin da zata zana WAEC zai shigar da ita wani Islamiyyan Matan Aure wanda akeyi Lahadi zuwa Laraba da safe 9-1, in lokacin shiga Makaranta yayi sai ta dawo na yamma ko asabar da lahadi,  Godia ta mai ya dagota suka  mike kan kafaffunsu,  zuwa makunni fitila ya nufa ya kashe wutan Ya jata zuwa kan Gado.
*Asuba ta gari Pure-Jaan*

*A GURGUJE *

Cikin Kwanaki 21, Masoya hudun nan sun k'ara kyau sun girgije,  har wani k'ibak'iba sukayi,  k'auna ce suke ginawa a gidajen su mai tsafta,  zumuncinsu ya dore,  kaunar junansu suke,  Ziyada ta koma Makaranta,  kamar yanda Abdulmajeed ya ma Matarshi Alkawari hakan ko akayi,  ya sakata a Fallahil Islam dake nan k'asan Maitama,  kullum shi ke kaita,  ko yana aiki sai ya yanke ya je ya daukota,  ya kumayi enrolling dinta a wani Catering School wanda zata dinga yi Online.
In suna Gida ko Najwa ta shjga Gidan Zaid,  ko Ziyada ta shigo Gidan Abdulmajeed.
Yau ma hakan ne, Najwa ta shigo Gidan Abdulmajeed, wanda cikin Ziyada ya dan fara turowa, ta  ciko ta kara k'iba, Ziyada tace "Muje baya muyi hoto" Najwa tayi daria tace "su kuma masu ciki har craving din hoto suke?" turo baki tayi tace "wai ba MyForever yace ki dinga min abunda nake so ba?" Najwa tayi daria ta daga hanuwanta sama tace "Sorry Matan Bhaiy,  muje muyi hoto" Ziyada ta mike ta ja hannun Najwa suka fita daga Gidan tace "backyard zamuyi" "duk yanda kikeso Hajiata" Ziyada ta kwalawa Mai aikitan kira tace "H-Jiddarh, zo ki mana hoto" jiki na bari H-Jiddar tazo ta karbi wayan ta shiga daukansu".



Suna gama Hotuna kuma suka bige da Video Call da Zaineema.

K A N O

Zaman Lafia ake a Gidan Daddy,  sun hade kansu suna kyautatawa Mijinsu da  Surikarsu,  ko waccen su tsakanin Mummy da Aunty Aynarh burin kyautata ma Hajjo suke,  tana jin dadinsu.
Mummy ta shiryu,  ba ruwanta da kawayen banza amma kunsan wata sain me hali baya barin halinshi,  takan nuna isanta gun kawaye don ta keta su fiye da tunaninsu,  amma baya ganan bata da matsala.
Daddy kuwa ya narka wata k'iba,  hutu da kwanciyar hankali ya darsu mai a cikin zuciya,  zumuncinsu da danuwanshi Sada sai abunda yayi Gaba.

A Gidan Paapa Zaid ya wadatar musu da komai,  duk asuba sai tayi waya da Yaranta da Surikanta,  bata da kadaici don akwai masu Aiki,  da wata babbar mata haka,  sannan diyar Yayanta Umaimah da take rik'o yar shekara 6, Allah yayi ma Umaimah farinjini don tun tana jinjira mahaifiyarta ta rasu,  kowa na sonta ,  yarinyar na da farinjini sosai,  one of  the best schools a Kano aka sata,  so Ko kadan Maama bata da kadaici.

Ana Azumi na saura Kwana Goma suka tarkato sukazo Kano don gabaki daya zasu tafi Umrah suyi Azumi Ashirin A chan,  Gabaki dayansu a Gidan Daddy suka sauka, nan aka yi ta murna da zuwansu,  Hajjo ta dinga dirka ma Ziyada Kayan kwadayi,  su Zogale da kwadan rama da sauransu.  Ana jibi Azumi jirginsu ya tashi zuwa Madinatul Munawwarah,  Daddy,  Paapa,  Hajjo, Mummy,  Maama, Aunty Aynarh,  Abdulmajeed, Zaid, Ziyada, Najwa, Zinatu,  Muhsin da Umaimah..



A chan suka ci rabi da kwatan Azumi kafin suka dawo,  a Kano sukayi Sallah.  Kafin suka koma Abuja.
Ba jimawa Najwa tayi WAEC,  ba da dadewa ba sakamako ya fito da kya, Makarantan su Ziyada aka nema mata,  bayan wasu lokutta ta fara classes a kan course din da ta zaba .

*MONTHS LATER(Bayan wasu 'yan watanni)*

K A N O

Maama zaune suna fira da Mummy, Mummy tace "wai ni Hajia Aleeya tazo neman taimako gurina?" Maama tace "Rayuwa, kin taimaka mata ko?" tace"Waaa?  Ni, ai wallahi koran kare na mata,  na kuma nace ma maigadi in ya sake ya barta ta sake shigo min Gida A bakin aikinshi" Maama tayi daria tace "Allah ya huci zuciyan uwar gatan marayu" Mairo na karkada kafa tace "Wallahi irinsu Hajia Aleeya ke kai mutum ga halaka,  Allah ka nissantar damu daga sharrin irin kawayen banzan nan" Maama tace "Ameen Ameen" Aunty Aynarh ta turo kofan Parlorn da Sallama, tana yatsina Maama tace "Ahhh,  ga Maman Biyu" Dan dariya tayi ta shigo ta samu wuri ta zauna tace "Maaman Umaimah bansan kin shigo ba" tace "ban dade ba,  yanzu zan shiga da mu gaisa" Aunty Aynarh tayi dan guntun tsaki, tace "Nidai Wallahi sam bansan warin Part dina,  zuciyana tashi yake" Mairo tace "ai kece bakya jin magana,  sai da nace miki ki dawo part dina,  kin k'i" tace "ai gashi na dawo, in ma na ga nan din nogo,  Kwara zan tafi,  wallahi ba zan iya ba" Mummy tace "nima na biki wallahi,  dan ba zaki barni nikadai ba" Maama tace "Ya zakuyi da Yaya fa?" Aunty Aynarh tace "yo ga matarshi" Mummy tace "Haba dai,  ai wallahi kina tafia, zan biki,  nima ban ina son zuwa Kwara" Maama tace "Sai ku dawo ku iske Yaya har ya auro mata Biyu, daya part dinki,  daya dayan" Daria suka fashe,  "ai ba ya fara ba" Maama tace "uhm uhm dai" suka sa daria.

K A D U N A
Chapter 126 · 0% Book details