← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 128

Sashe 59

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

tanan yake fita ba yana kai aya ya mike a fusace ya nufi bedroom dinsu. Tsoro ya darsu a Zuciyar Mairo, ko a shekarun baya da yake mata fada be mata irin wannan ba, sosai ta tsorata, k'aryarta ta k'are, things are falling apart, tunani kala kala a kwanyar kanta, saboda tsabar mamaki ko yatsunta kasa dagawa tayi balle ta iya cewa wani abun. Yanda taga Rana haka ta ga dare, kwatakwata bacci kauracewa Idanunta yayi, Abubuwa kala a ranta, ta kasa gane dalilin da ya chanza Daddy dare guda, Lallai reshe ya juya da Majuyi, wai yau ita Daddy ke daga ma Murya, har ya kirata da Sakarya,Tabbas dole ta tashi tsaye ta san abun yi tun kan dare ya mata, a dayan Bangaren karon farko da tsoron Haduwarta da Nakowa ya darsu a Zuciyarta, Daddy duk ya ruguza mata lissafi, bata san ya zata kaya ba, a kan Idonta aka kira Assalatu. ******* Sosai ta firgita da taji abinda ake so ta fada a Kotu, ta kalli Dad da Mom kafin ta kai dubanta ga Attorney dinsu, tace "Amma ba haka bane ba fa, ni da kaina na dauki Credentials din nan, na kai ma wani a waje, ya za kuce ince bansan da zancen ba?" Mom ta hau lallashinta tace "ita sam ba zata karyata Majeed ba" Dad yace "Nana, do you want to rot in Jail? In ba haka kikayi ba, za a saka ki a Prison kuma i cant save you, ina so ki ba Attorney Hadin Kai, zan sa a nemo mishi Credentials dinshi, zan bashi aiki, kuma zan rokeshi ya maidaki dakin ki, that is in munyi winning case din, others ba zaki koma dakinshi ba, kuma zaa kulle ki maybe life imprisonment" Sosai ta tsorata, bata son haka ya faru, bata son zama part of any of this, kawai tana so ta koma wurin Majeed dinta, a wuce gurin, a haka Dad dinta ya dinga dorata, da kyar da sudin goshi ta amince zatayi abunda suke so, haka aka dinga karanto mata Irin Shaidar da zata bada a Court Gobe. (Anzo gurin,daidai gurin, who is excited? Ghen ghen) KOTU Kotu ta cika ta batse da jama'a, kowa da zaman da yazo saurara, mafi akasari manyan Mutane ne abokan Huldan Hajia Mairo Da Alhaji Nakowa, kowa ya hallara, Nana ta k'i yarda ta kalli inda su Majeed ke kallo, a ka gabatar da Shari'ah, Ba tare da bata lokaci ba Alkali ya umurci Lauyan masu kara da ya gabatar da Majeed a gaban Kotu. Majeed ya fito jiki ba kwari, yau ko Breakfast beyi ba, tsayawa yayi inda aka tanada domin bada Shaida. Lauyan Alhaji Nakowa ya nemi da abasa izini ya yiwa Majeed tambayoyi, nan take Kotu ta bashi dama. Lauya Usman Baraji Me kare wadda ake k'ara ya fara jefa masa tambayoyi kamar haka: "Ko zaka iya fadawa kotu Sunanka, inda kake zaune da kuma Sana'ar ka? Jim Majeed yayi kafin yace, "Sunana AbdulMajeed Abba Abu, ni mazaunin garin Kano ne, a halin yanzu bana aiki Amma ni Architect ne". "Mallam AbdulMajeed shin menene Alakar ka da Wacce ake kara?". Majeed ya hadiye miyau din takaici kafin ya amsa da; "Matata ce a da amma yanzu babu aure a tsakanin mu, ba ma tare". Lawyer ya sake jefo mai tambaya"Wacce take k'arar fa ko menene Alakar ka da ita?" A takaice yace"Mahaifiya ta ce". Barrister Usman Baraji ya karanto ma Majeed k'arar da Mahaifiyarshi tayi ya tambayeshi "Mallam AbdulMajeed muna so ka gaya ma Kotu, shin wannan bayani da na maka haka yake?". "Eh ya mai sharia haka abun yake, babu tangarda a bayanan da mahaifiyata ta ba ma Kotu". Barrister Usman Baraji yace "tsakani ga Allah kaga Lokacin da Nana Nakowa ta daukan maka Credentials ta ba ma wani?" Majeed yace "Aa bangani da ido na ba, amma da bakinta tace ita ta dauka". Barrister yace "tambayar itace Kaga Lokacin da ta dauka da Idonka?" Majeed ya hadiye miyau yace "Aa bangani ba" Barrister yace "Kaji Audion da ake ikirarin tayi a cikin Maye?" Majeed yace "Eh da kunne na naji". "Mallam AbdulMajeed Kotu tagode da wannan shaidar da ka bayar zaka ka iya zuwa ka zauna har sai an sake buk'atar ka." Yayi Godia ya juya ga Mazauninshi. Barr ya maida dubanshi ga Alk'ali yace " Ya Mai girma Mai sharia, a report din da muka samu, sun nuna mana tambayarta yayi wata ba ma Takardunshi, k'ilan ta tsorata da wani abu ne ta amsa abunda ba tayi ba, sannan kuma maganar Audio dinnan, muna so a sanya ma Kotu taji, Nagode Ya Mai girma Mai sharia ". Alkali ya juya kan Lauyan Mairo ya umarce sa da ya gabatar da shaidunsa. Lauyan Mairo ya mike cike da isa ya ce "Ya Mai Sharia, Shaidar mu Kenan AbdulMajeed, kuma ya bamu tashi Shaidar, shikenan shaidan da mu ke da". Cikin zafin rai Mairo tace "wani irin shikenan Barrister Khalim? Ina audion? Ka musu Playing". "Wani Audio kenan Hajiya"? "Kutumar Babba burauba! yau akeyin ta, Bar khalim bansan wasan banza dana wofi, Audion da na tura maka lokacin da nazo Office dinka, nace maka Alhaji Nakowa ya sa anyi Attacking Aliyu Abokin Majeed an goge Audion, don kar a samu matsala na zo har Ofishinka na tura maka?" Barrister Khalim yace "Aa Hajia Mairo, i dont know what you are talking About, ni baki turo min ko wani Audio ba". Wani tsallen da Hajia Mairo tayi sai da ta chakumo wuyan Barrister Khalim, tace " Ni zaka mayar 'yar iska? Kaika Nakowan ya sayeka ko? To wallahi baka isa ka mayar dani mak'aryaciya ba" Alkali ya tsawatar ma Mairo, yace "ta yi taka tsantsan da yanda take gabatar da kanta a gaban Kotu, Kotu ba zata dauki wulakanci da shashancin banza, Kotu ta ma Mairo gargadi da Babban Murya. Mummy tace " Ayi Hakuri Ya Mai Sharia, raina ne ya baci, amma ba matsala in shi ya sayar da Audion, ni ban sayar da nawa ba, yana nan cikin Wayata" Alkali yace "ta gabatar da Audion gaban Kotu" da Murmushi tace "Minti daya" ta koma gun zamanta ta bude Jakarta ta ciro Wayarta ta hau latselatse, kusan mintina 5 shiru, take zufa ya hau ketowa Mairo audio dinnan ko sama ko kasa ta rasa shi a wayarta. Da sauri ta kalli direction din da Alhaji Nakowa yake, watsowa mata mairo murmushin mugunta yayi, zufa ya shiga keto mata, ta san k'aryarta ta k'are, a hankali tace "Yau ake yinta" wurin Barrister Khalim ta nufa, tace "Bar Khalim kai wa girman Allah ka bada audio dinnan, kayi hakuri, i'll pay twice what they paid you". Barrister Khalim yace " Ki daina bata min lokaci, ki daina bata ma Kotu Lokaci, hakan na nufin, there was never an Audio, you made everything up" Zuciya taci Mairo, ta hau surfa ma Barrister Khalim Zagi ta uwa ta uba, Alkali ya sake tsawatar ma Mairo a karo na biyu yace "Malama Mairo idan kina da wata shaida da zaki gabatar to bismillah kotu na sauraronki inko babu to kotu zata zartar da hukunci a kammala wannan shariar ba ku kadai bane" Ai kamar jira take nan ta hau surfo balai da masifa ba kan Lawyern kadai ba Kotun duka, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, zage zage take kamar sabon hauka,sai sakin layi take tayi "ni zaka yaudara Khalimu? wato Alhaji Nakowa yayi bribing dinka? Ya saye Kotun gabaki daya, har Alkali tsohon Najadu, to wallahi ba zata sabu ba, sai na shayar daku madaran Mamaki dukan ku" Alkali ya umurci YanSanda su kama Mairo, "da sauri Majeed ya nemi Afuwa a madadin Mahaifiyarshi, ya ba Alkali hak'uri, janta yayi ya koma wurin Zama don jiran Hukuncin Judge. "Lawyern wanda ake k'ara ko kana da abun cewa?" cewar Alkali, Barrister Usman Baraji yace "Ya Ma girma mai Sharia, ina so Kotu ta gayyaci Nana Nakowa gaban Kotu" "Kotu na Bukatar Nana Nakowa a gabanta" Alhaji Nakowa ya sadda kansa daidai yanda Nanan zataji shi yace "go Nana, you know what you must do" kai ta gyada ta tashi ta je gaban Kotu ta tsaya, Bayan ta amsa tambayoyin Gabatarwa Barrister Usman Baraji ya fara mata tambayoyi kamar haka; Add Vote Nana Nakowa, shin kin dauki Credentials din AbdulMajeed?" tace "Aa ban dauka ba" "ya akayi kika tsinci kanki a halin da kike ciki yanzu?" Nana ta juya ta kalli Mummy tace "Wata rana Mummy ta kirani dakinta tace ince ma Dad dina ya bani 5mil" sai nace mata tayi hakuri, shima Daddyn beda kudi yanzu, shikenan ta fara threatening dina, wai in ban nemo mata kudi ba, zamana da Yaronta ya k'are, zata k'ala min sharrin da ba zan iya firda kaina ba, da nuna mata ni ban san inda zan samo mata kudi ba ramfa ya baci, the next day sai naji tace wai na sace ma Majeed Credentials kuma wai ina bin Maza" Mairo mamaki ya hanata motsi, ta san ita Makira ce, amma bata taba zaton Nana ta fita iya Makirci ba, kirikiri Nana ta shirga mata k'arya, kotu ya hau surutu, kowa da abunda yake tofawa, sai da Alkali yace 'Order' kafin aka sausauta. Barr Usman yace "Mungode Nana Nakowa, Ina son Kotu ta kira mana Alhaji Ado Nakowa" Alhaji Nakowa ya gabata gaban Kotu, Barr yace "Me ke tsakaninka da Hajiya Mairo?" Alhaji Nakowa yace "Matata k'awarta ce, kuma mun taba wata kwangila da Alhaji Abba Abu" Barrister yace "kace kana da Maganan da kake so kayi a gaban Kotu kafin a yanke Sharia?" "Ya Mai sharia "A lokacin da AbdulMajeed yake auren Nanata, Hajiya Mairo tana amfani da son da diyata ke ma danta tana amfani da hakan matsayin jarinta kamar yadda ta gaya muku da kanta, bata sati bata buk'aci kudi daga gun diyata ba, in Nana ta nuna babu saibta mata barazana cewa zata sa Majeed ya saketa, haka diyata ta kare rayuwarta gidan Abba Abu cikin Barazana, baya ga haka, ina bin Hajia Mairo Naira Miliyan 30, ta karba Miliyan 20 kamin auren danta da yarwurina, Miliyan 10 kuma daga baya ta karba bayan sunyi karayar Arziki, nima ba su ke gareni ba a lokacin, amma saboda naga akwai Alakar auratayyar
Chapter 59 · 0% Book details