← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 128

Sashe 18

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haba Zaid, Meye haka kakeyi? Baba ya fi karfin wulakanci a wurinka, ya wuce haka a gunka, be chanchanci haka daga gareka ba, kar a zama dan Adam butulu mana din kaga yana son ka.
*
Hello Lovers, ya kukaga Babi na Goma? Zaid be bata muku rai ba? Nidai ya ban haushi. Ya batan rai sai da na sa Omo da soso na wanke lol.

#1love
#ADAY
#anatare
#bibiliciousfreakingfans
#nagode.

Biebee Isa
#
[12:02, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1鈨�1鈨�

聽 聽 聽聽 Da gudu ya danna Motar ya bar Unguwar Gaba daya, Zuciyarshi na mai zafi, don me Baba zai ce ya manta da komai? Don me Baba zaice ya yafe musu, don me Baba zaice yai watsi da abun da ya k'uddurta ba zaiyuwu ba, he's waited for this time his whole life, he cant just push it away. Amma Zaid Baba ne fa, your Only Parent, wanda yake son ka fiye da rayuwa da kanta, dan guntun tsaki yayi chan kuma ya rage gudu ya ci birki k'iiiii.
聽 聽 聽 *
Zubewa Baba yayi kan kujera yana maida numfashi a hankali a hankali, idanunshi a lumshe, Zaid ya gaya mai magana, Zaid ya watsa mai kasa a ido, Zaid ya nuna mai be isa dashi ba, it hurts really bad yanda ya dauke Zaid ba haka Zaid ya dauke shi ba, da Zaid zai tsaga Zuciyarshi, da ya ga shi kadai ne abunda yake so a Duniyan nan, dafe kanshi yayi da hannu bibbiyu domin kanshi ya mai nauyi. Ji yayi digar hawaye a k'afanshi, da sauri ya bude idanunshi tare da kallon kasa, Zaid ya gani kwance kan kafafunshi yana kuka, da sauri Baba ya dago Zaid, Zaid ya k'i dagowa ya daura kanshi kan cinyan Baba, yana kuka, Baba yace "Yadai Zaid?" Zaid yace "Kayi hakuri babana, ba zan sake ba". Ajiyar zuciya Baba yayi ya shafa kan Zaid yace "Baka laifi Zaid" Zaid ya girgiza kai, yace "Aa Babana, i'm so sorry, i mean it, ba zan k'ara ba ka yafe min, you are all i got kuma ina sonka with every breathe i take in" dadi ya lullube Baba, ya daga Zaid ya rungume yace "i forgive you Zaid, i'm not trying to take away your happiness, i know these people wronged you, amma Inallaha ma'asabirin" Zaid yace "Shikenan Babana, ya wuce" ya mik'e ya shige daki, yanda yayi maganan zaka san be kai har zucci ba, Baba ya bishi da ido yana kallon shi, ya san donshi yace maganar ta wuce, don yafi karfin shi, ba wai don yana so ba, anya baya nuna son kai cikin lamarin Zaid? Baya son ya rasa Zaid, gani yake zai iya rasa Zaid idan Mairo ta ankara dashi,amma in hakan zai ba Zaid fariniciki, zai cika mai burinshi, kuma zaiyi protecting dinshi until his last breath, Wayarshi ya ciro ya latsa yayi kira.
鈥�*
B A Y A N聽 K W A N A聽 B I Y A R
聽 聽
聽 聽聽 Tun bayan maganarshi da Baba ya koma rayuwar daki,ba聽 ya bude k'ofar dakinshi,har makaranta ya yanke zuwa, haka Iya zata ta buga k'ofar don ya bude amma ba ya budewa, damuwa ce ta mai yawa,bai k'ara shan giya ba say tari sai ya bude zai sha sai ya fasa don yasan Baba ba zai ji dadi ba. Waya Iya ta ma Baba, Dama Baba bai Gari, ta gaya mishi halin da Zaid yake ciki,kullum sai sunyi waya,amma be taba nuna mai akwai wata matsala ba, hankalinshi tashe ya shaida mata yana nan zuwa Gobe da sassafe.
Hakan kuwa akayi Washeagari wurin k'arfe 4 sai ga Baban Zaid ya dawo, be tsaya amsa gaisuwan da Maaikatan gidan ke mai ba ya shige cikin dakin Zaid, ya shiga kwankwasawa, Zaid be tanka ba a zatonshi Iya ce, saida Baba ya ciri baki ya kirashi, "Zaid taso ka bude min" gaban Zaid ya fadi, yana mamakin me ya dawo da Baba yau Wednessday? A hankali ya rarrafo gun k'ofar ya bude jiki a sa6ule, da azama Baba ya kutsa kai ciki, ya nufa inda Zaid ke tsugunne,nan da nan ya ga ramar Zaid, ya fad'a yayi bak'i, hannu ya sa ya janyo Zaid tare da rungumeshi idanunshi a lumshe, jikin Zaid da Zafi, Baba yace "Zaid what did you do to yourself? You look Miserable, what are you turning yourself into?" baki na rawa Zaid yace "i'm sorry Babana,kar ka damu please" Baba yace "hmm, na san damuwarka, na san meyasa ka haka,ina zuwa" Baba ya tashi ya bar dakin, chan sai gashi ya dawo da wata k'atuwar envelop, murya a dishe ya mik'a mai envelop din yace"if its because of Abba Abu's details here you go" farinciki ya ziyarci Zaid, amma abun mamaki kawar da kai yayi ya k'i amsa, Baba yace "ka karba, you've waited all your life, take it" cikin murya me kama da ta rada yace "bana buk'k'ata kuma" Baba yayi ajiyar zuciya yace "Zaid, you have Rights to this, ba zan tauye ma na, you are grown up now about 21years, i shouldnt be deciding what you should or shouldnt be doing,make your own decision, so take this envelop, everything you need is there, the whole Information" sosai yaji dadi amma sai yace da Baba,Is this Ok with you?" Baba ya daga kai yace "Go ahead Son" hannu biyu Zaid ya sa ya karba envelop din. Baba ya mik'e yace "barin shiga wanka" Allah Allah kawai yake Baba ya fita yanzu, yana fita Zaid ya bude Envelop din, da hotuna ya ci karo.

Hoton Farko Hoton tamfatsesen Gida ne.

锟�

An rubuta full address and description na Gidan a Maitama district,sai kuma daga k'asa a kasa Late Sada Abu's property. Zaid ya hadiye miyau, wannan gidan ma na Babanshi ne kenan, shine suka tare da zama ko? Mu je zuwa dai.

锟�

AbdulMajid da Zaineema aka sa a jikin Hoton na biyu, Sosai Zaid ke binsu da kallo one by one,Abdulmajid, his loving brother,yayi girma be da matsalar komai, kilan tun bayan tafiar shi ya manta dashi, while shi kullum sai yayi kukan rashin shi, haushi ya cika fal zuciyar Zaid,tsanar Majid na ratsa shi kafin ya kai dubanshi ga Zaineema,look at his Zaineema, duk ta girma abunta,a yanzu ba digon sonta ko kadan a ranshi.
A k'asan hoton aka rubuta details in su, AbdulMajid, Oxford University, yana karantar Medicine yana 2nd year dinshi,ga numbern wayanshi,email address dinshi,Facebook and twitter account.
Zaineema tana Nigerian Turkish tana SS3.
聽 Ajiye hotonsu yayi ya dauko na wacce a ka rubuta Ziyadatu,Sosai yayi mamakin bayan Zaineema Mairo ta haifa yarinya har ta girma haka?,clearly yarinyan looks young and preety, nan itama aka bada details dinta na tana primary 5 a wani Primary School.

锟�

Sai Hoton Autan Abba Abu wato Zinatu, yarinya ce da ba zata wuce shekaru hudu ba, ran Zaid sai tafasa yakeyi wato 'yayan Baba Abba Hudu, ba wanda ya san nan gaba nawa zasu k'ara haifawa, shi an kashe mai mahaifa, su kuma suna nan suna ta hayyafa, da Maamansa na nan, kila itama da tayi 4 ko 5 nan take idonshi ya dira a kan hoton mutanen da ba zai taba mantawa ba, Hasken da suka kara, ko k'ibar da sukayi be sa su chanzawa a idon shi ba, ba zai taba Manta fuskar su ba, musamman fuskar Matar da ya tsana fiye da fir'auna, Hoton dauke yake da fuskokin Baba Abba da Mairo suna daria, basu da wata damuwa basu da matsalar komai, sun salwantar da rayuwanshi amma sun cigaba da tasu rayuwan ba tare da damuwa ko wani abu ba, a Baiyane Zaid yace "Baba Abba, dan Zaki ya girma, you and your family will pay for what you did to me and My Family. Enjoy the little time you have, farincikin ku ba me dorewa bane, zan tarwatsa ku duka, zan tarwatsa farincikinku, ku yi amfani da damar nan kuji dadin rayuwanku na tsawon Shekarun da zan tashi tsaye kanku, nan ba da jimawa ba, i'm coming for you all, i'll come for you time din ba zato ba tsammani, da ranku amma zaku so mutuwarku, ba zan daga muku ba, ba zan rage muku ba, Ramuwar gayya tafi ta gayya zafi, ni Zaid Sadam Audu, nayi Alkawarin rusa Farincikinku gabaki daya".
*
聽 聽 聽聽
聽 聽聽 I N D I A

锟�

Najwa Sada Abu ta taso cikin So da k'aunar Mahaifanta biyu,yarinya ce me shiga rai, kawarta daya tun tasowarta, Kaveri,makarantar su daya, ta samu komai na rayuwa, Najwa ta tashi tana jin Yare uku zuwa hudu a duniya, Hausa a bakinta don Mahaifanta Hausa suke mata duk da Hausanta sirkakke, Turanci kuwa a Makaranta sukeyi, tun tana yar kankanuwa in tana Turanci sai ka rantse baturiya ce,ga kuma Yaren Hindi, Haba yarinyar da aka haifa a k'asar India ai dole take iya yarensu,gashi ko don Vijhay bhaiya da ta dauke shi kamar聽 na jini, har yau ya kasa iya Hausa balle Turanci. Duk sadda Najwa ta rikide tafara Hausa ko Turanci ko Indiyanci, to sai ka bude baki kana kallonta, don duk yaren da tayi sai kace bata iya ko wanne yare ba sai shi.

锟�
Chapter 18 · 0% Book details