← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 128

Sashe 80

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

Girgiza kanta takeyi tana kuka tace " Karyane, wallahi kana sona, i refuse to believe all this, ka nuna min ingantacen so, ba zan yarda ba, in ma kana da wani unfinished bussiness da su Mummy ne, i dont care, ku zauna kuyi settling din kanku, ku yafe ma juna, amma kar ka min haka , donAllah kar ka min haka" Zaid yayi fuskan tausayi yace "Awwwn, My Poor Wife, ba kyason Mijinki ya barki ai?聽 Congrats Ba zan barki ba, amma zaki so mu rabu, duk da ba zan rabu dake ba sai na tabbatar na muku tabon da ba zaku taba mance ni ba" ya tsugguna ya dau jakkarshi ya fice daga parlorn ita kuwa rushewa tayi da wani irin kuka mai ratsa zuciya.

A cikin Mota ya zauna ya dinga sauke ajiyar zuciya da karfi, kanshi ya dau chargi, In ranshi ya baci, abu daya kawai ke kwantar mai da hankali in ya shiga irin yanayin nam, da sauri ya fita ya bude booth, Akwatin Armstrong ya bude, Gwangwanin Giya sun kai goma daga gani masu tsada ne, ya dauko daya da karfi bude lid din zai kafa kai ya sha.
"Zaid Alkawarin da ka mun kenan?" Ya rantse da Allah muryan Babanshi Sadam yaji a kwanyar kanshi, da wani irin murya kamar fatalwa, da sauri ya wurgar da Giyar hannunshi ya fada Mota聽 ya latsa horn aka bude mishi gate da sauri, ya fincika Motar da karfi ya fita daga Gidan, Driver dinshi da Odile suka shiga wata Motar suka bi bayanshi a guje.
Saida ya kusa Minti 50 yana zagaye garin Kano, kafin ya samu ya dawo daidai, daga bisani ya buga tsaki da karfi? Meye hakan to?" Armstrong ya kira ya bashi umurnin ya wuce Airport Direct.
掳掳掳掳掳掳掳
Har wurin k'arfe biyu tana nan yashe a inda Angonta ya barta,聽 zuciyarta na tukukin zafi,聽 bata son yarda da duk wasu magananunshi,聽 zata cigaba da mai uzuri har ya dawo gareta,聽 a yanda ta fahimci maganganunshi, Akwai wata boyayyen zance tsakaninshi da Iyayenta,聽 a yanda yake yada mata habaici ta gane Iyayenta sun taba mishi wani laifi, to me zasu mishi?聽 Zaid fa ba zai wuce tsaran YaMaji ba,聽 in kuma laifi suka mishi ko wani nashi meyasa zasu yarda ya aureta,聽 to menene? duk yanda taso gano kullaliyar da ke ciki ta kasa,聽 su kadai zasu gaya mata meke faruwa,聽 da sauri ta tashi ta nufa daki dan kiran Mommy a waya,聽 tana son jin komai, abubuwan da suka faru a baya kafin a haifeta,聽 turus ta tsaya da ta tuna wayarta na hannun Zaid,聽 ba kuma ta isa ta fita ba,聽 hawayenta sun kare karkaf,聽 ta fada toilet don yin Alwala don ko Azahar batayi ba.
****

A cikin Jirgi Armstrong聽 ya lura da Zaid聽 yayi nisa cikin tunaninshi,聽 ya dan tabo shi yace "Are you OK?" Zaid ya danyi tsaki yace "I'm fine" arm yace "You want to talk about it?" Zaid a fusace yace "Shut the f**kup Arm" Armstrong ya daga hannunshi sama yace "Sorry,聽 naye shiru".聽
Duk yanda be so yayi tunaninta ya kasa,聽 kawai ya dauko earphone babba ya sa a kunnenshi ya kura volume duk dai don ya manta da tunanin da zuciyarshi keyi.

Bayan kwana biyu....
PORTHACOURT 10am

A daddafe yayi kwana biyun nan,聽 wani hali take ciki?聽 Me takeyi?聽 Ba wai don ya damu ba fa,聽 kar ma ayi zaton ya damu, kamar an tsunguleshi ya tashi聽 a zabure,聽 ya kira Arm,聽 yace "book a flight to Kano"Armstrong聽 yace "why?" a fadance Zaid yace "Stop Asking question聽 stupid,聽 book the goddam flight" Armstrong聽 yace "OK i got you" ya kashe wayan ya kira waya,聽 chan ya sake kiranshi yace "Sorry boss,聽 they'd be no flight to Kano today(saidai聽 kayi hakuri,聽 ba jirgin kano yau)" ran Zaid a bace yace "Seriously? Then get my Private Jet" Armstrong聽 zaiyi magana Zaid ya katse shi da cewa "Arm if you wont get me to Kano i'll find someone who will(Arm in ba zaka kaini kano ba,聽 zan nemo wanda zai kaini)" cikin聽 sanyin jiki Amstrong yace "OK boss" Amstrong ya kashe wayan yana mamakin meke samun Zaid,聽 duk ya sukurkuce lokaci guda,聽 ya zabure yana abubuwa kamar someone that is desperate,聽 da wannan tunanin ya iso Gidan Zaid, Driver ya kai su inda Private Jet din ZSA yake,聽 kasancewar Amstrong ya iya tuk'a Jet,聽 shi ya tuk'a Jet din,聽 a hanya Amstrong聽 ke tambayan Zaid meyasa yake son komawa Kano da gaggawa,聽 Zaid yace saboda yaje a cigana da kuntata ma Ziyada,聽 in ba sa tare zata fi sakewa, tafi walawa,聽 shikuma be son ganin ta sakata ta wala, amma in yana nan zata takura ta zama cikin kunci. Armstrong ya tabe聽 baki,聽 yayi shiru da bakinshi don kar yace wani abu a hayyayako mai.

KANO 1pm
聽聽 Abin duniya yayi ma Mairo cunkuso, komai ya tsaya mata cak ta rasa meke mata dadi. Banda tunani kala kala bata komai. Hankalinta na tashi a duk lokacin da ta kira wayar Ziyada taji switched聽 off, Tun auren Ziyada batasan inda aka kaita ba, tayi tunanin duniya ta gano amma ta kasa. Ta gaji da Kira wayan Ziyada don baya shiga, nan fa ta rinka surfa ma MTN zagi kala kala tana kwashe masu albarka.
Duk da haka ba ta daina trying number dinba, a hakan har charging wayanta ya kare kap. Garin masifa da rawar jiki taje ta 茩one charger saida haya茩i mai firgitarwa ya fito.
Gefe ta koma ta rukuba tana huci, abin duniya yana damunta,聽 ta tambayi daddy da Abdulmajeed duk sunce basu san inda Gidan Ziyada yake ba,聽 duk da sun san ko ba dade ko ba jima sai ta san inda diyarta ke zaune,聽 Wani dabara ya fado mata taje wajen dangin oduduwa watau Hajia Ainau domin tabbas tasan inda take,聽 ita ta kaita dakin Miji.
Da farko tayi kememe da shawarar amma kuma saita tuna batada wani tudun dafawa, gwiwa a sanyaye ta rinka fizgan jiki har Gidan Hajia Aynarh,聽 ita wallahi bari dai ta gano gida ziyada, sai tace ma Zaid tana bukatar Mota don abun kunya ne a ce tana surikar Gatan Marayu kuma tana hawa Keke Napep聽 .

聽聽 Babu kunya ba tsoron Allah tayi ma Hajia Aynarh聽 sallama a dakile聽 da mamaki Hajia Ainau take kallonta bata taba zaton Hajia Mairo聽 ta san gidanta ba,聽 nan ta murtuke fuska ta amsa mata sallamar ciki ciki.
"Ina wuni ina gajiya?" Hajia Mairo tace don tana son suyi su gama ta tafi gidan diyarta,
"lau" kawai Hajia Ainau tace saita cigaba da abinda takeyi wato shan kankana, batayi mata tayi ba banda danna waya na rashin dalili data soma,聽 don聽 har ranta tana kishin Hajia Aynarh.聽
聽聽 Hajia Mairo idan ranta yayi dubu ya 蓳aci amma saita danne saboda ita take neman taimako wajenta. Murya yana rawa ta tambaya Hajia Ainau inda Ziyada take.

聽聽 "Nima ban sani ba" Hajia Ainau ta amsa mata a takaice, 聽 Kakalo murmushi Mairo tayi saita ce, "Haba Hajia kiyi hakuri mana Dan Allah ki fada min inda take, wallahi inasan ganinta ne. 'Yata ce kwana biyu kenan ina kiranta a kashe,聽 dole nake shiga damuwan rashinta,聽 ki gaya min please"
聽 Ita kam Ainau halin ko ta kula tayi sai laste laste take na na' urar bature. Mairo kam sai magiya takeyi har saida H. Ainau tace mata cikin izgili "jeki tsohon gidanku tana chan" a zatonta Gatse Hajia Aynarh takr mata,聽 tace "DanAllah聽 ki gaya min,聽 tana ina?" tace "Haba Hajia Mairo, ya zaki zo kina min ihu akai,聽 nace miki tana tsohon gidanku na GRA,聽 me kike so kiji bayan nan?聽 DanAllah ki rabu dani"
"Ban gane tsohon gidan mu ba" ta fa蓷a ido a warware gabanta na bugun taratara
聽聽Hajia Ainau bata ce mata ci kanki ba, nan tabama banza ajiyar ta.
Saurisauri gudu gudu Mummy ta fita daga gidan ta taro Adaidaita聽 tace a kaita GRA,聽 kuma tsakani ga Allah聽 ko kudin Napep聽 din bata dashi,聽 in taje ta bada.
***
A cikin kwanaki biyun nan,聽 wanda ya san Ziyada ya ganta ba zai ganeta ba cikin wannan yanayin,聽 duk ta rame ta jeme,聽 akwai abinci a gidan,聽 amma bata iya ci ko ta dafa,聽 bata bacci don fargaba ta ya zata kwana a gidan nan ita kadai,聽 sai dai bacci barawo ya saceta,聽 ta sha kokarin guduwa marasa imanin nan ba sa barinta fita ,聽 ba hanyar guduwa,聽 hawayenta har sun kafe,聽 kukan ma bata iyayi,聽 Ziyada dai ta koma abar tausayi, tana kan daddumarta tana Addua taji alamun an bude kofar parlo,聽 a guje聽 ta kwasa ta fita聽 parlon,聽 ganin Zaid tayi sanye cikin riga top聽 da ta waje da wando jeans Zai rufe kofa.

锟�
Chapter 80 · 0% Book details