← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 128

Sashe 44

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba, yayi parking, A tsorace suka shiga gidan a Parlor suka iske Muhsin na Kallo, Oyoyo ya tashi ya mai, ya bi su Hajjo da ido, Majeed yace "Muhsin ba ka gaida Hajjo ba" cikin hausanshi yace "Ina kwana" Hajjo hawaye ya ciko mata, wannan Jinin Abba ne, amma ko haihuwarshi bata sani ba ta shafa kanshi tace "Ina wuni dai ko?" ya gyada kai, Majeed yace "je ka kira min Zuzu da Zainee" da gudu yayi dakin Ziyada yana kwada masu kira "Ya Ziyada, Ya Zaineema, Yaa Majeed na kiranku". Nana na jin Muryan Majeed ta fito, tana yauk'i idonta ya sauka kan Najwa, Najwa gabanta ya fadi, Nana ta daure fuska, "My Majeed me wannan yarinyan ta dawo yi?" a tsaye ya kalleta yace "Zauna" jin muryanshi cike da seriousness ya sa ta zama, ba ta damu da Tsohuwar da ta gani ba. Ziyada ta shigo parlorn da Sallama, Murmushi kawai ta ma Najwa ba tare da tace komai ba, ba wai don ta san Hajjo ba ta gaisheta, Hajjo tace "Ziyada ce?" Majeed yace "eh itace" ya kalli Ziyada yace "Zuzu kinsan wannan?" ta girgiza kai alamun "Aa" ya jinjina kai yace "ta shiga ta kira Zaineema, Kafin tazo sai ga Zainee ta fito rai bace, bata san abun da zai dameta, ta fito ta kalli Hajjo shekeke, ta so ta ganeta, don ta san ta, da wayonta ta je gidan Hajjo, don dai kawai sun dade basu hadun nan bane, ko nuna alamun ta santa batayi ba tace " YaMajeed gani" a dakile yace " baki iya gaisuwa ba? Ko ba ki ganeta bane?" baki ta turo tace "Ina wuni?" Hajjo ta amsa ta na Murmushi, Majeed yace "Barin kira Mummy". Duk da Gabansu duka faduwa yakeyi, amma sun dake, Majeed ya shiga Dakin yana Sallama, fushi takeyi dashi da Daddynshi sabida zuwan Hajia Aynau, yace "Mummy, munyi bak'uwa" hararshi tayi tace "waye" yace ke dai taso "Mummyna" jan hannunta yayi suka fita Parlo, Najwa ta hango, bata gane ta kusa da ita ba, Ranta a bace tace "dawowa da ita kayi?" har suka zo gaban Tsohuwar, Mairo tsakani ga Allah bata gane ko wacece ba, sai da Hajjo ta bude baki tace "Mairo mun wuni Lafiya?" kamar ta arta a guje don dago me muryan baki na rawa tace "Hajjo?" ta juya ta kalli Majeed cikin rashin fahimta. "Me kikeyi a nan Hajjo?" Majeed yayi saurin cewa "don Uwa ta zo Gidan danta sai ace me tazo yi?". Majeed ya kalli kannenshi yace "Ziyada, Zinatu Muhsin, Meet your Grandmother, itace Mummyn Daddy" Mummy tace "Majeed What are you Doing?meyasa ka kawota nan, ya ma akayi ka san inda take?" Majeed yace "Mummy, Hajjo ta dawo nan da zama, mutuwa ta raba, gidan Danta ne" wani Shewa Mummy ta sake tace "Kutumar Bala'i, ka fara shayeshaye ko Majeed? Kowa ka gani ka kwaso kace nan ko? To Wallahi baka isa ba, tun kuruciyata ban zauna da Hajjo ba, yanzu ba zan zauna da ita ba Wallahi, dole ta koma inda ta fito" be bi ta kanta ba yace "Ziyada, ina so ki koma dakin Zaineema da zama, ki bar ma Hajjo da Najwa dakinki kinji?" Ziyada tace "Okay Yaya" da dan Dokinta, ba wai tana da saurin sabo bane, amma sai taji son Kakarta, ta matsa kusa da ita tace "Najwa taimaka ki tayani kwaso kayan Tsohuwar nan, barin nuna mata dakinta" Hajjo tayi dariya tace "kece dai Tsohuwa, kina gani na sabon Jini" Najwa tayi daria, Ziyada ta kama hannun Hajjo ta mik'ar da ita. Mummy ta finciko Ziyada, tace "kar ki tabata" Majeed shima ya janye Mummy tare da daga murya "Enough is Enough Mummy, uwar Mijinki ce kike ma haka as if she's a piece of trash?" Mummy tace "She is a Piece of trash" Ran Majeed ya baci yace "Mummy, Wa billahilazi Laillahaillahuwa, ba me bina bashin rantsuwa, idan kika takura, ko kika muzguna wa Hajjo while her stay here, Z.an tafi, zan barki Mummy, and i will never Come back, kindai ji rantsuwar dan Musulmi" baki na rawa tace "Majeed are you threatening me?" yace "i am not, na dai gaya miki,idan na tafi, i will make sure you never see me again" to ya tabo kahon zuciyarta lakwas tayi, huci takeyi, bata son abun da zai rabata da Majeed, fuu ta wuce daki kamar zata tashi Sama, ya kalli Nana yace "And Najwa, shes my Guest ba ruwanki da ita, ko kallon banza kikayi mata, dagaske zan rabu dake Nana" Nana ta k'ulu iya kuluwa, ta tashi a fusace ta wuce daki, Ziyada tace "karki damu Tsohuwa, muje Daki" Hajjo tayi dariya tace "zaki san tsohuwa in saurayinki ya ganni yace ni yake so" sukayi daria duka, Majeed yaji dadin yanda Hajjo ta sake lokaci guda, ya zaro wayanshi ya kira Daddy yace ya dawo gida akwai bakuwa na jiranshi, Daddy yace dama yana kusa da Gida gashi nan dawowa. * Daddy na dawowa Majeed be ce mai komai ba ya ja hannunshi ya turashi dakin Ziyada. * Mairo kuwa kamar tayi hauka cikin daki, meke faruwa da ita ne? Asirin da tayi ya fara karyewa ne? Ya akayi Majeed yaje Gidan Hajjo? Ya akayi Hajjo ta yarda tazo Inda suke, bayan Boka ya tabbatar mata da cewa sun rabu kenan da Abba? Ya akayi Abba ke mata gardama har ya na wurganta da mugun kallo Tab duniyar na juya mata baya, a fili tace "na shiga uku ni Mairo".. 掳掳 Bibilicious freaking fans, da fatan munyi Sallah lafiya, nagode da yanda kuke hakuri da rashin post din da ke zuwa muku da wuri, ku min uzuri, ina da patient din da ba lafiya, ku sata a adduoinku don Allah, Allah ya bata lafiya ya sa Zakkan jikine Amin. So ya Wannan Babin? Me kuke tunanin zai faru nan gaba? Any hunches? guesses? No? Drop your Votes and Comment Line by line Please. #1love #ADAY #bibiliciousfreakingfans #anatare DADE ANA YI....sai gaskia馃挱 NA BIEBEE ISA 庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Wattpad:@biebeeisa Pg2鈨�1鈨� Ramewa, tsamurewa da Duhun da tayi ba zai sa ya mance Fuskar nan ba, Fuskar da tayi sanadiyar kawo shi Duniya, Fuskar Mahaifiyarshi ya gani a jikin Madubin dakin Ziyada, hawaye suka soma suntiri a kuncinshi, bai tantance ba, shin dagaske ne itace ko ba ita bace ba, Matsowa yake tayi har sai da ya zo daf da daf da ita kafin ta zube kan guiwowishi gabanta. Ba su ji shigowanshi ba, sai dai ganinshi sukayi durk'ushe gaban Hajjo yana Kuka, baki na rawa tace "Abbaaa" cikin muryan Kuka yace "Ummma", Ziyada ta ja Hannun Najwa suka fita suka bar musu dakin. Kasa daurewa Hajjo tayi ta fara Hawaye, Daddy kasa magana yayi dai hawaye, sai ya bude baki zaiyi magana sai ya kasa, Itace tace " Kar ka damu Abba, Kayi Magana". Kuka mai sauti ya sake kamar karamin yaro, "Umma, ni mai laifi ne na sani, ni watsatse ne na sani, ni butulu ne na sani, duk son da kika nuna min, Umma ni na sa k'afa na shure, ni na wofintar dake, fiye da shekaru 5, bansan cin ki ba, ban san shan ki ba, Umma Allah ba zai barni ba, kema ba zaki yafe min ba, amma Umma ki sani, bansan meke dawainiya dani ba, amma Wallahi ba yin kaina bane, Wallahi bansan ya abubuwa ke faruwa ba". Murmushi mai ciwo tayi, ta dago hannu ta shafa fuskarshi, tace " Abba, na sani, na san ba yin ka bane, kar ka damu, Akwai Allah, Allah ba Azzalumin kowa bane, Allah na yafe komai banda hak'k'in Mutum, in dai ina da Hak'k'i, Allah ka bi min Hakki na akan duk wanda ya shigo tsakani na da Yaro na, Allah ka bi min Hakkina, Wahalan da nasha Allah ka sani, Allah ka isar min, kayi shiru Abba,kar ka sake zubar da hawayenka, na yafe maka". Gyada kai yayi amma ya kasa tsaida kukan, Kamo kanshi tayi hannu biyu, ta karanta mai Ayatul Kursiyu da AmanarRasulu, sai wasu daga cikin ayoyin Shi'fa, ta tofa mai akai ta shafa kanshi, shiko ya saura kanshi a kan cinyarta yana sauke Ajiyar Zuciya. * Ziyada ta ja Najwa Kitchen don daura Abinci, Ziyada jin kanta take cikin Farinciki, Zahiri bata da san mutane amma sai taji ta sake da Najwa, kawai yau Nishadi takeji, Tuwon Semovita Miyar Egusi tace da Najwa zasuyi, Najwa dai kallonta take tayi da ta kasa daurewa sai tambayanta tayi meye tuwo?" Ziyada ta kalleta da mamaki, Ya zaayi Najwa tace bata san Tuwo ba, ai har Ghanan sun san Tuwo, yanda da ta ga Najwan nayi ne ya sa ta zargin ko Najwa 'yar Ghana ce kuwa?, amma rana bata karya, "ban labarin k'asarku Ghana" inji Ziyada. Hinkim Gabanta ya buga, bata san komai da k'asar Ghana ba, kuma har yanzu bata farfado daga Yaudaran 'yan Nigeria ba, Generosity din Majeed da Ziyada ba zai sa ta yarda da su ba har ta bude mata sirrinta, inda inda ta kamayi, a tak'aice tace "Zan baki labari wata rana, yanzu dai muyi focusing kan Tuwo". Yanayin da tayi maganan yasa Ziyada zarginta, amma don dai bata da hujja ya sa ta kauda tunanin wani abu. Haka suka cigaba da Girki har sai da suka gama Tuwo da Miyan Egusi, kafin Najwa ta fita don bata son warin Kifin da Ziyada keyin Farfesun *Catfish *. *** Wani Fara'a taga Daddy nayi, baki har kunne, bakinta na rawa tace " Daddy, me ke saka farinciki?" galala ya kalleta, yace "Ji Maryam da wata magana, Umma nagani mana, har kya tambayeni me ke sani Farinciki? Ga abu a Zahiri?" kinsan yaushe rabon da na ganta? Yau da tace min ta yafe min, sai naji kamar an sauke min dutsen Uhudu a kai, Allah ya ma AbdulMajeed Albarka, yanda ya sadani da Mahaifiyata, ba zai taba tabewa ba da sunan Rabbi" Mamaki ya hana Mairo Magana sai dai uhm da tace. Haduwa sukayi gabaki daya a Dining Table, da k'yar Majeed ya samu Mummy ta fito, Daddy jiki sai rawa yakeyi, ya dauko Coolern Parpesun Kifi ya tura ma Hajjo Gabanta yace "Umma, kici" Murmushi ta mishi, mantuwa ya mance rabon da taci Abinci haka, abu kadan Daddy zaice "Umna kaza, Umma
Chapter 44 · 0% Book details