Sashe 90
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Binshi tayi da idanuwa, So take gani a Idonshi, Kula da damuwa take gani a idonshi, na gaske ne? Ko kuma na sa ta fada cikin wani tarkon, tsaki tayi tace "banda lokacin yarda da kai, in ma dagaske kake, in ma karya kake, duk karya na dauke su, kalamanka na yaudara ne" magana takeyi kamar yana gabanta.
**
Waya General Manager ya mishi, kan cewa Mutanen nan fa ba su tafi ba, suna jiran shi Yau by 8 zaayi meeting, tsaki yayi yace "ba zai samu zuwa ba, in dole sai ya je za suyi agreeing to contract din su tafi baya so" chan kuma yayi wani tunani yace "No, kace musu i'll see them by 8" kashe waya yayi ya Kira Armstrong yace "ya mai booking two flights zuwa Bauchi. Fita yayi ya koma dakin Ziyada ya ga bata nan, ya lek'a Kitchen ya ganta tsaye tana dafa Indomie kwara daya, Murmushi yayi, yace "ki shirya za muyi tafiya yau" kallonshi tayi ta watsar, ta matsa kusa da inda ake ajiye plates ta juye Indomie dinta ta dauka yaji ta koma daki ta barshi tsaye kamar Sakarai.
Daki ta je ta zauna ta ci Indomie dinta tas, ta shiga ta kai plate, ta dawo ta kwanta kan Gado, don bacci takeji, baccin nan har bayan Laasar, Zaid ya shigo dakin don su tafi Jirgin zai tashi da karfe 5, ganinta yayi kwance kan Gado, ya dan hau ya bubbugata yace "Ziyaa, bacci kikeyi? Kinyi Laasar ma kuwa? Tashi kiyi Sallah mu tafi, yi sauri, ba musu ta tashi tashiga toilet, yana nan zaune ta fito daure da Alwalanta, ta dauko Hijab a nitse tayi laasar dinta, lazimi ta fara wanda sai da ta dau minti 10 tanayi, kuma bata da niyyar tsayawa, cewa yayi "Tashi mu tafi kar muyi missing Flight dinmu, ina kayan da kika shirya a sa a Mota?" bata tanka shi ba sai Mikewan da tayi, hawa Gadon ta sakeyi ta kwanta tare da jawo bargo, da sauri ya yaye mata bargon yace "Tashi please, in bacci zakiyi sai kiyi a hanya, tashi mu tafi" gyara kwanciyarta ta tayi ta fincike bargon ta rufe Jikinta da shi, da mamaki yace "Haba Ziyaa, na fi 20 mins in jiranki, kuma na gaya miki flight din mu is 5, yaushe mukaje Port din?" ki tashi donAllah, ya isheta da magana tace "kayi tafiarka Mallam, don ni ina nan, ba inda zani" baki ya sake yana kallonta, chan yace "Haha, tashi, nice Joke, tashi mu tafi" ta dan juyo tana kallonshi tace "Joke? Zakaga Joke" ta sake komawa ta kwanta.
Nazarinta Zaid ya tsaya yi, dagaske take ba zata ba, bayan ta sa ya jirata, kuma tace ba zata ba, aiko bata isa ba, ya mik'e ya bude drawer dinta da k'arfi, dan karamin akwati ya zaro ya shiga harhada kayanta a ciki, ta cikin bargo take kallonshi, ya fita ya ajiye Akwatin Kofar Parlo, ya kwalawa Mudi kira, da sauri Mudi ya dauki Akwatin yayi cikin Mota, komawa dakin yayi yace "Ziyaa, kar ranki ya baci, tashi mu tafi" ta murguda baki tace "sai kayi, na ce maka ba inda zani ko?" kakkabe hannunshi yayi kamar akwai datti a kai, bata ankara ba sai ji tayi ya janyota ya dagata sama ya dorata kan kafadarshi, mutsu mutsu ta fara yi tana fadin "meye haka? Put me down" cilla cilla take tayi tana wulwula kafa tana bugun shi a baya, ko a jikinshi shi dai fita yayi da ita, ko dankwali babu a kanta, haka ya tusa ta Mota ya zagaya ya shiga dayan side din ya tuka ya fita daga Gidan, Securities suka bishi a baya.
Fuskarta murtuk'e tace "wai meye haka? Ka ajiye ni, nace ba zani ba, ko dole ne? Haan naci na meye?" shi dai be ce mata uffan ba, tayi ta masifarta yayo banza da ita, da taga dai dagaske din tafiya zasuyi don sun dau hanyar Airport, tace "sai ka tsaya in dauka mayafin da zan rufe kaina, tunda kai ba kada Ilimin Addini, baka san ya kamata ba, baka da kishin Matarka, zaka bari garadan da Muharammamta suga jikinta da gashin kanta" kiii ya ci burki a gangaren titi yana kallonta, rai bace yace "Nine banda Ilimin Addini?" ko tsoro babu tace "Hakan nake nufi, Jahili ne kai a addini, in ba haka ba, ta ya zaka fito dani haka" zaiyi magana kuma ya fasa, ya bude kofa ya fita ya bude Booth inda ya sa kaya, ya dauko Akwatin gaba ki daya ya zagayo dashi daidai ita ya ajiye tare da bude, mamakin sauyin shi take, ta shiga dudduba kayan da ya zabo mata, tsaki tayi, duk ba wasu kayan mutunci, duk fitted gowns ne, chan dai ta zaro wani Mayafi ta yafa a jiki tunda kanta, ta maida kafafuwanta Mota, be ce mata komai ba ya zige zip din, dama masu tsaranshi sun fito suna tambayan lafiya, banza yayi dasu, da suka zo taimaka mishi gurin daukan Akwatin ya buga musu tsawa wai yana da hannu, da sauri suka koma motocinsu shi kuma ya rufe ya dawo ya kunna mota ya figa da karfi, Ziyada ta buga tsaki da k'arfi tace "kai dai ka sani" be tanka ta ba don ya lura ta koyi rashin kunya, be ce komai ba har suka iso Airport inda zai jirgi zai jirasu, kamar dama su ake jira, suna isa jirginsu ya tashi.
B A U C H I 6:15pm
Already su Faisal na Airport din bauchi suna Jiransu, Ziyada ta dinga murza hanayenta biyu a Saboda sanyi, Zaid ya lura da hakan, dukkansu ba me Rigar sanyi, sakalo hannunshi yayi a hannunta, kamar ta fizge kawai sai dai ta share kar ta basar da shi gaban yaranshi, ganin Motoci kusan 5 don tarban Zaid ya sa Ziyada jinjina kai, lallai kudi na inda suke, suka shiha Motar tsakiya Faisal na gaba, Faisal yace ma Zaid "Barka da zuwa Boss" a kasaitance a amsa mai, Ziyada ta bi Zaid da kallon yanda yake shan kamshi yana magana, Faisalyace "Barka da Zuwa beehive Madam" Ziyada ta murmusa tace "Ina wuni" Wannan Murmushin ya bata ran Zaid sosai, wato shine ba zata ma Murmushi ba amma ta iya ma wani? Faisal ya kalli Zaid ta mirror yaga yanda ya hade rai, sai yayi saurin fara karanto mai Updates daga jikin Tab dinshi, kafin yace "Boss, Company ko Masauki?" ya kalli Ziyada, kafin yace "mu fara zuwa Hotels din" Faisal ya kalli driver yace "Muje Zaranda Hotel".
Cikin wasu Mintuna suka iso wani Wakeken Hotel, me suna Zaranda Hotel, suka fito, Faisal ya raka su har zuwa gaban dakin da ya musu booking, wani kuma ya kwaso kayan Ziyada da Jakkar Zaid, Faisal ya bude dakin dayan kuma ya shigar musu da kaya, Ziyada ta dinga bin dakin da kallo, tunda take bata taba kwana Hotel ba, yau zata kwanan hotel, zama tayi kan kujera, Zaid ya kalleta yace "Kina jin Yunwa ai?" banza da shi tayi, yayi maganan duniya kan ta fadi me take son ci tayi banza dashi ta kyale, haka ya hakura ya bude Wardrobe ya dauka towel ya shiga toilet yayi wanka da Alwala, ya fito daure da guntun towel, da sauri ta kawar da kanta, yana karasowa dakin ta shiga toilet da sauri don dauro Alwala.
Sai da ta bata lokaci kafin don ta tabbatar ya shirya, tana fitowa taga ya kabbara Sallah, itama ta nemi Mayafi ta kabbara Sallah, sai da suka idar da Sallah ya kalleta yace "zanje Meeting, please in kina jin Yunwa, ga Waya chan ki danna 1 roomservice ki fada duk abunda kike so su kawo miki, take care of yourself please" be tsaya jin rashin kunyarta ba ya dauki bag ya rataya ya fita. Kamar jira take, yana fita ta kira roomservice tace a kawo mata Chips da liversauce" ba a wuce 15 mins ba akayi knocking aka kawo mata service dinta, tana gama ci ta chanza kaya, ta kunna TV ta fara kallo, har wurin past 10, kafin ta kashe kayan Kallon ta kwanta, ba bacci takeji ba, ta dai gaji ne, ga tsoron da bata san na meye ba.
Wurin 10:30 sai ga Zaid ya bude ya shigo da Sallama, ya kunna wuta, ganin Plate yayi alamun taci abinci, ya sauke ajiyan zuciya, ya kalli Gado, ya ga ta kwanta, a gajiye yake, a gun Meeting din sai rushing yake don ya dawo ya ganta, harda ya hakura a ka gama and it was succesful..
Kulle kofan yayi ya soma Zare kayanshi a hankali ya chanza zuwa Pyjamas, ya kashe Wuta ya dauko Laptop dinsa ya hau kan Gado, kamar jira take ya hau Gadon tayi zunbur ta tashi, da hasken Laptop dinsa yake kallonta yanda ta tsura mai ido yace "Yadai?" tace bangane ba, ya zaka hau min Gado? " da mamaki yace "to ina kike so na kwanta Kujera?" tace "ba dai dakin nan ba, ta ya zamu kwana daki daya?" Murmushi yayi yace "to ya kike so inyi?" a takaice tace "ka kama wani Dakin" ya kalleta yace "banda kudin kama wani dakin" galala tace "kaidin? Ni mallam ka fitar min a daki, ba zan kwana daki daya da kai ba, ko ka fita ko na fita" Zaid ya kalleta sosai yace "kiyi hakuri ki kwanta, barin koma kujera, ba bacci ma zan ba, zanyi wani aiki ne" cike da karfin hali tace "ni fa ba zan kwana daki daya da kai ba" ya kwantar da murya yace "kiyi hakuri, gobe sai mu raba daki, please Ziya, i dont have the strength to argue" bata tanka shi ba ta juya ta kwanta, ganin haka ya sa shi tashi ya koma kan kujera ya cigaba da latselatsenshi, Ziya ta sauke Ajiyar Zuciya, bata san ya zaayi dama ta kwana ita kadai ba, dama duk wani abu da take karfin hali ne, Thank God be fita ba, hankalinta zaifi kwanciya in ta san cewa yana dakin, bargo ta ja ba a dau lokaci ba bacci ya kwasheta.
INDIA