← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 128

Sashe 89

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba su wuce 30mins ba suka dawo, sauri sauri gudu gudu yake abubuwanshi, ya fito daga mota ya shiga gida ya dauko ruwa ya shiga dakinta, bata yi bacci ba, ya dagota ya bude mata maganin kamar yanda akayi prescribing ya sa mata a baki, ba gardama ta karba ta sha, kafin ta koma ta kwanta ointment ya kara shafa ma kafanta ya gyara mata kwanciya ya ja bargo ya rufeta, yana kallonta har bayan wani lokaci bacci ya soma daukarta.
Be san lokacin da ya kwanta gefenta, daga bisani ya rungumota yana jin dadin kasancewar su haka, da wuya a ga Zaid na bacci, baya baccin da ya wuce 2hrs, and his very sensitive, duk yanda yake bacci ko yayane ya ji motsi ko ba na mutum ba sai ya farka, amma be san lokacin da ya fara bacci ba yanzu, be so wani dalili ya rabasu.

Da k'arfe 5 da wani abu Zaid ya farka sakamon jin Ziyada na zufa, ya taba jikinta, yaga zufa takeyi alamun Fever din ya sauka, dadi ya ziyarce shi, ya dan zame jikinshi kadan, a hankali ya cire mata Sweater, tare da goge mata zufan jikinta, be damu ba, da hannu ya goge mata, ya kunna AC kadan. Fita yayi ya wuce daki, lokacin Asuba yayi haka yayi alwala yayi Sallah, abun mamaki nan inda yayi sallahn ya buge da bacci kamar an bashi maganin bacci.

Da Yunwa ta tashi, rabonta da Abinci tun kalacin safe, gari ya waye, Subhanallah batayi Asuba ba, jin jikinta tayi garau sai dai yunwa, she was sick yesterday, amma yau jinta take kamar ba ita bace ke kwance jiya magashiyan, da sauri ta shiga toilet tayi Alwala, Sallah ta fito tayi tana gode ma Allah da ya kara mata da lafiya, Toilet ta sake fadawa tayo wanka ta fito ta chanza kaya, bari ta gyara Gado kafin ta fita neman abunda zataci, tana daga Bargo taga Sweater me laushin gaske, Haba! Tun da ta tashi takejin kamshin Zaid, a hankali abubuwan da suka faru jiya suka soma dawo mata, ta tuna yanda yake mata magana da damuwa kwance a muryarshi, anya kuwa? Ko duk hakan na cikin shirin da yake mata, kai, ba zata yarda dashi ba, inaa, gyara dakin tayi ta chanza bedsheet, ta linke bargo, ta fita ta wuce kitchen.

Komai akwai a kitchen, tayi mamakin yanda komai na kitchen din ke karuwa, store ta nufa tana kallo, me zata ci? Me zatayi? Ita ba wai girkin ke mata wuya ba, me zata dafa ne ke bata wuya, guntun tsaki tayi ta dibo Dankalin da be wuce 15 ba amma irin manyan nan ne, ta fita kitchen dashi, daidai sink ta tsaya ta dauko peeler, ta shiga ferewa, bata dau lokaci ba ta gama, kamar cubes ta shiga datsawa, a haka ta soya Dankalin, ta fasa kwai ta soya, ta hada ruwan zafi tayi Tea.
Buruntu ya sashi fitowa ds sauri yayi Kitchen, tsaye ya ganta tana hada breakfast dinta kan tray, wani Murmushin da be san daga ina ba ya subuce mai, kallonshi tayi so daya ta kawar da kai, ta gabanshi ta raba ta wuce fuskarta ba wata Annuri, Tofa! Bayan ta ya bi, ko har yanzu bata jin dadi ne? Amma she looks perfectly Ok, ta warke da bata zo Kitchen ba, da sauri ya bita daki, tana zaune Kan Gado tana cin Dankalinta da Kwai cikin kwanciyar hankali, daga nesa ya hango dankalin nan, don kwadayi na kwadayi, a halin yanzu be taba gannin abunda yake son ci ba kamar abunda Zuzu keci, a hankali ya karaso gunta, a hankali yace "Ziya, Ya jikin? Ina fatan kin samu sauki?" banza ta ba ajiyarshi ta cigaba da cin dankalinta kamar ba ayi wani halitta a gun ba, be hakura ba ya sake cewa "Ina fatan ba abunda ke miki ciwo?".

Ya dan murmusa a ranshi yace "tana fushi ne, haha tana so na, zan ga inda fushin zai karashe" cikin kashe murya, da ya san zai narkar mata da zuciya yace "Haba My Forever, dont you want to talk to your Forever?" tsaki ta buga sosai da sai da yaji tsakin a tsakiyar kanshi, shi ake ma Tsaki yau? Banda ita, wa ya isa ya mai tsaki ya barshi, lallai Ziyada ta ciri tuta, tsugunna yayi gabanta, ya dauki fork din da ta aje ta dauki cup din shayinta har ya sa fork din ya dangwalo dankali da shi ya ga tayi saurin ajiye cup din shayin ta yi saurin kwacewa daga hannunshi, har ta dan bashi tsoro yanda ya ga ta zabura, shima da sauri ya mike yace "Yadai?" Kamar jira take tace "Poison, ko Asiri kana so ka mutu da wuri ne? Ko kana so na mallakeka ne? Da hankalinka zakaci abincin da akayi Asiri don mallakeka? Haba mana, kar ka zama wani mara wayau mana".

Sosai da mamaki yake kallonta, duk ta chanza, ta rikide ta koma wata da be sani ba, ya san cewa tabbas magana ta gaya mai, yanda kasan Me Ciki haka yake jin kanshi, so yake yaci dankalinta, wani abu ke ingiza shi, dan kawar da kai yayi, besan meyasa yake jin shi wani dolodolo gabanta ba, share maganar da tayi yayi yace "Ziya, bani inci please, nima Yunwa nakeji, kuma shine zaki dafa ke kadai, kuma kinsan cewa ba ke kadai ke cikin gidan nan ba?" ya karashe cikin karyar da murya, da karfi tace "Heheh, Ni in dafa ma Abinci? You are sick in the head, lokacin dana so kaci abinci na ya wuce, ni banson Almubuzaranci, amma da na baka abinci na, gwara na zubdashi a kasa na taka".

Ranshi ya fara baci yace "Ki bani ko ranki ya baci, this is my House" ta danyi guntun dariya tace "bacin rai? Na nawa kuma sai dai kar a kuma, and this is your House but this is my room, baka isa ka sani abun da ban yi niyya ba, banda lokacinka, a lokacin da ka barar min da ruwan zafi a kafa, a lokacin duk wani k'ima, mutunci, daraja da wata So ya bare tare da ruwan zafin and Abu na karshe, ina so ka sani raina ya gama baci ta kanka" ranshi bace da mamakinta be so ya yarda da abunda tace, be so ya sake jin wani abu daga bakinta, don me zatace tabar son shi? Ya zaayi ta bar sonshi? The whole Him, for God sake he's Zaid Freaking Sadam Audu, ba ta san yanda mata ke mutuwan mai ba? Matan da sun fita da komai, sai yaji kamar ta ci mai fuska, kamar dan shekara 4ya mareshi zai iya daukan rejection dinnan ba.

Da karfi yace "Shuttup, kar ki sa na miki abunda ba zakiji dadinshi ba" dariar da ya tsana tayi tace "bana tsoronka, bana shakkanka, thanks to you ni ba mafadaciya bace, ka koya min fada, ni ba mara kunya bace, ka koya min rashin kunya, so mu zuba ni da kai, duk wanda ya gaji yayi sanadiyar dayan, ko gawa ta ko taka, ko ka barmin Gidan, ko ni na bar ma Gidan, don na tsaneka wallahi, i hate you Zaid, nayi nadaman saninka, kaci amanar Soyayya, kaci amanata kuma ban yafe ba" abun mamaki juyawa yayi ya fita daga dakin a guje kamar dan Yaro.
A zaton ta wani abu yaje daukowa don ya bugeta, amma taga shiru, haka ta zauna ta cigaba da cin abincinta ta fita ta kai kayan kitchen, zuciyarta bushe, ba a haifi wanda zai wulakanta Family dinta ta raga mishi ba, So kadai zai hanata gurza mai rashin mutunci, amma yanzu ta sa Martaban Family dinta a gaba, ta zabi hakan akan Farincikinta, ba zata sake bari Zaid ya wulakanta ta ba ko Family dinta, ba za ta fita ba ba kuma zaa zo gunta ba ko? Ba wani abu, muje zuwa" har tayi hanyar daki, kuma ta fasa ta koma Parlo ta zauna ta kunna Zeeworld ta hau kallo ba tare da ta damu ba.
Bayan Wasu Awannni.

Daki ta shiga domin yin Sallahn Azahar, tana cikin yi sai ta ji shigowarshi, sai da ta idar ta dade tana Addua, da ya ga bata da niyyar shafawa sai ya dauko Magungunan jiya ya matso kusa da ita yayi tsugunni a gabanta, ballowa yayi ya kai bakinta, ta kawar da kai, ya sake kai mata, ta sake kawar da kai, ya dai daure yace "kisha magani please" a dan tsiwace tace " ba zan sha ba", ranshi ya baci sosai, Masifa ya fara mata "Ke Mallama, ki kama kanki kinaji ko, kinga ina lallaba ki zaki fara kawo min raini? Toh ki kiyayi kanki, ki cece mu daga bacin rai dukkanmu, ke ke ciwo amma na fiki damuwa, jiya baki san wanda ke kanki ba, an samu kin fara jin sauki kuma zaki fara wani iskancin banza kice ba zaki sha magani ba, har kin isa ki sa na fita k'arfe dayan dare don siyo miki magani kuma ki k'i sha? Wallahi baki isa ba, ki karbi maganin nan ki sha kar na saba miki" jiki na rawa, dama wasa guri gareshi, da sauri ta karba ta sha ta karashe da murguda mai baki, Kyau ya ga ta mai, be san Murmushi yake ba, ita kuma tayi kicinkicin da fuska. K'afarta ya jawo ya sa a jikinshi, tana kallo ya matsa wani mai me kama da vaseline a hannunshi, ya shiga shafa mata sama sama don kunar ya fara bushewa, ya dago kai ya kalleta, yace "Ki daina sawa ina miki Masifa, ki dinga yin abunda nake so kinji" bata ce mai k'ala ba ila kawar da kanta da tayi, be damu ba ya tashi ya fita ba tare da ya damu da shariyar da take mishi ba.
Chapter 89 · 0% Book details