← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 128

Sashe 53

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Majeed da Ziyada, shi Majeed din ne ya taimakeni" Paapa tace "you need to be very careful, zamuyi processing yanda za mu turo miki kudin jirgi ki dawo India, you've been away for long, we cant handle it". Baki na rawa Najwa tace "Paapa Ya Zaid din fa? Ban ma fara fita nemanshi ba fa, Paapa ku dan karamin lokaci, i need to find my brother, haba nasha wahalan da ba zan bari wahalan ya tafi a banza ba ba tare da na hadu da Brother dina ba" Maama tayi karaf tace "wahala Najwa? Wace iri? Me ya faru dake? Are you Alright?" ta katseta da sauri "Maama stop overreacting, bansha wahala ba fa, kawai i mean i cant stop now after all that has happened, ina ji a raina na kusa ganin Yayana, in nace zan dawo yanzu ai komai ya tashi for Nothing, afterall thats why i'm in Nigeria, to find my brother, i cant stop, atleast not now, Maama kuyi hak'uri ku k'ara hakuri,ku tayani da addua ba zan dawo India ba sai da Yayana, i dont know how, but a raina ina ji i'll see him soon, this my Number, zamu dinga magana time to time, and yes I need that money, ku tura mun kunji, I love you so very much, Maama Paapa, i miss you" ba ta bari sunyi magana ba ta katse wayar. Dadi ya rufeta, sai taji kamar an sauke mata nauyin shekara da shekaru, tayi magana da Mahaifanta, farincikinta suna lafiya, ba abunda ya samesu, yanzu zata jira su tura mata kudi, ta fara binciko Yayanta, ta koma k'asarsu, su zauna as one big happy Family, ta share hawayenta, tana juyawa wa zata gani? Majeed ne tsaye da hanayenshi biyu rungume a k'irjinshi, da alamu duk maganar da ta gamayi a waya da da mahaifanta akan kunnuwanshi, a ranshi yace "ta min k'arya, tazo Nigeria neman Yayanta ne, meyasa zata min k'arya? Bata yarda dani bane?" Iyakar rudu Najwa ta shiga tuni jikinta ya fara rawa, bude baki tayi zata mai magana ya daga mata hannu alamun ta dakata, jiki ba walwala yace;.. 掳掳掳掳掳 Bibilicious freaking fans, ya kuke, ya jirana? Lol, i've missed you sosai, hakurin zan cigaba dai da baku, wannan page din bezo muku kamar yanda kuke tsamanni ba, amma kar ku manta sannusannu bata hana zuwa, next page abunda kuke tsammani zai faru,kun sani ai? ko sai na fada? Ok Haduwan Zaid da Abba Abu's family. Ya zaa kare a Kotu tsakanin Mairo the Dragon (lol) and Family din Nakowa? Wa zaici nasara a tsakaninsu? Guess Wai shin Me Zaid ke Planning? Makeup artiste? Seriously? Me zaiyi da makeup artiste? Any guesses? Ehen meyace Na'eelah ta mai? And Majeed? Ya fara son Najwa, amma ya gano Makaryaciya ce, shin zai sake yarda da ita kuwa? Zata kare kanta? Ko kuma wani karyan zata shirga mai? Heheheh Nextpage will come soonest, i promise, just bear with me please Vote, Comment and Share. #1love #ADAY #bibiliciousfreakingfans #anatare #nagode 馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱 NA BIEBEE ISA 庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Wattpad:@biebeeisa Pg2鈨�4鈨� Daga hannunshi yayi alamun ta dakata, bude baki ta sake yi da niyyan yin magana ya katseta ta hanyar cewa " shhh PureHeart, kar kice komai" idanun ta ta kyafta so biyu a kasalance tace "Yes i lied to you, na maka k'arya, kayi hak'uri, zan gaya maka" girgiza kai yayi yace "Kowa na son Privacy, i respect Privacy alot,musanman Family Issue, so kar ki damu, ba sai kin gaya min ba I understand" ya juya bayan ya sakar mata murmushi me sanyi. Har ya fara tafiya, ta girgiza kai ta bi bayanshi tare da cewa "Nazo neman Yayana ne, tunda nake ban taba ganinshi ba" chak Majeed ya tsaya kafin ya juyo, cikin yanayin da ya fi kama da rashin yarda yace "What?" a hankali ta tako har gaban shi ta cigaba; "Asalin Parents dina 'yan Nigeria ne, Unknown reason ya sa su komawa India, kafin tafiyarsu, sun bar Yayana da yake Makaranta, kuma they couldnt come back for him, so an haifeni a India, na girma a India" Majeed cikin rashin fahimtar abunda take cewa yace "Bangane ba PureHeart, me kike cewa?". "Iya Sani na, Mahaifana na son zuwa Nigeria neman Yayana Zaid, sun rabu dashi yana da shekara 11, a duk lokacin da sukayi shirin zuwa Nigeria, wani Badluck zai faru dasu, har su kasa zuwa, A kullum Maama na cikin Kuka, muna da komai amma rashin Danuwana na sata cikin damuwa, farincikinta ragagge ne saboda rashin shi" Majeed yayi shiru yana nazarin maganganunta kafin yace "Me kike nufi da ba zasu iya zuwa Nigeria ba?" dogon numfashi Najwa taja kafin ta sake tace "its kinda complicated, but you see tun bayan barin su Nigeria, they cant remember anything about Nigeria, they dont even remember the State they are from, all they could ever remember is that they are Nigerians, and they left their Son in some Boarding house(abun na da dan mamaki, tun barin su Nigeria, suka mance komai, ba sa iya tuna komai, ko garin da suke sun manta, su dai sun san yan Nigeria ne su, kuma sun bar Dansu a Makarantar Kwana). Kan Majeed yayi nauyi da Zafi a hankali ya furta "Sihiri" da sauri Najwa tace "Exactly, haka Aisha ta fada min, maybe someone is jealous of them or something" Majeed yace "it can be anything" Najwa ta gyada kai da ta lura ya fahimceta "An haifeni na tashi a India" "how comes kika iya Hausa?" tayi murmushi tace "Well na tashi naga su Maama na hausa, a gida is hardly muyi Indianci ko Turanci" Majeed ya Murmusa yace "basu manta aladarsu ba". Murmushi tayi sannan ta dan chanza fuska tace "tunda na fara Wayau nake ganin Hawayen Maama na ta dalilin Rashin Danuwana, Alwashi na dauka, sai nazo Nigeria, sai na share mata hawaye, sai na nemo Yayana, ba don na san ta inda zan fara nemanshi ba, bansan inda zan dosa ba wurin nemanshi, k'udiri daya ne a raina, zan nemoshi, zan ganshi, sai dai in baya raye,no matter what da izinin Allah" ta share hawayen da ta fara kafin ta cigaba sa magana "i'm sorry na maka k'arya, i just dont know who to trust, my first Day in Nigeria was a Terrible Experience, kai shaida ne, ina tsoron kar wani yayi amfani da bansan kowa ba ya min mugun abu, maybe saboda ni bak'uwa ce or something, but ka yarda dani, nayi niyyan gaya ma gaskia, yanzu ina iya cewa, bayan Paapa da Maama, you are the one i trust the Most". Yayi murmushi mai nuna jin dadi sosai ga maganar ta ta k'arshe yace "na fahimce ki fully PureHeart, farkon haduwan mu naga wautarki, har yanzu ina ganin wautarki, you are so Innocent and Naive, some may call it Stupidity, da hausa muna ce mai 'sokonci', literally zan iya ce miki ke Sokuwa ce, i mean wanene cikin hankalinshi zai dauki Waya ya ba wanda be taba gani ba? Wa zai yarda ya ba wani Akwatinshi da ke da muhimman abubuwa ya tafi dashi da sunan zai kai Mota? Eye?" sukayi daria gabaki daya, ya cigaba "so until you find your Brother, ni zan zama Yayanki, kuma zan kula dake, kuma zan kareki da Iyawata, and zan taimakeki da iyawata, kuma da yardan Allah zan sada ki da Iyayenki, kuma zan tayaki neman Yayanki, kuma zan kalleshi cikin idanu, in tayashi murnan kasancewarki kanwanshi, kuma zan bashi hakurin rashin kasancewarku tare don ba zaku kasance tare yanda ya kamata ba, saboda ni zan daukeki in kai ki Gidana".. Hannu ta sa ta rufe fuskarta, yace "PureHeart dago ki kalleni" a hankali ta dago yace "ina ce yanzu ba 'yar Ghana bace wanda za a ma auren dole?" tayi dariya ta girgiza kai, yace "Ok now lets Find your Brother, da sauri sauri, don shi zai ban Aurenki, whats his name again?" dariya tayi tace" ZAID, ZAID SADA" a ranshi ya Maimaita sunan, a fili kuwa yayi Murmushi yace "OK, lets find Zaid Sada" tayi dariya tace "How?" ya kashe mata ido daya yace "dagaske ban sani ba, amma mu je zuwa" yayi gaba ta bishi a baya, tana jin Majeed har ranta. LAGOS Sun kawo decision, wannan ne karonsu na k'arshe, well maybe, ya gama karance ma Na'eelah Plan dinshi, ta amince zata bishi kano har tsawon kwanakin da yake so ta zauna. Sai da suka fara zuwa Lagos, inda Zaid zai hadu da Rita Phillips, rannan Appointment dinshi ya shiga Office dinta, Rita ta ji dadi Matuka, irin the whole Mighty Zaid Sadam Audu in her Office? Thats an honor, Zaid ya karanta mata irin makeup din da yakeso, ta jinjina kai ta shaida mai makeup din 8hours ne, sai an dauka awa takwas ana yi, ya dan bata fuska, be son zama, amma in zaman zai sa shi cimma burinshi to zaiyi hakan, so tace yaushe zaa fara makeup din? Yace "zai kirata, but in zaayi makeup din, sai tazo Kano kuma maybe a rana daya zaayi makeup din so biyu, it depends dai, kuma yana da bukatan duk lokacin da yake son makeup din s kasance tana garin Kano, be damu ba in zata kashe Appointments dinta, kawai ta hau Jirgi tazo Kano, or maybe zai dauketa ne hire har sai ta gama mishi aiki, so ya bata umurnin yin Calculations gabaki daya, har da su kudin Accomodation, kusan mint 10 tana Calculating, a dan tsorace ta kalleshi tace "4.3 million". Zaid ya mik'e tsaye yace "Rita Phillips, I'll see you in Kano" ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba. Ta bishi da ido, to me hakan ke nufi? Ya amince zai biya ko be amince ba? To yace he'll see her in Kano, yana nufin sai tazo mai makeup din kenan? God he's too bossy". K A N O "Aliyu A A yan fashi suka kama shi a hanyar shi na zuwa Wudil" cewar Majeed da ke sanar da su Mummy, Mummy tayi zumbur tace "Kai Subhanallah, ince dai ba su mai mugun abu ba ko?" Majeed ya dan daga kafadu yace "abun mamaki ko sata basu mishi ba, kawai dai wai sun karbi wayanshi ne sun
Chapter 53 · 0% Book details