Sashe 97
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sosai ya hau kan Gadon, Gabanta ya hau dukkan ukuuku, a bayanta ya kwanta tare da juyo da ita tana fuskantarshi, a kunnenta ya mata rada "Ni Mijinki ne, be kamata ki juya min baya ba kinji?" a hankali ta gyada kai alamun taji, kare matseta yayi yana binta da wasu kauna a jiki, ganin yanda yake matsowa jikinta ne ya sa ta daburcewa jiki na rawa tace "Zanje Makaranta" Murmushi yayi don ya san ta tsorata dashi ne yace "Yanzu zaki makaranta?" da sauri ta gyada kai tace "Gobe" a takaice yace "na cireki" za tayi magana yace "Makarantarki zaki Koma, baze ko? Chan zaki cigaba da karatunki bata iya amsa shi ba, ta mayar da idanunta ta rufe.
A nutse yake nuna mata yanda yake jinta a zuciyarshi, cikin kwanciyar hankali yake nuna mata yanda soyayyarta tai mishi illa batare dayai amfani da kalamai ba. Cikin kwanciyar hankali yake hade zuciyoyinsu da ruhinsu waje daya cikin salon da bazai mantu a wajen su ba har abada.
***
*Bayan Wasu yan Kwanakin da ba su kai Sati ba*
Soyayya, Aminci da Shakuwa ta darsu a cikin zuciyoyin masoyan nan biyu, burin daya ya kyautata ma daya, a zaman da sukayi da juna sun fahimci halaiyar junansu, sun sake da junansu, sabida Kwanciyar hankali Zaid ya kashe wayoyinsa don samun hutu, shi fita kasashe bude ido be dameshi ba, niyyarshi ya dauketa su tafi chan Porthacourt su danyi hutu ba tare da hayaniya ba, a yanzu ne Zaid yasan cewa ya dade yana cikin bakin duhu, a yanzu ya san cewa akwai wani abu So, a yanzu ya san cewa mutum na zama da tsana da bakinciki a ranshi in yaso, in ko ya so cirewa zai cire ya musanya da So, Allah ne shaidarshi yana son Ziyada, yana son kyautata mata kamar yanda take kyuatata mishi, shiyasa jiya da daddare da ta zo mai da bukatar suje Gidansu be ce komai ba, amma duk da baya so, ba zai hana ba, dole ya hakura suje Gidan, wurin breakfast ya gaya mata ta shirya anjima su tafi, dadi ya kamata, ta tashi ta rungimeshi tana mai godia breakfast din da basu gama ba kenan.
**
Aunty Aynarh ta shigo Gidan da Sallama, duk yaran su ka tashi suka rungumeta, fara'a take tayi, ta zube kasa ta gaida Hajjo, Daddy baki har wuya yaga Masoyiya, a mutunce aka gaisa, Mummy sai famar wurga mata harara take ko a jikinta, ta kalle su tace "Allah ya sa ba ku daura abincin Rana ba, na riga na mana Lunch" Zaineema ta murmusa tace "ba mu daura ba ko" tace "yauwa perfect" Key ta mik'a ma Abdulmajeed tace "Ka dauko Kayan Booth" Abdulmajeed ya karba ya kalli Najwa yace "muje ki tayani dauko kaya" tashi tayi ta bi bayanshi suka bar Parlorn, Mummy ta kalli Daddy tace "bari in daura mana Abinci kafin yara su fara jin yunwa" Daddy yace "Maryam bakiji Hajia Aynarh tace ta yo abinci damu ba?" Galala ta kalleshi, kwana biyun nan tsinkata yakeyi gaban jamaa, kar ya mata haka yanzu ta wayance tace"wai sai a kara ko?" Daddy yace "Aa, am sure Abincin da yawa, ki bari da daddare ayi, yanzu dai muci wannan" zama tayi tana wurgar Hajia Aynarh da harara, ita ko hararar mugunta take mata.
"PureHeart, i cant wait naga su Maama don nace su bani ke na aura" Murmushi tayi tace "suna nan tafe cikin kwanaki" yace "Allah ne shaidana, ina sonki dominsa" Murmushi tayi tace "main tumase karta hoon" idonshi ya juya sama cikin salon banji me kikace ba, tayi daria tayi gaba, ya bi bayanta yace "Nidai a bar min magana da Indiyanci" dariya tayi tace "Aunty Aynarh na jira" ya bude Booth ya fiddo kayan ciki duka har su carpet, plates da cups, sai Flask kusan kala uku, suka dau iyakan iyawansu suka kai ciki, suka dawo suka dauka sauran.
Carpet din suka shimfida a tsakar Gidan, suka jera komai a kai, sai da sukayi Sallahr Azahar suka fito waje kan Carpet din, daidai nan Ziyada ta shigo Gidan da Sallama, duk sukayi kanta suka yayyabeta suna murnan ganinta, Oyoyo Oyoyo, daga baya Zaid ya shigo, baki Mairo ta washe, shi kuwa kamar an aiko mai da Sakon mutuwa, faraar fusakrshi ya dauke dif, Abdulmajeed a karaso gunshi ya mika mai hannu don suyi musabaha, ba yabo ba fallasa ya karba, tare da dan durkusawa ya gaida da Daddy da Hajjo da Aunty Aynarh da ke zaune kan Carpet, duk ya bi yaran gidan da kallo inda suke gaisheshi, tausayinsu ya kamashi, Zaineema yarinyar da yaso kamar me, be manta kaunar da ke tsakaninsu ba, yarinyan da Mairo ke rankwashinshi in ya dauketa, rashin imaninshi ya sa ya rabata da Mijinta, ya zaiyi ya gyara mistake dinnan? Idonshi ya kaiga Najwa wanda take wurga mishi wani mugun kallon "na san ko waye kai" da sauri ya dauke kai yana me jin tsoronta, kar fa ta ganeshi, kar ta tona mai asiri Ziyada a rabu dashi, Allah sa bata ganeshi ba, ji muryar Mairo yayi tana cewa "Ku shigo Parlo sannunku da zuwa" Ziyada tace "Aa Mummy, bari mu zauna a nan so kike ayi picnic din banda mu?" Mairo ta tabe baki tace "ba wani picnic, dangin yarbawa ce tayi son iyawanta wai ta dafo mana Abinci, kamar munce ba mu da abinci". Ziyada tace "Yayy, dama nayi missing Abincin Aunty Aynarh" Mairo takaici kamar ya shideta, tace "Alhaji Zaid kai ka shigo Parlo ka zauna" banza yayi da ita, ba wanda ya lura da ko gaishe da Mairo beyi ba, ya samu wuri kusa da AbdulMajeed ya zauna, wanda Hajjo ke gefenshi Najwa na nata gefen, Mairo tace "Lah, Alhaji, zaman kasa be kamace ka na, please ka shigo ciki" ko kallo bata isheshi ba, Daddy yace "Maryam ki barshi ya zauna cikin Yanuwanshi mana"
"'Yanuwanshi" kalmar da Zaid ya fada kenan, ya kalli gefen shi ya ga su Hajjo da Muhsin da Zaineema zaune, dayan gefen Daddy da AbdulMajeed da Zinatu da Ziyada a zaune, sai ya ji shi kamar daya daga cikinsu, ba abunda ya kai bond din Yanuwan jini karfi, ba abunda ya kai feeling din dadi, tabbas yaji wannan connection din, ya ji shi among them, ko yaki ko ya so "they are his Family" yayi Alkawarin gyara laifinshi, "I will fix this , i will fix everything " ya fada a ranshi..
Daddy yace "Oya a bamu mu ci" Hajia Aynarh tace "ai ga yara na nan, su zuba mana" Mairo kamar ta mutu ganin yanda Hajia Aynarh ke fi'ili gaban Daddy.
Zaineema ta bude kulolin, Faten Wake da Amala, duk wanda kake so sai a sa maka, Miyar Amalan yaji Ganda da Stock fish, Alallen kuwa ya hadu da kwai da kifin Sardine, Faten waken ma yaji dryfish da Ganda.
Tace "Daddy me zaa sa maka? Hajjo me zaki ci?" tace "a zubo min Faten Wake, mun dade bamu hadu ba" akayi daria, Daddy yace "a zuba min Amala" Mummy fa baki ta yatsina tace "Moimoi".
Ziyada tace "YaMaji me zakici?" ya tashi daga durkuson da yayi yace "Zuzu serve your Husband, ni da kaina zan zuba abinci na" Hajia Aynarh tace "banda abunki Ziyada ana ta Miji wake ta wani YaMaji".
Ta k'asa ta kalli Zaid din da yayi mugun dauke kai, yana iya cin Abincin Musamman da yaji cewa ba Mairo tayi shi ba, Hajia Aynarh tayi, kuma yana iya cin Amala, don yana son abincin, ita kuma bata yi zaton zaici ba shisa bata tambayeshi ba, a hankali suka hada ido yace mata "Amala" Ziyada ta murmusa, Najwa tace ita kuma a bata irin na Hajjo ba wai don ta san meye ba, amma don yayi kama da wani soup din India, kowa ya fadi abunda zaici akayi serving kowa..