Sashe 45
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
kaza" haushi kamar ya kashe Mummy, kowa na ta cin Abinci, banda Najwa da take ta juya cokali, ta zurfafa a nata tunanin, Maama, Paapa, tare suke cin Abinci, kewansu ta ke ji, ko wani hali suke ciki? Majeed na lura da ita yace "yadai Najwa? Ko in dafa miki Indomie?" Duk suka kalleshi da mamako, barin ma Nana da take ji kamar ta makureshi. Najwa ta Murmursa tace "Aa, ina iya ci" yace "Oya Eat, in ba za ki iya ci ba a dafa maki Indomie" ta soma dauke numfashi tana hadiye tuwon nan, don bata son Warin Kifin. Najwa ta fara tashi, tace ta k'oshi, Hajjo tace "ki kara mana 'yarJikata" Najwa tace "Nakoshi" Mairo ta tabe baki, Najwa ta mike ta koma daki, hannu ta daura a kai, hawaye suka fara sunturi, magana ta fara ma kanta da k'arfi, "Najwa Sada Abu, zama ya kawo ki Nigeria? Shin kina yin Abunda ya kawoki? Kin san halin da kika bar Maama a cikin kwanakin nan? Ke baki nemi Yayanki ba, ke ba ki nemi Maama kin sanar da ita hakin da kike ciki ba, duk da zata shiga damuwa atleast call her and tell her sje shouldnt worry about you, tell her you are Ok, Najwa how can you be so Stupid?" Sai ta fashe da Kuka tace "Maama i'm so sorry, ya zanyi? I dont know who to trust, bansan ta ya zance ma Majeed ya kira min ku ba, bayan i told him a different story, me zai faru in Asiri na ya tonu? Me zai faru in ya gane k'arya nake mai tun farko, k'ila zai koreni daga gidansu, ni kuma i wont take that risk, ba zan bashi chance din sanin wacece ni ba, dole in tashi da k'afafuwana, in yi abun da ya kawoni k'asar nan". Haka ta dinga surutai ita kadai dole fa ta fara fita neman Yayanta, amma ta ina?? Da Asuba bayan sun dawo daga Masallaci, dakin Hajjo suka nufa, tana zaune kan darduma Daddy da Majeed suka shigo da Sallama, sai da ta shafa Adduar da takeyi ta amsa Sallamarsu, daga gefe suka tsugunna, Majeed ya gaishe da ita yana tambayarta "ya kwanan bak'unta?" tace "Alhamdulilah" Najwa da ke kan gado ta gaishe su, Majeed ya mik'e yace "bari ya koma daki" sukayi Sallama ya wuce, ya bar Daddy nan, Najwa ta koma bacci, Daddy da Hajjo ko suka sha firarsu har gari ya waye. ****** Da sauri Mummy ta shigo dakin su Zaineema, tana kiran "Ziyada,Ziyada" Ziyada tafi to daga toilet da sauri tace "yadai Mummy?" da fara'arta tace "Yau Dan Deputy Governor zai zo wurinki, yanzu mukayi waya da Her Excellency" Ziyada ta daure fuska tace "Mummy ni wallahi ban son haka, donAllah kice kar yazo" Hajia Mairo ta hau lallashinta kan cewa ta rufa mata Asiri, ta shirya yanzu zai zo fa" tashi kawai tayi ta shige toilet, Mummy ta kalli Zaineema da take kwance tace "Zainee please talk her out" daga Gira tayi alamun "OK". * "Ziyada meyasa kikeyin haka?" ba gwara miki Auren ba? Ni yanzu da nake zaune a nan kin san yanda nakeji? Ji nake kamar in koma Kaduna, ko Khalid zai wulakantani ba zanyi fushi ba saboda ina son Mijina, kuma Aure shine rufin Asirin Mace, ki saurareshi in yazo please, dan Deputy Governor ne fa, yanda muke shiga one problem or the other, ki ka aureshi ai mun warke, Mummy ta bar shan wahala, ke ma zaki cigaba da School dinki a Base ba sai an saki wani BUK Ko NW ba, think about it". Ziyada ta kalli yayarta ta watsar, kamar ba zatayi magana ba chan tace "Auren Jari kuke so inyi kenan,hmm, zan saurareshi ne kawai don mu fahinci juna amma in be mun ba, Allah ya sa dan Shugaban K'asa ne, ba zan aureshi ba, one thing is for sure, ba zan taba auren wanda bana so ba" ta tashi ta wuce dakinsu Hajjo". *** 3:00pm Jikin Mairo 6ari yakeyi ganin sha tara ta arzikin da ake ta shigowa da su, da kanta ta shigo da Amjad har Parlor, k'amshin shi ya kaure Parlon gabaki daya,Mairo kamar ta mai sujadda takeji, tace "barin turo maka Ziyadan ko?" yace "Okay, Mummy" Mairo ta shiga ciki, Zeenat ya yafito da hannunshi, tana karairaya ta matso, sai yaji ta burgeshi, yace "whats your name?" tace "Zinatu Abba Abu" ya dinga mata tambayoyi tana bashi amsa, ya ciro bundle din 500 yace ta siya chocholates, ta karba tace "thanks" har ta juya zata shiga ciki ta juyo ta kalleshi, tace "i hope you marry my Sister Ziyada" ya murmusa yace "I surely will" ta sa kai ta wuce ciki. Fama take tayi da Ziyada kan ta fita su gaisa, ta k'i, Mummy bata da wani choice da ya wuce ta rok'i Hajjo ta roketa ta fita, tace "Hajjo, kice mata taje bakonta na jiranta, ba dadi a barshi, gashi dan babban gida, be saba jira ba" Hajjo tace "yau ga tsiyan banza, ina aka ta6a gudun masoyi? Maza ki tashi ki tafi ko in sa6a miki, haka akeyi?" Chan kuma sai ta hau lallashinta tace "So kike naje na miki sinacin(snatching)? Ina laifin wanda yace yana sonka? Gaisuwa ne, ba zai rage miki komai ba" ta turo baki tace "Mummy kin gaya ma YaMaji?" Mairo tayi karya tace "ai abokinshi ne, shi ma ya mai kwatancen gidan" Ziyada ta mike ta ja hannun Najwa wai ta rakata, Mairo ta galla ma Najwa harara, nan da nan Najwa ta zame hannu, tace "kije kawai" Ziyada ko tace "in ba da Najwa ba itama ba zata ba" Hajjo tace "tashi ki rakata Najwa, ba don son ran Mairo ba ta bar Najwa ta rakata, suna fita ta bi bayansu, tace " ke Najwa zo ki kawo mishi abun motsa baki, Najwa tace "Ok Mummy, jeki Ziyada, yanzu zan zo" Ziyada tayi gaba, Mummy ta tasa k'eyar Najwa suka wuce kitchen. **** Tayi Sallama kanta a k'asa, ya mik'e tsaye "Sweetheart sannu da zuwa" Ziyada ta dago kai ta kalleshi, mayataccen kallon da yake binta dashine bataso, wuri ta samu ta zauna, cikiciki tace "ina wuni" cikin doki yace "lafiya lau beautiful" ya sauko k'asa kamar me neman gafara, yayi yayi ta dago kai ta k'i, yace "ina Mummy, Mummy kinga ta ki dagowa in ganta da kyau, Alright, Fine, Sunana Amjad" Ziyada da dai ko ci kanka ba ta ce mai ba, yayi yayi tayi magana ta yi shiru, haka yayi tagumi ya tsura mata ido. **** Nana ta fito tana karairaya, "Brother Inlaw, sannu da zuwa" da faraa suka gaisa, ta gabatar da kanta a matsayin matar Majeed Yayan Ziyada, suka gaisa tace "to brother inlaw, na barka lafiya, ni na fita, sai mun sake haduwa a Sha Soyayya lafiya" yayi dariya, tare da daga mata hannu. Takaici kamar ya kashe Ziyada, Nana batayi ba ko kadan, haka Mummy da Zaineema suka shigo suka Gaisa, Mummy tace "kaci Dambun naman please, feel at home" murmushi kawai yayi, Mummy ta ma Ziyada ido alamun ta kula shi, Ziyada ta dauke ido, haka Amjad ya cigaba da surutanshi amma a banza. Add Najwa ta shigo da Sallama dauke da tray cike da kayan mak'ulashe, ta durk'usa ta gaida Amjad, ya amsa da faraa, yace "ya sunanki?" tace "Najwa" "Nice name, are you her sister?" Najwa tayi saurin kallon Ziyada tace "uhm, erhm, eh" yace "Najwa Ziyadatu bata magana ne? Ta k'i min magana, ki gaya mata tana wahalar dani, please" Najwa ta murmusa kawai ta kama gabanta don Mummy ta gargade ta, da da ta kaimai ta juyo". Haka ya cigaba da yi mata fira ba tare da ya damu da ta tanka ba ko ba ta tanka ba, yana ta bata labarin France inda yayi karatu, sai kuma Maganar Mommy dinsa. Amjad fari ne k'yak'yawa sai dai siriri ne sosai, duk kyanshi Ziyada bataji ya burgeta ba ko dis, ita bata son Namiji haka, he's nosy, kuma ta lura dashi dan Mommy ne, abu kadan zaice Mommynshi kaza, haba! Surutunshi ya cika mata kunne, Gode ma Allah tayi don taji wayar shi yayi k'ara Alamun kira ya shigo, tana jinshi yace "1minute Sweetheart let me answer this call" Shiru tayi bata amsa mai ba. PORTHACOURT NG Gyara tsayuwarshi yayi tare da kara Waya ya a kunnenshi yana murmushin Mugunta "Hello, Amjad Sahabi" yana jin muryanshi a k'agauce yace "Yes who is this?" Zaid ya sake murmusawa yace "This is Zaid Sadam Audu" da murna yace "OMG!! ZSA kaine?" a tak'aice yace "yeah!" Amjad yace "Wow, its been long, tun France, how have you been" Zaid da ya soma k'ulluwa da surutan Amjad, ya sanshi talkative ne, to shi ba wannan ya kira shi ya ji ba, ya dai daure yace "Amjad, kaje Zance Gidan Abba Abu gurin Ziyada Right?" Amjad ya kalli Ziyadan da ke wasa da yatsunta, yace "yeah, ya akayi kasani?" Zaid yace "lol, ya ba zan santa ba, Aurenta kake sonyi? Amjad are you out of your senses? Kasan bansan shiga harkan mutane, amma da naji kaine kake nemanta shiyasa nace zan gaya ma, duk da we werent on good terms back then, but ba zan ga abunda zai cutar da kai in dauke ido ba" Amjad ya dan fara tsorata yace "Zaid, ban gane ba" Zaid yace "ka binciki Khalid Maikudi a garin Kaduna, he was Zaineema's Ex Husband, na san ka ga Zaineema s a gidan, Khalid ya saketa ne saboda ya kamata da Kwarto a dakin aurensu, and Matar Majeed Nana, God that girl is terrible, wannan karya ce, muguwar 'yar slow ce, shes a wh*re, muguwar 'yariska ce, in ba ka yarda ba, na maka sending pictures dinta ta Whatsapp, and then Ziyada, da tana karatu a Base University, da aka gano tayi ciki shine suka neman mata transcript suka cireta a Makarantar, Suka barar da cikin a Ikhwaan Clinic, if you are in doubt kaje ka bincika Clinic din, da kake ganin Ziyada kamar Saliha, ai ta fisu iskanci, don ta dame su ta shanye, Hajia Mairo kuma, ka bincika kaji halayarta ko gurin Mom dinka, ka tambayeta halaiyarta da suna School, Amjad listen and listen good, Alhaji Abba Abu ya samu karayen Arziki, ba