← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 128

Sashe 64

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana jin haushita, wai ta ya zai fara auren yarinyar nan? Ya fa lura dagaske take, mts, kawai bari ya sa su Amstrong su mata fyade, nan da nan Zuciyarshi tayi mai gardama, ba zai bari hakan ya faru ba, to ko meyasa? Be son dogon tunani zuciyarshi ta sake mai wani tunanin, ko dai ya aureta din yayi making life dinta miserable, daga baya sai ya saketa ya wulakanta ta, yace "Wallahi kaman kin san a matse nake nima, please kiyi saurin gaya mishi, zan turo magabata na, nan ya cigaba da gaya mata kalan son da yake mata" ita kuma tayi ta shiga yanayin Masoya. Kalaman da ya mata amfani dasu yau sun matuk'ar Girgiza mata Zuciya, a ranta takeji, ba ta da Miji sai ZSA dinta, har tana ji in bata aureshi nan da nan ba, wani mummunan abu zai samu zuciyarta, tana Jin kunyan YaMaji, amma dole shi zata samu ta sanar mawa, tunda Zaid yace "ta gabatar da shi. Dakin Mummy ya shiga ya daga katifa ya ajiye package din Cocaine din a karkashin Gadon, murmushin mugunta yayi, yace " dole kiyi zaman gidan Yari, kama mutum da Cocaine a Nigeria babbam laifi ne wanda yake daidai da kisan mutum" ya fita cikin farinciki, zuwa Anjima zai kira Police Headquater ya gaya musu yaga wata dealer ta kawo Cocaine Gidan Alhaji Abba Abu" ya fita daga dakin da farincikin yau zai kara k'untata ma Mairo, ya koma Dakin Majeed ya latso Wayarshi ya soma magana cike da gadara da isa; "Labaran, zan turo maka numbern Alhaji Abba Abu, zaka kirashi, zaka ce mishi kaji labarin yana son saida Gidanshi, ka gaya mishi zaka siya da Gidan da Komai Miliyan 50, zaka bashi Sati daya yayi settling, zaka zo kuyi magana face to face" be tsaya jin abunda zaice ba ya kashe wayan. Da Marece Sun dawo Gida dukkansu, Majeed na gaya ma Daddy "duk a wulakance ake taya Gidan, daga masu cewa Miliyan 25, sai masu cewa Miliyan 20" Daddy yace "Maganar banza maganar wofi, ko Lokacin da Marigayi Sada ya gina Gidan nan ai ya kai Miliyan 20 din, balle yanzu da komai tsada yake, don sun ga ana bukatar kudin ne ya sa suke ma Gidan Tayin banza" Mairo taji wani dum a Zuciyarta, Abba har ya tuna Gidan Sada ne? Wai ba dai Asirin nan ya fara karyewa ba, wai Ya? Abubuwa na ta 6are mata, ta dai share tace "shiyasa nace muku a bar zancen saida Gida, don wulakanci, tayin banza a ke ma Gidan" Daddy yace "kina da abunda zaki biya Alhaji Nakowa?" tayi tsaki "ku rabu da dan iskan nan, daukaka kara zanyi" Daddy yace "kina da Matsala, Gida ko yau aka samu me siye miliyan 30 wallahi sai na saida mishi, fadan da yafi karfin ka ka maidashi wasa, mu dai san mun rabu dasu" shiru dai tayi don ta san yanzu abunda ya sa kanshi, shi yakeyi. Majeed yace "dazun naje Gidan Aunty Aynarh, duk yaran na gaisheku" Daddy yayi murmushi yace duk suna lafiya ko? Sun sake jikinsu ko?" Majeed ya Murmusa yace "har ce ma Zeenatu nayi tazo muje Gida wallahi tace ba inda zata" sukayi daria banda Mairo da ta daure Fuska, Yauwa Daddy, munyi magana da Ziyada kan wani Yaron da ke nemanta, yana neman izinin zuwa gunku, don dagaske yake" Mairo tace "ba tada hankali? Muna cikin halin haula'i shine take neman dadako mana Aure?" Daddy yace "aa Maryam, ai kinga bata da masaniya kan abunda ke faruwa, kuma ai ba yanzu suka ce suke sin auren ba, gabatar wa zaayi, kafin komau ya lafa, sai inyi bugabuga na in mata abunda zan iya daidai gwargwado, don yafi da yarinya ta samu Miji a Aurar da ita, kai AbdulMajeed, kace mata ta gaya maka wanene shi, in anyi bincike, in mun yaba da halayen shi, sai ya turo Magabatanshi". Majeed yace "Daddy, Bincike ko bazai mana wuya ba, saboda ansan Yaron a Africa gabaki daya" Wuf mairo tace "wanene?" Majees yace "Zaid Sadam Abdu Gatan Marayu" Mummy da Daddy lokaci daya suka ce "Gatan marayu dai?" Majees ya jinjina kai, Daddy yace "Aiko mun je mishi gaisuwan Babanshi wata rana da zamuzo Kano" Mairo dadi ya lullubeta, shikenan karshen wahalarsu yazo, Dukiya da abunda ya tara ya linka Alhaji nakow so dubu dari, ta kasa boye farincikinta tace "Ai yayi sauri yazo wallahi, ko ina diyata ta ganshi? Allah me iko" tuni Daddy da Majeed suka gano inda ta dosa Daddy yace "Maryam, ki fita idona, ba auren Jari zanma da diyata ba, da shi ya ganta yace yanaso da ban amince mai ba sai ya nemi so gurin yarinya, amma tunda ita tace tana so, zanyi Binciken Yaro, duk da Zahirin yaro muka sani Babanshi mutumin Kirkine, in muka gano yana da wani hali ba za mu yarda ba, dole suyi hakuri da juna, abunda kike tunani ba haka zai faru ba, in abu ya tabbata Aure zamuyi ma yarinya ba maganin Matsalolin mu ba" Mairo a fusace tace "wai ni Daddy me kaji nace?" Daddy yace na dai gaya miki, ki fita Idona" tashi tayi fuuu ta wuce daki rai bace. Alhaji Labaran ya kira Daddy, ya karanto mai duk abunda Zaid ya gaya mai banda Kudin da zai biya, yace "zai zo ya ga Gida, sai suyi ciniki" Daddy yayi hamdala yace "kuzo kuga Gida Gobe, in Gida ya musu, sai ayi Ciniki". Sukayi Sallama, ya gaya ma Majeed yanda sukayi, Majeed yace " to Alhamdulilah, Allah ya sa su siya da daraja". Da daddare, Zaid ya kira PoliceHeadquater, ya basu bayanin Ganin da ya ma Matar Gidan da Cocaine, ya musu kwatancen Gidan Alhaji Abba Abu, nan da nan aka cika Motar Yan Sanda da Police sukayo Gidan Alhaji Abba Abu, suna Parlo Gabaki daya suna cin tuwo, Police suka shigo Gidan, gabansu ya fadi, Babban dan sanda yace "Ina Hajia Mairo Abba?" Mairo tace "ya akayi? Daga ina?" yace "mun samu labarin cewa kin shigo da Cocaine Garin Kano, yanzu ma haka yana dakin baccin ki" Zaro ido sukayi duka, a tare suka Maimaita "Cocaine?" "inji uban wa yace haka?" Inspectore yace "Kina iya fito mana da su, a sallameki tare da fahimtar juna, amma ba ma hukuma wuya zai kara miki charges ga laifinki, tun kafin mu kai ga bincikarki, ki fito dasu, muna da Na'ura me bincikar kayan maye(cocaine detector), indai yana Gidan nan, duk inda suke zamu ganesu, ya ba sauran umurnin kuna Detector din su hau bincikar Gidan, haka suka bar bazu suka hau bincike da Injin din. A Dakinsu Mairo, ba inda ba a duba ba, na daga k'ark'ashin Gado, saman ceiling, toilet, Wardrobe, ko ina, duk wani lungu da sak'on dakin Mairo sai da aka duba, amma baa ga komai ba, an bincika ko wani Daki na gidan, Najwa ma na daki taga an shigo bincike duk tabi ta tsorata Majeed yace " ta kwantar da hankalinta, bincike suke" haka ma dakin Majeed, aka binciki jikin Nura da ke baccin karya, da gan sai dakin yara, da dakin Zaineema, ko ina na cikin Gidan sai da aka bincika, har da jikinsu sai da aka sa naurar nan aka bincikesu, sai da suka zagaya baya Boysquaters amma shiru, kowa ya dawo yayi reporting "All Clear Sir" Inspector da Mamaki yace "are you sure?" Daddy yace "you know we can sue you for this?(kunsan muna iya kai k'ararku Kotu saboda haka?)" "Ka bar yaniskan Daddy, sai Kotu ta shiga tsakaninmu, in banda cin zarafi, a rasa inda za a zo neman Cocaine sai Gidan nan?" ta ci kwalar Inspector din "Danubanka sai ka nemo min Cocaine a cikin Gidan nan, saboda kun raina mu, binciken ku zai kawo ku nan? To muje ka kara bincikar mu, ko in kwale ma jikina har ciki kagani ko na boye a chan" da kyar Majeed ya raba Mommy da Inspector, Inspector ya basu hakuri, ya sanar dasu cewa waya aka musu aka basu kwatancen Gidan, aka tabbatar musu cewa Akwai Cocaine a dakin Hajiar" Daddy yace "Shikenan, bawani abu, but next time, dont barge in to people's house without an Evidence" suka sake basu hakuri suka wuce. Mairo ta hau haki, Wallahi Alhaji Nakowa ne, shine da iskancin nan, aiko sai na mai Wulakanci, da ni yake zancen, Daddy yace "Maryam, tunda dai basu ci nasara akan mu ba, sai mu gode ma Allah, don tsakanina da Allah na mugun tsorata, sai mu sake kula da lura, koma waye, Allah ya fisu" Majeed yace "Nagode ma Allah yaran nan ba sa nan, da hankalinsu a tashe yake". Allah ya kara tsare mu suka amsa da Amin banda Mairo da ke ta huci. Zaid ya zube ya zauna dirshen a k'asa, lately things are not going as he planned, karo na uku kenan, yana shirya abu yana rugujewa, amma yana da tabbacin wannan, da kanshi ya daga katifa ya saka Cocaine dinnan, ko dai basu bincika da kyau bane? Amma da detector sukayi amfani, ya san yanda abun ke aiki, ko da nesa da kilometer 10 ne zaiyi detecting wurin, Zuciyar shi ta raya mai "wani ya dauke ya salwantar kamar yanda yake bata maka duk wani shiri" A Fili yace "to waye?" shi yasan lokacin da yake shirinshi ba kowa a Gidan, to ko Aljannu ne? Kai Impossible, in ma daukewa akayi wani ne ya dauke, wanin da ya san duk shirin da yakeyi, koma waye zai biya abunda yayi, cocaine dinnan ya kai kusan Miliyan in saidawa zaayi, don ma abun ko a jikinshi, da wani ne da yayi kukan asara, kwalliya be biya kudin sabulu ba, zai gano ko waye, ko da Aljanni ne, zai gane be da wayau. ***** *KAFIN DAREN* Tana lura da duk wani taku na Nura, ta ga ya shigo da wani package a Hannu, hankali kwance ya sa makulli ya bude k'ofar Dakin, ya shiga beyi Minti biyu ba, ya fito, shikadai ya fito ba package din, a ranta tace to meye ciki? Kila wani sharrin zai k'ulla musu, ya sa Mukulli ya sake kullewa ya soma kiraye kirayen waya a Parlor yana bada Orders wurare dabandaban, ta lura shi din wani babba ne, yanda yake waya yana bada
Chapter 64 · 0% Book details