← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 128

Sashe 46

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

su da komai sai gidan da suke ciki, bar ganin Gidan Tamfatsetse, shi kadai suka mallaka, duk buga buga sukeyi, so suke su hadaka da ita ka zaman musu source of income, is that the kind of girl you want to marry? Babanka is a Respected Man, Auren diyar Abba Abu will tarnish your Family's Image" Amjad yayi shiru yana nazarin Zaid, yace "Are you sure?" Zaid yayi dan tsaki yace "trust me i have nothing to gain idan na musu sharri, you have sources, ka bincika ka gani, i thought you should know ne, don ni na san halaiyarsu kaf, we were once neighbors a Abuja, Use your brain, Number dina ne, if you need anything" Dif Zaid ya kashe wayar, ya Murmushin jin dadi ya san yaci nasara. K A N O Ng Zufa ya shiga keto ma Amjad, tunani barkatai, shin ya yarda da abin da yaji? To Zaid Sadam ne ya gaya mishi, Zaid Sadam kuwa ya sanshi a France, ba ruwanshi da harkan kowa, duk yanda Amjad ya so shige ma Zaid a wannan, Zaid be bashi chance ba, har Zaid ya k'are zaman France Amjad ba zaice ga Abokin Zaid ba, Zaid be damu da kowa ba, to don me zai musu k'arya, yana da kudi sosai don me zai bata lokaci wurin musu sharri? lokaci daya zuciyarshi ta aminta da abunda Zaid ya fada mai, Allah ne ya soshi, ya tsamoshi daga sharrinsu, ya wurga ma Ziyada wani kallon tsana ya tashi ya kwashi keys dinshi, ya sa kai ya fita, da mamaki ta bishi da ido, to me ya faru, duk da bata damu ba, taji ba dadi, amma da alama wayar da ya amsa ne aka bashi bad news. Ta kwashe kayan ta kai kitchen, Su Mummy suka mata chaa, "ya tafi? Ya kuka kare?" Ziyada bata son surutu sai kawai tace "yace zamuyi Waya" ta shige dakin Hajjo. **** WASHEGARI Sadaf Sadaf ta k'araso Parlorn daidai Wayar da ke ajiye ta ci burki, ta dauka wayan, bata san wayar waye ba, addua take Allah ya sa wayar ba Password, tana swipping ko taci saa wayar ba Password, ta tura wayar cikin rigarta ta fita waje da sauri tayi baya wurin boysquaters. A sarsarfa ta sa numbern Paapa, sai da ta kira so uku be dauka ba, kamar tayi kuka, tayi dialing numbern Maama, itama kira take tayi amma no response, Waiyo Allah Najwa ji take kamar ta sa ihu, tana so tayi waya da Maaman ta, jin Alamun ana takowa ta inda take ya sata deleting numbers din da sauri ta maida wayan a riga ta koma parlor, inda ta ga wayan ta maida ta ajiye, ta koma Daki. I N D I A Kwanaki 18 daidai kenan da tafiyar Najwa, in ka Alhaji Sada Abu da Matarshi sai sun baka tausayi, Rayuwa suke kamar Matattu, ba su da wani jin dadi da walwala, duk sun rame sun fita hayacinsu, barin ma dai Maaman Najwa, hardai shirin biyo ta Nigeria sukayi, kamar Kullum suka kasa, wannan karon Paapa ne ya sul6e ya fadi k'asa, ya karye k'ashi, yanzu haka suna Asibitin Apollo inda Maama ke aiki, Zafi dubu da goma wurin Maama, ga rashin sanin halin da diyarta ke ciki, ga Miji kwance a Asibiti ba lafiya. Da ta samu Bacci ya dauki Paapa, sai tace bari ta tashi taje Gida tayi wanka, sai su dawo tare da Vijhay. * Wayar Paapa yayi ta ringing har So uku kafin nata ya hau ruri, tana cikin gida, Wayoyin kuma suna cikin Mota inda ta barsu, sai da tayi wanka ta dan dafa musu Abinci, kafin ta kira Vijhay suka koma Asibiti, ba tare da ta duba Wayarta ba ko na Paapa, ko da suka isa Asibitin, Paapa ya farka, Maama tace "Papi kya huwa?" a hankali yace " Najw a-" ta karado gunshi da sauri ta riko hannunshi, yace "Yesmeenah, nayi Mafarkin Najwa na ta kwala min kira" da sauri ta tashi ta wawuro Jakkarta ta ciro wayoyinsu, Ikon Allah taga missed calls 3 ana Paapa, Biyar ana ta, kuma international call, callcode din Nigeria +234, kuka ta fashe dashi tace "Wallahi Papi Najwa ce, Najwa ce ta kira mu" yunk'urin tashi yakeyi Vijhay ya tareshi. Maama tabi bayan Missed call din ana dauka "Meri Beta(Diyata), Najwanatu Ke ce?" shiru ba amsa, Hello kinaji? Kiyi magana mana, bakiyi missing Maama dinki bane? Haba diyata ki min magana" nan ma Shiru, sai nishin da takeji sama sama, Maama ta fara shesheka tace " ba zakiyi magana ba, to ga Paapan ki ? Da sauri ta ba Paapa wayan "Papi tak'i ta min magana" Paapa ya amsa wayan "Hello, Hello, ba kya jine, kiyi magana mana" dif sukaji wayar ta katse, hannu na rawa suka sake dialing, sai akayi rejecting, da su ka kara sai ji sukayi wayar a kashe, Maama tace "Papi meke faruwa? Najwa ta kira mu taki magana" Paapa yace "kwantar da hankalinki, it shows that Najwa is fine, tunda har ta iya kiranmu, kila service ne, network ne, shiyasa baa ji, ko kuma chargy it can be anything, thing positively Yesmeenah, Najwa zata sake kiranmu kinji?" Da haka ya lallabata har ta dan kwantar da hankalinta. K A N O Ng Ta shigo Parlo dauke da plate din fruits, ta zauna tana cin Apple cike da tak'ama da isa, Hajia Mairo kenan, Uwar Gidan Abba Abu, tana chanza Channel taji wayarta na ringing, Janyo wayar tayi ta ga International Number ce, +91, da mamaki tace "toufa, wannan numbern wace k'asa ce?" tana dauka ta sa a kunne tare da fadin "Hello" Muryar da taji ne ya sa kirjinta Dukan Chalugude, gabanta kamar ya fashe don duka da sauri, tayi k'asak'e tana sauraron Muryan da ke Amo a kunnenta, ba zatace ga abunda matar ke cewa ba, amma hankalinta in yayi k'ololuwa to ya tashi, bata gama tsurewa ba, sai da taji Matar tace "Papi" hankalinta be kai ga tashi ba kamar yanda taji Muryan Namijin da ta fara So a rayuwarta, ba zata iya mance Muryarshi ba, tsoro da fargaba ya sata latse wayar, a guje ta fada dakinta, ta shige toilet da gudu, shower ta sakar ma Kanta, bata damu da kayan da ke jikinta ba, ya akayi haka? Shine tambayar da ke kai kawo a kanta, ta ya akayi suka kirata? Ya akayi suka samu numbern ta? Sada? Yesmin? Ya akayi suka ita kiranta wai? Ita da aka bata tabbacin zasu guje duk abunda zai sadasu da Nigeria, ta ya zasu iya kiran Nunbern Nigeria? Tsigar jikinta duk suka mimike, ina ma zata iya kuka, ta kasa, Kar fa su dawo, ta ya akayi, Mamaki da tsoro sun hanata yarda da cewa su dinne suka kirata, da gangan ta k'aryata kanta, ba su bane, it cant be them, ba Sada bane, ba Yesmin bane, ba su bane, kar ku min haka, kar ku dawo, kar ku dawo donAllah, ba kunya ba tsoron Allah Mairo ta daga hannu sama tana rokon Allah, Allah ya k'ara nesanta Sada da Matarshi da Nigeria, amma fa kamar taji sun fadi Sunan Najwa, what if sune Parents din Najwa? What if-?" da sauri ta kawar da tunanin nan, a fili tace "No, it cant be" ita fa duk yanda zata kawar da tunanin nan sai ta kawar dashi, ta gama da babin Sada da Yesmin, abunda ya faru sama da shekara 18 shine zaace sai yanzu zasu baiyana? Be yiwuwa, kawai banzan tunani take tayi, ba su bane, Mairo da taurin Zuciya, ta kan kitsa ma kanta abunda take so ta yarda dashi, haka tasa Zuciyarta yarda da ba su din bane, ta fito daga toilet ta chanza kaya, kai tsaye ta dauko wayarta ta kunna, tayi blocking numbers din da aka kirata dasu ta fito Parlor. * Tana fitowa ta ci karo da Najwa, gaban su a tare ya yanke ya fadi, ita Najwa tana tsoron ganin Mummy, ita kuma Mummy ganin Fuskar Najwa tayi ya rikide mata ya koma mata na Yesmin. Kiris ya rage ta fadi k'asa amma da yake Mairo Mace ce mai kama da Maza sai ta cije tace "ke zonan" jiki na rawa Najwa ta k'arasa gaban Mummy ta durk'usa, Mummy tace "tambayan ki zanyi, in kika sake kika min k'arya sai na miki mugun duka kinaji na" Jikin Najwa ya hau karkarwa, ta gyada kai, Mummy ta dauko wayarta ta nuna mata last call tace "ke ki ka kira numbern nan?" da sauri Najwa harda rintse ido tace "aa" Mummy ta jinjina kai tace "danubanki ke 'yar wace k'asa ce?" muryan Aisha ta tuna inda take ce mata "Najwa you must not trust anyone" baki na rawa tace "Ghana" cikin tsawa tace "ina Iyayenki suke zaune?" tuni Najwa ta gama tsurewa, wani tsawa da Mairo ta daka mata sai da ya sata ciwon kai lokaci guda, "suma 'yan chan ne, 'yan Ghana ne" "k'arya kikeyi" "dagaske" Mummy tace "karbi wayan nan, sa numbern Iyayenki, ki kirasu in tabbatar" Najwa ta tsure tace "ban rik'e number dinsu ba" Mairo ta jawo ta ta hau kilarta, k'arya kikeyi, Najwa ta hau kuka a hankali yanda ba kowa zai ji ta ba. * Kamar daga sama sai ga Majeed, da sauri ya k'arasa gunsu, cikin Zafin nama yace "Mummy me nace miki game da Najwa?" cikin Hargowa tace "wannan yarinyar Makaryaciya ce, shes not what she says she is, wayana ta dauka ta kira Iyayenta, na tambayeta ita yar wace k'asa ce tace wai Ghana, kuma numbern da aka kira ni da shi irin Asian countries din nan ne, nace ita ta kira numbern ta k'aryata, dan uwarta nace ta ban numbern Uwarta, wai ba ta rik'e ba, dan uwarta wani da zaice be rike numbern uwarshi ba?". Majeed yace "muga Numbers din" "kika sake kika nuna mai numbers din ya bi bayan wayan kinsan Majeed da bin didik'i ya gano gaskian lamarin k'aryarki ta k'are" Zuciyar Mairo ke mata gargadi, da sauri tace "Nagoge numbers din" Majeed yace "Mummy ki bar Najwa please, idan bata so ta baki numbern Iyayenta ba dole bane, ta fada bata so Baban ta ya san inda take saboda zai mata auren Dole, da sanin Mamarta ta zo Kasar nan, ba ruwanki"
Chapter 46 · 0% Book details