Sashe 60
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
yaranmu, nayi chukuchuku na hada mata akan zata biyani in ta sayar da wasu kadarorinta da tayi ikirarin tana dasu, shine nake son Kotu me Adalci ta da tace mata ta biyani, ina da bukatar amfani da su". Kamar Robot haka take zaune, komai ya dauke mata dif,ba ta gane komai, sai da Majeed ya zungureta "Mummy yaushe kika ci bashin Miliyan Talatin? Firgigit ta tashi kamar wacce aka tsikara, kamar ta rufe Alhaji Nakowa da duka tace "Babban Balaeen chan, Kaci uwar rainin wayau Alhaji Nakowa, dan kutumar babbar buraubaka wani yace ka bamu Miliyan 20 dinnan? Ba lokacin da kuke son Majeed ya Auri Nana bane kuka kawo mana Miliyan Ashirin din har gida ba? Saboda kai baka tsoron Allah, kuma da yake karya cike yake a tunbinka zaka ce Miliyan 30 ne, kuma wai bashi, to Mortgage bank ma yaci Ubanshi, shege Makaryacin banza, sai ka danneni ka karba, karfi yaci daru ya danne, Mutumin banza". Da k'yar Alkali ya sa Mairo yin shiru, ya juya ya tambayi Alhaji Nakowa Shaidansa na Maiaro ta karbi Bashi a gunsa, yace " kwarai kuwa ina dasu ya mai shari'ah, ganin da nayi Miliyan 20 da ta karba da farko bata fara biya ba, hakan yasa naji shakkun sake bata wasu kudaden don nima lokacin ina fama da kaina, Don haka nace sai ta sa ka hannu a wadannan takardu guda biyu, sai da tayi signing gaban Matata Aminiyarta, da wasu k'awayensu su 3," Alk'ali yace a gabatar da takardu gaban Kotu, Sakatare ya amshi takardun daga hannun Alhaji Nakowa ya ba mai shariah". Sosai Alkali ya karance takardar sannan ya sa aka mik'awa Mairo ta duba ko tana da Ja, Cikin tashin hankalin da tun da tazo duniya bata taba ganin irinshi ba tace"WALLAHI WALLAHI ALKALI BAN SAN WANNAN BAYANI BA, TABBAS WANNAN SA HANNU NA NE AMMA NI BA NI NAYI BA, wani ne yayi fabricating Evidence dinnan, dis is a Forged Signature". Alk'ali yace "Alhaji Nakowa kana da Shaida, baya ga takardun nan?" Alhaji Nakowa yace "Shaidun da ke jikin Takardun, Hajia Sugrah, Hajiya Zarah Bukar, da Hajiya Suwaiba wanda suke ce ma Mom fateey, kuma duk suna cikin Kotun nan mai Albarka" Alk'ali ya bukata da su fito gaban Kotu, ya musu tamboyi suka amsa, suka shirshirga tasu karyan, suka ce a gabansu akayi a garin Abuja, tayi Signing din kudin a kan Idanunsu, kuma Alhaji Nakowa ya bata kudin kan idanunsu. Mairo ta hasala ta chakumo Hajia Suwaiba don sun fi shiri tana jijjigata "Wallahi k'arya suke man, kuji tsoron Allah Hajia Suwaiba, ku tuna Zaman mutunci da Amana da mukayi da juna, kar Alhaji Nakowa ya siyeku kuyi min kazafi" Mom Fateey ta bangajeta tace ba wani "kazafi, abunda muka gani ne muka fada, mu muna bayan gaskia". Bakin Hajiya Mairo be mutu ba, nan ta hau surfa ruwan zage zage da tsine tsine, harta Kotun da Alkalin sai da ta zage tas, Majeed ya ji kanshi na barazanar fashewa, a hankali ya zame jikinshi ya bar Kotun. Kotu ta dau Hayaniya, kowa da abunda yake tofawa, Alk'ali yayi 'yan rubuce rubucen shi, Alkali ya umurce kowa da yin shiru, da k'yar aka samu kowa yayi shiru, Alkali ya zartar da hukuncin shi kamar haka; Bayan Kotu ta saurari bangarori biyu, na me k'ara, da wadda ake k'aran, Kotu tayi watsi da k'arar Hajia Mairo a matsayin Kara Mara kan Gado, saboda rashin kwararun hujoji da Shaida, sannan kuma Kotu ta ci tarar Hajia Mairo Naira Dubu Dari Biyar don ta ci Zarafin Kotu ta Wulak'anta Kotu, Sannan kuma Kotu ta Umarci Hajiya Mairo da ta biya Alhaji Nakowa kudin sa Miliyan 30 a tsakanin Watanni Uku, in ba haka ba, Kotu zata kwatar mai hakkinshi da karfi, kuma zata fuskanci fushin Hukuma, duk wanda Hukuncin nan beyi mai ba, to yana iya daukaka k'ara zuwa Kotun K'asa" A nan Alkali ya kawo k'arshen Shariar Hajia Mairo, da Alhaji Nakowa Kotu, Alkali ya mik'e kowa ya mik'e. Kasa Motsi tayi ta kasa yarda, komai sai kware mata baya yake, tana ganin Alhaji Abba ya fita a fusace, ina ma zata iya hawaye, tana kallon Alhaji Nakowa da Iyalanshi suka tako har gabanta da Murmushin Farincikin yace "Da wa ta 6are Hajiya Mairos? Na gaya miki sai kinyi nadama, tsautsayi ya sa ki ka makani kotu bayan baki da ko sisi, while kin san komai yanzu in baki da kudi ba a damawa dake, bansha wahalan komai ba, har kawayenki, da Miliyan daya kachal na sayesu, hahah kin ban tausayi fa, anyway duk inda zaki nema min kudi ki nemo min, kafin kotu ta Wulakanta min ke, hahah ku mu tafi". Nan suka barta zaune da ta rasa abun yi, da k'arfi ta sake Ihu sai da Kotun gaba ki daya ya Amsa. ***** Ghen Ghen Ghen...... Najwa kina rusa ma Zaid Plans ko? Allah ya sa ya gane kece, he'll roast your skinny ass back to NewDelhi India Lol. Haha, ya kuka ga Shari'ar Nakowa da Mairo? Anya Mairo tayi deserving haka? Wannan sharri kala kala? Who wants justice for Mummy? Mummy kar kiji komai, akwai Allah. A bar Mairo haka? Yayyy Loverz, i made it, dama nace zaku jini yau, so please ku cigaba da mun Uzuri kunji? Makaranta, ba kullum zaku dinga samun post ba, maybe once a week, but i know you love me zaku min uzuri, so please bear with me. And Yay Wattpadians, You know you are the best right? ADAY yayi hitting 6k votes Wallahi naji dadi sosai, lets keep rocking it, ILYSVM nagode Sosai, Allah ya samu Aljanna duka, da masu voting da Ghost readers din, amma dai ghostreaders, hmmm nayi shiru. Please Vote and Comment line by line. #1love #ADAY #bibiliciousfreakingfans #anatare #nagode DADE ANA YI....sai gaskia馃挱 NA BIEBEE ISA 庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Wattpad:@biebeeisa Pg2鈨�7鈨� Yana shiga Gida ya ci karo da Najwa, yanayin da ta ganshi a ciki ya bata tsoro, ko da aka gano Asirin Nana ba ta karanci abunda take karanta a fuskarshi ba yanzu, tsoro ya bata, a hankali ta matso kusa dashi huci yakeyi a hankali, yak'i kallonta, yak'i bari su hada ido, cikin sanyi tace "Meri Jaan (Rayuwana)" runtse idanunshi yayi, be ma san su hada ido, saboda yanayin da yake ciki, hannu ta sa ta kamo hannunshi, janshi tayi har gaban 2sitter, zaunar dashi tayi, ta wuce kitchen da sauri, roban Ruwa me sanyi ta dauko da Cup, tsiyaya mai tayi ta mik'a mishi, beyi gardama ba ya karba cup din ya kafa kai, kurba uku ya shanye ruwan tas, ganin haka ya sa ta karbi Cup din, kara tsiyaya mai tayi ya sake karba ya shanye tas, zama tayi dan kusa dashi ta fara nanata " Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" tayi ta maimaitawa har sai da Majeed ya fara bi, haka sukai tayi har tsawon Minti Uku, kafin ya samu dan natsuwa. Daddy ya shigo Gidan shima a sukwane, hankalinshi shika tashe, Najwa ta tabbatar abunda ya samu Majeed shi ya samu Daddy, shima ruwan Sanyin ta dauko mishi, ta tsiyayya mai, ta bashi ya sha, a hankali yace "Nagode" wucewa tayi daki ta sanar ma Hajjo, halin da ta ga Daddy da Majeed, mikewa tayi tana sallalami, fita tayi Parlo, "Abba me ya faru?" a raunane ya dago kai ya kalleta, a hankali ya kwashe komai ya gaya mata, a fili take maimaita "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, ita ko Hajia Mairo me ya aiketa? Inace an bar maganar da dadewa?to yanzu meye abunyi?" Daddy ya sauke numfashi yace "Biyan Kotu kawai zaayi, amma ban san inda zamu samo Kudi ba" Majeed ya nisa kafin yace "A sayar da Gidan nan" Daddy yace "AbdulMajeed" Majeed ya katse shi ta hanyar cewa "Daddy, ina zamu samu 30.5 Million? Daddy, mun rasa komai fa, ina ganin mu sa Gidan nan a Kasuwa din gudun cin Mutuncin Alhaji Nakowa da Kotu" Daddy ya jinjina kai yace "Haka ne" Hajjo tace "Sai mu koma chan Rijiyar Zaki ko? Tunda tsaf gidan zai kwashe mu duka" haka suka cigaba da maganan sa Gida a Kasuwa har Mairo ta shigo ko Sallama babu. Kallo daya zaka mata kasan cewa damuwa ta cika zuciyarta fal, tayi kalar tausayi, duk ta fita hayacinta, kujera ta samu dan nesa da Hajjo ta zauna tana mayar da numfashi, Majeed ya so mata magana amma ganin zai kara cikin damuwarta ne kawai ya sashi yin shiru, Mairo ta ja tsaki karo na ba a dadi, ta dan muskuta tace "Sai na shayar da Alhaji Nakowa Madaran Mamaki wallahi, sai na nuna mishi ruwa ba tsaran kwando bane, in banda iskanci, ni zai yi wa Sharri? Shi kudi ko? Duk ya siye su Suwaiba, To wallahi sai na daukaka k'ara, sai munje Babban Kotu da su" dukkansu tsura mata idanuwa sukayi, chan Daddy yace "Enough Maryam, please, mun yanke Hukuncin zamu Saida Gidan nan, a biyasu kudin su, wata Shari'ar Sai A lahira" wani ashar Mairo ta laliyo, tace "in sun isa hadari ya daukeni, ba su isa mu saida gidanmu ba, ba su isa bane". Muskutawa Majeed yana rufe idanuwanshi a hankali, saboda zafin ds suke yaji muryan Daddy na cewa "Na bar sakar maki komai na Gidan nan Maryam, na bari, ni zan ja ragamar Gidana, daga yau, ba zaki sake yin wani abu ba tare da sani na ba, ba zaki sake yanke hukunci ba tare da shawarata ba, in kuma kikayi, Maryam, zan baki mamaki Wallahi" yana kaiwa nan, ya tashi ya kalli Maman shi, ya mata alama da zai shiga daki, kai ta gyada mai, ya wuce ciki, Hajjo ta kai dubanta ga Mairo tace "Hajia Mairo, hakuri zakiyi ku koma Gidana, dakunan zasu ishemu duka" wani irin harara Mairo ta buga ma Hajjo, kafin ta ta figi gyalenta tare da Mukulli ta fita. Duk suka bi bayanta da Ido, Hajjo tace da Majeed "Abdallah, Allah ya maka Albarka, kar ka sa damuwa a ranka, tashi ka shiga daki, ka huta ma ranka, komai yayi zafi maganinshi Allah, tashi ka tafi" Majeed ya tashi ba tare da yace mata komai ba ya shige dakinshi, tashin hankali bai sa ya tuna wani Nura ba, be ma lura be dakin ba, Zama yayi kan