Sashe 56
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
bai da amfani" Na'ela ta fashe da kuka tace "hantarar mu sukeyi kullum, haka muke fama" da sauri Majeed ya fita daga Motan yayi inda yaran suke, takalmanshi ya cire yayi kamar zai buge yaran, da gudu suka ware suna mai gwalo. Majeed ya matsa kusa dashi, ya hade kai da guiwa, Majeed ya sa hannu, bai kyamace shi ba, ya dago shi tsaye, karaf idanuwansu ya gwaraya, sunyi kusan Sakwan Goma suna kallon Juna ido cikin ido, wani kallo ne da ba su san na meye ba, kafin shi Nuran ya juya kallonshi ya koma mai Kallon Rashin sani, Na'ela ta karaso gun, da hannu Nura ya mata alama da waye wannan? Ta mayar mishi da hannu kan ya kwantar da hankalinshi, Majeed yace "kuzo mu tafi Gida". Naeela ta ja hannun Yayanta Nura ta tura shi a bayan Mota, ita kuma ta shiga gaba, Majeed yayi starting Mota yayi Hanyar Gidansu Gabanshi na dukan Ukuuku, be san yanda zasu kwashe da Mummy ba. Yana Mamaki, mutane da yawa in zasuyi abu sai dai su nemi Izinin Mahaifinsu, amma su gidansu ya sha Banbam, Mummy ce ke da gida, harta Daddyn in zaiyi abu, sai ya tambayi Izininta, wannan wani irin rayuwa ne?. Ta Madubi yake kallon Nura, shi kuwa Nuran yasan shi yake kallo, so ya k'i bari su hada ido, kallon da ya mishi dazun ya so kwance mishi abubuwa da dama, a cikin idanunshi ya ga Tausayi fal, da ya cigaba da kallonshi, zai kasa aiwatar da abunda yayi niya, its better suyi avoiding Eye Contact, duk da shi Namijin Duniya ne, ya dade yana Jiran ranan da zasuyi gani gaka da 'yan Gidan, sai yau yake jin shi daban, jikinshi yayi Sanyi, amma in ya tuna Shekari nawa ya kwasa yana gina Fansarshi sai yaji Sanyin Jiki ba nashi bane, he went through alot to stop now, ba zai yiwu bane, lokacin da suka sha kwanan Gidan, Rayuwanshi ya soma dawo mai, ya tuna lokacin da ya bude Wallet din Baba Abba ya kwashe kudin Cikin ya gudu ko takalma be da a k'afa, duwatsu na chakar mai k'afa, ya gudu don tseratar da Rayuwanshi, Hawaye ya gangaro mai, ya sa hannu ya share, a idon Majeed, nan ya kara jin tausayinsu duka, horn yayi Fallalu Direba ya bude Gidan, ya shiga Yayi Parking. Nura ko ince Zaid ya daga kai ya bi Gidan da Kallo, komai na nan yanda yake, ba abunda ya chanza, Da ba dan Hajiya Mairo ba, da yanzu shi da Mamanshi, da Babanshi, da K'annen da Allah kadai ya san yawansu ne a Gidan nan, Kai, Wallahi dole ya Wulakanta Hajia Mairo da Zuriarta, ba zai taba yafe mata ba, duk sauran Farincikinsu sai ya rusar dasu, ya fara da Ziyada, sai ya bari lokacin da ya zamana ba zata iya rayuwa babu shi ba, lokacin zai Wulakantata, ya tozartar da ita, he'll break her heart up,shatter her dreams and she wont be able to love ever again. Hannun Naeela ya ji a na shi, ashe ana ta mai magana ya zo su shiga yana chan duniyar tunani, oh oops, hakan ma yayi, don abun yayi kama da Kurman gaske. 9:45am ne, Kan Dinning Table, Mummy, Daddy, Zaineema, da Hajjo keyin Breakfast, Majeed ya shigo da Sallama, Mummy ta amsa mai da faraa, "Boy, Har kadawo daga kai Ziyadan Makaranta?" ya gyada kai tace "zo zauna kayi breakfast" yanayinshi ya chanza, tace "Yadai Boy?" yace "Mummy bani kadai bane, tace " kai da su waye?" yace "Mummy, ni da wasu bayin Allah ne" a takaice ya basu labarinsu Naeelah, Mummy tuni ta fara hura hanci tace "AbdulMajeed, kafita ido na tun wuri, wato kaine Redcross ko? Kai kafi kowa Imani, to sannu Mai taimakon Agajin gaggawa, kayi na farko kaci Nasara, shine kace bari ka karo wasu har biyu ko? Mace har da Namiji, saura maka Mutanen dutsen Dala, ban ma san ganinsu tun wuri ka fitar da Mutanen kar in saba maka" kafin Majeed yayi Magana, tuni Zaid ya Banko Labulen Dinning din ya shigo, Hajjo, Daddy, Mummy da Zaineema suka Mik'e tsaye lokaci daya... 掳掳掳掳掳 Ghen Ghen, So Majeed yaci Alwashin taimakon Najwa ko ta halin k'ak'a, hmm this Majeed always Acting the Good Guy. Is Zaid really Playing Ziyada? Poor Ziyada, girl is into the guy like Sosai, anya Zaid zai taba Sonta? is there hope for these two? Zaid in Abba Abu's? Omg, What is Zaid doing? What will happen next? Dont ask me I really dont know. Zaid a Roof daya da Najwa? Seriously?. Hello Bibiliciousfreakingfans, ga Babi na Ashirin da hudu, kamar yanda nayi maku Alkawarin zaizo soonest gashi na cika. Nasan Zaku k'ara min Uzuri, saboda na koma Makaranta, abubuwan za su sake Yawa, amma nasan kuna tare dani kamar yanda nake tare daku. Bear with me please. Tsakani da Allah 'yan Labe (Ghost Readers)kuna k'ona min rai, ganin gari ne zai sa kayi karatu a Wattpad amma voting ya gaggareka? Haba mana? Ba kusan yanda nake son ganin Notifications din Voting din da kukeyi ba, ba fa zai rageku da komai ba, donAllah yan labe ku bari, haba mana, ba girmanku bane, yanda kuke karantawa kunajin dadi kuyi wa Allah kuyi Voting nima inji dadi. Ehen to the real wattpadiansbibiliciousfreakingfans, sorry didnt get to reply your comments, was super busy, lets keep rolling Aye? we good now, Vote and Comment Line by Line. #1love #ADAY #bibiliciousfreakingfans #anatare #nagode Biebee Isa Add Vot DADE ANA YI....sai gaskia馃挱 NA BIEBEE ISA 庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Wattpad:@biebeeisa Pg2鈨�5鈨� Daya bayan daya ya ke binsu da kallo, su ma duk shi suka zuba ma ido, idon Zaid ya tsaya chak kan Hajjo, yana tunanin inda ya san fuskar, tabbas yasan Fuskar nan, amma a ina, 'Umma Hajia ce' cewar zuciyarsa, zubewa yayi a k'asa, Majeed yayi saurin tarban shi, Mairo ta fara surfa bala'i, "danubanka waye sa'anka a nan da zaka shigo kana bin mu da wani mugun kallo?fita danubanka" da sauri Zaid ya daga Ido ya watsa ma Mummy wani mugun kallo wanda zata rantse da Allah taji tsoro. Naeela ta shigo da sauri ta zube inda Zaid yake, tace "kuyi mai afuwa, be san abunda yakeyi ba, ya ga 'yallabai ya shigo ne, shiyasa ya biyoshi, kuyi mai aikin gafara" ta tallabo Zaid ta mikar da shi, tace "Ya Nura mu fita, mesa ka biyo shi?" sosai Hajjo taji tausayinsu, tace "ka sa musu Abinci Abdallah" Mairo tayi karaf tace "Burauba ne!" Daddy yace "Maryaaam" alamun gargadi, ta kalli Daddy kafin ta wuce fuuu kamar zata tashi sama. Zaineema ma ta tsame hannunta ta shige ciki. Daddy ya kallesu yana me tausauya musu "AbdulMajeed, ka basu abinci suci" yace "to Daddy" ya matso inda warmers din suke aje, ya zuzzuba musu a plate, Hajjo tace kuzo ku zauba ku ci" Naeela tayi murmushi ta karaso, Zaid na tsaye yayi kamar beji ba, sai da Hajjo ta mik'e ta kamo hannunshi tana fadin "Zo nan Jikana, Zo kaci abinci" kallonta yakeyi sosai, wani abu na ratsa zuciyarshi, 'Jikanta' ko ta ganeshi ne? Binta kawai yayi ya zauna kan dining table din. Matso mai da Plate Hajjo tayi da sauri ya kawar da fuska a ranshi yace 'i cant eat this shit', Taliya ne da Miya, ya ma zaayi yayi breakfast da Taliya da Miya?, kuma yana kallon kalar taliyar ya tsaneshi, shiyasa ba zai iya ci ba, shi da duk kayan Abincin Gidanshi na waje ne, Hajjo ta tabo shi, ta mai alamu da ya ci, kai kawai ya girgiza mata, Naaela da ke cin abincin tace "Hajia ya k'oshi, da Safen nan na sai mashi k'osan talatin ina jin ya k'oshi, idan yana jin yunwa zai min alama" Hajjo tace "to shikenan" Majeed yace "Daddy, wai da Boysquaters zan sauke su?" Daddy yace "anya, Majeed? Ina ganin BQ dinnan duk karikitai ke ciki" Majeed ya danyi shiru sai chan yace "da Mummy zata yarda, ita Na'ilar sai ta zauna tare da 'yanmatan, shikuma Nuran sai mu zauna tare a dakinmu". Hajjo tace "ita Yarbudurwar sai tazo nan dakin mu hadu da Najwa" Daddy ya nisa yace "hakan ma yayi" Majeed yace "Mummy fa?" "kar ka damu da ita" cewar Daddy, Naeelah ta zube k'asa tana godia harda kukan farinciki, ta k'ara da cewa, zata dinga fita neman aiki, in Allah ya sa aka dace, zan tara sannan mu san nayi, Mungode". Hakan kuwa akayi, tana gama Kalaci Hajjo ta tafi da ita daki, shi kuma Majeed ya kama hannun Zaid suka wuce chan dakinshi, Majeed ya tura Zaid cikin toilet, ya mai alama da yayi wanka. Fita yayi yana me neman numbern Najwa ringing daya ta dauka: "PureHeart ina BQ ina jiranki, i want us to talk" cikin sanyin Muryarta tace "Sorry, bana gida"da mamaki yace"what?" tace "Sorry, ban gaya ma ba, Mamma ne ta kira tace sun tura min kudi a moneygram na GTBank" shiru Majeed yayi yace "Stay where you are, gani nan zuwa". Ya kashe wayar ya fita. * Tsaki yayi a karo na ba adadi, yana lek'awa ya ga Majeed ya fita, shima ya fito daga toilet din, ya dan zaro wayanshi daga cikin wandonshi, ya dan latsa wasu numbers ya kira, "Hello Arm" Amstrong daga dayan bangaren ya amsa "Hello Oga" Cike da matsuwa Zaid yace "i'm tired, i cant survive here" Arnstrong yayi daria yace "too early for you to say" Zaid yace "I cant eat the sh*t they are eating here(ban iya cin abinci da suke ci a nan)" sosai Amstrong yayi daria Zaid ya fara k'ulluwa yace "f*ck you! Get me lunch later, text me what to tell that girl (ka kawo min abincin rana anjima, ka min text din abunda zance ma yarinyar nan, yana nufin Ziyada)". Amstrong ya tsaida dariyan shi, yace "OK". Katse wayar yayi yana kallon dakin AbdulMajeed, a Lokacin dakin Mahaifiyarshi ce, ya tuna lokacin da Maman shi ke mai wanka shi da AbdulMajeed, lokacin da zasu tube zir su shiga wanka tare, a dakin nan suke wasan banza mama ta bisu da gudu suyi ta wanata suna zagaye dakin a guje, dakin nan na da tarihi, yana cikin tunaninshi ne wayarshi tayi vibrating alamun text ya shigo, yana budewa ya