← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 128

Sashe 68

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

聽 聽 聽 聽聽 Zaune suke cikin Parlorn Abba Abu's Mansion, kallon wakeken Parlorn yake yana murmushi, bejin soki burutsun da Armstrong yake mai,聽 hankalinshi na chan gun tunani, komai na tafiyan mishi daidai,聽 komai na tafiyan mishi kamar yanda ya tsara, amma cikin zuciyanshi yana jin yana kewan wani abu,聽 kamar wani abu a cikin zuciyanshi is empty,聽 like something聽 is missing, "to meye?" Ya fada a bayyane,聽 Armstrong聽 ya kalleshi,聽 ya lura Ogan nashi yana cikin damuwa yace "Sup Boss?" kamar jiranshi Zaid yake yace "Arm,聽 i dont know whats happening to me,聽 but i'm feeling empty" Arnstrong ya kalleshi yace聽 "You feeling聽 Empty? In this bighouse?(kaji ka bakomai? A cikin wannan babban gidan?) " hannu biyu Zaid ya sa yana mai bayani yanda yake so ya fahince shi "Arm, Its聽 like i'm missing something,聽 like a lame person,聽 like a human with no ear, or eye (ina ji kamar ba ni ba,聽 kamar akwai wani abun da babu a jikina,聽 ina jina kamar wani gurgu,聽 kamar mutum mara kunne ko ido)" Armstrong聽 ya kalleshi sosai yace聽 "But why? All you ever wanted was this house,聽 and its yours why do you feel like something聽 is missing?(amma saboda me?聽 Wannan gidan ne burinka,聽 kuma yanzu naka ne,聽 meyasa kakeji kamar baka cika ba? ) " Hannu biyu zaid ya sa ya dafe kanshi kamar zaiyi kuka yace "I really dont know".聽

Shiru sukayi na wani lokaci kafin Armstrong聽cikin sanyin聽 jiki yace "You are inlove boss" wani darian rainin wayau Zaid yayi wanda tsawon shekarunsu tare Armstrong be taba yin irinshi ba "Hahahha What?" Armstronng聽 yace "you wont believe it,聽 but you love thay your cousin, shes the one you are missing(ba zaka yarda ba,聽 amma kana son Yaruwarka,聽 ita ce kake rashi)"聽 da karfi Zaid yace "LOL, Arm you are delusional, take this, go take your baby{booze} (Arm kana hauka, karba,聽 je ka sha giyarka)" ya ciro rafar dubu ya jefo mishi,聽 Arm ya chafe yana daria ya mike yace "Think about it"聽聽 Zaid ya dan kausasa murya yace "Out" da sauri Armstrong聽 ya fita yana daria.

A ganinshi ya mallaki Gidan聽 nan ya gama cikar burinshi,聽 a ganinshi zaman su a Gidan Hajjo sabon聽 shafi ne na talauci, da karfi da yaji ya tallautasu, hakan ya ci ace ya sa shi farinciki,聽 duk wani burinsa ya cika, ya ga bayansu, ya ga karshensu, amma聽 akwai sauran rina akaba,聽 a hankali ya furta "Ziyada".聽

Yau Kwanan su 9 yau basu yi waya ba,聽 tun randa yaje gidan Aunty Ainarh,聽 gani yake ya samu Gidan to neman me zai cigaba聽 da yi mata? Yayi zaton ya gama aikinshi na dasa mata Soyayyarshi聽 a zuciyarta, yasan yanzu tana cikin damuwa da takejin wayarshi a kashe , a kan idonshi tayi ta kiranshi baya da dauka,聽 karshe ya kashe wayar da yake kiranta da shi,聽 baya son damuwa sai gashi tunanin Ziyada na sashi damuwa, ya dayki聽 maganar Armstrong kamar Mara kan gado,聽 be dauki聽 maganaar da wata amafani ba,聽 tsaki ya buga,聽 zuciyarshi tace "ai shes not heartbroken yet,聽 rabuwa da ita ta haka bazai yi making wani聽 effect ba, ya rabu da ita ta hanyar da zai聽 taba zuciyoyin Abba Abu's duka, ya wulakanta ta, ya tozarata ta,聽 ta hanya daya ce hanyar 'Aure',聽 Zai Aureta ya gallaza mata,聽 ya gana mata azaba karshe聽 ya mata sakin cin mutunci bayan ya zubar mata da k'ima da daraja a idon mutane,聽 da wannan聽 zai gama da babin Abba Abu gabaki daya,聽 Murmushin mugunta ya sake a baiyane yace "Sai na Aureki Ziyada Abba Abu".
******

We are back people,聽 i've missed you so much bibilicious freaking fans,聽 i appreciate聽 each and every single one of you #1love.

Ehen,聽 lets see how many votes and comments this page will聽 get for the first time after a long time.聽 Vote and Comment Line by Line.

#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode

Biebee Isa
馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Wattpad:@biebeeisa

Pg2鈨�9鈨�

Kiran Alhaji Ado Mali ya shigo wayar Zaid,聽 kamar jiranshi聽 yake聽 ya daga da sauri sai kuma ya rasa me zaice mai,聽 daga bangaren Alhaji Ado yace "Allah ya ji k'an Gatan Marayu" dadi ya ziryaci Zaid,聽 a duk lokacin da aka ma babanshi addua ya kan tsinci kanshi cikin jin dadi da Annashuwa, a kasaitance yace "Ameen Baba Ado" "Muna Lafiya Gatan Marayu na biyu?" Zaid da ya matsu da ya zaiyane mai damuwanshi聽 yace"Eh聽 Baba Ado" suka danyi shiru na wasu dakiku kafin聽 Alhaji Ado yace "dazun naga聽 missed call dinka,聽 lokacin ina tare da mai girma shugaban k'asa" Zaid ya rasa ya zai fara magana,聽 chan kuma yace "uhm,聽 dama gidan da nake zuwa sukace in kira Iyayena"聽 sai da Alhaji聽 Ado ya dade yana nazarin Zaid kafin ya聽 fahimci inda聽 zancen sa ya nufa yace "Zaid,聽 kana nufin inda kake neman yarinya aka ce ka turo聽 magabatanka?" dan tsaki yayi mara sauti kafin yace "eh" Baba Ado yace "Alhamdulilah, kana Porthacourt ne?" a takaice Zaid yace "Ina Kano" Alhaji Ado yace "ina Abuja,聽 amma gobe sai in biyo jirgi inzo聽 Kano,聽 zan sanar da Alhaji Umar,聽聽 in yanada lokaci聽 sai muje tare" Zaid yace "Nagode Baba, Allah ya k'ara girma" suka ajiye wayan, ya kanji natsuwa in yana magana da Alhaji Ado, ya kan tuna babanshi,聽 yanayinsu harta maganansu iri daya.

Alhaji Ado Mali Shahararen dan kasuwa me sarrafa gwal tsakanin Mali,聽 Senegal da Nigeria, aminin Marigayi Alhaji Sadam Audu gatan Marayu ne,聽 farkon zuwan Alhaji Ado Nigeria da Gatan Marayu suka fara hulda,聽 haka har Aminta ta shiga tsakaninsu,聽 yanda Alhaji Sadam Ke som Zaid聽 haka Alhaji Ado ke sonshi,聽 don dai shi Zaid din dan kutsu ne be dauke shi uba ba kuma bai zuwa inda yake,聽 amma sosai聽 yake ganin mutuncin Baba Ado.

Yayi mamaki kwarai da ya tuntunbi Baba Ado da maganan Ziyada,聽 sai yanzu ya ke tambayan kanshi聽 dalilin da ya sashi kiran聽 Baba Ado,聽 ya ga Auren ba auren soyayya bane,聽 auren daukar fansa ne,聽 meyasa be yi hayan Iyayen da zasu je gidansu Ziyada ba? Auren ba Aure bane,聽 na wasu聽 lokkuta ne,聽 meyasa be nemo iyayen bogi ba sai Babban Mutum kamar Baba Ado,聽 wanda a yanzu yake ganin shine babanshi.

"Saboda kana sonta,聽 saboda ka na son gina Auren ku ta hanya Madaidaiciya,聽 ba ka son harkar聽 karya a maganar aurenku,聽 kana iya聽 bin ko wacce hanya don cikar burinka ba tare da ka damu da illar bin hanyar nan ba, amma ta kan Ziyada,聽 ba zaka iya ba,聽 ba zaka fara rayuwar aurenku da karya ba" Cewar Zuciyar Zaid.
Ya runtse ido da Dan k'arfi yace "Rubbish,聽 you are soo stupid for thinking聽 of this" ya buga tsaki, ya cigaba聽 da surutanshi shi kadai.

聽聽 Da kwatancen AbdulMajeed Aunty Aynarh ta kawo su Gidan Hajjo, ta juyo ta kallesu tace "ku fito ko?"聽 Zeenatu tace "where is this place?" Aunty Aynarh ta murmusa, Ziyada da Zaineema suka kalli Gidan
su ma suna tunanin ina ne nan, don da wayonsu ba su zo gidan ba, Hajjo tace "sun dawo nan din ne?" Aunty Aynarh ta gyada kai, kafin wani ya k'ara magana AbdulMajeed ya fito daga gidan, gabansu ya yanke ya fadi, duk da duhu ya fara yi,聽 hakan be sasu kasa ganeshi ba,聽 duk ya tsamure, ya kara tsawo, fuskarshi ta sake tsawo saboda rama, kamar wanda yayi sati yana jinya, Ziyada ta sa hannu ta bude kofar mota ta karasa ta tsaya a gabanshi, tsura mai idanuwanta tayi,聽 baki na rawa tace "YaMaji, baka da lafiya ne?" murmushi yake k'okarin yi mata, ya girgiza kai ganin hawaye kwancen cikin idonta yace "its going to be Alright" ya ja hannunta suka karasa gabansu Hajjo, da Murmushi yake gaidasu bayan ya rungume kanenshi, Aynar da hajjo sukace "Majeed baka lafiya ne?" murmushi ya kwakulo yace "lafiya lau nake" gudun kar su sake watso mai tambaya yace "ku mu shiga Gida" Zeenatu ta tirje聽 tace "ina ne nan?" Majeed yayi murmushi yace "sabon gidanmu".

Suka bi Gidan da kallo gabaki dayansu,聽 ganin聽 rashin yarda a cikin idanuwansu ya sa shi cewa "Ku muje ko" yayi gaba,聽 ba su da wani zabin da ya wuce su bishi a baya suna kallon Gidan, ba karamin gida bane,聽 kuma ba babba ne,聽 irin gidajen da din nan ne na block,聽 a lokacin da sai masu kudi ke zama a ireiren Gidan,聽 amma da yake yanzu zamani ya chanza,聽 kuma tsohon gidane,聽 ba za a sa Gidan a ko da irin gidajen lowcost ba, suka shiga da sallama,聽 tabarma suka gani shimfide Daddy da Mummy na zauna kai,聽 chan gefe kuma Najwa ke rakube,聽 Mummy ta tashi da sauri ta rungumo yayanta,聽 Daddy ya tashi聽yana musu sannu da zuwa.聽 Aunty Aynarh ta lumshe idanuwa ta bude,聽 har ranta takejin murmushin da Alhaji聽 Abba yake watso mata,聽 sosai ya gaida Hajjo kafin ya maida kanshi zuwa ga Hajia Aynarh.

Ran Zinatu a bace tace "Mummy ina ne nan?" Mummy ta ja numfashi da k'arfi, duk suka zuba mata ido,聽 Zaineema ta kalli Majeed tace "Yaya meyasa muke nan?" baki ma rawa Mairo tace "Erhm,聽 zamu zauna a nan ne na wani lokaci,聽 ana gyara a Gidanmu,聽 in an gama zamu koma chan" Majeed ya dafe kai yace "Mummy,聽 hakan be da amfani" ya durukusa ya dauki Muhsin,聽 ya ja hannun Zinatu ya wuce dasu daki,聽 yace "oya Sleep,聽 gobe akwai school".聽
Chapter 68 · 0% Book details