← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 128

Sashe 85

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ziyada bata taba zaton Zaid be da hankali ba sai yau, zubewa tayi a gabanshi tana kuka mai ratsa zuciya ta rungumo kafarshi, tace "Zaid, na rokeka da sunayen Allah kyawawa,聽 na hadaka da girma da zatin Allah ka bari,聽 Ya Isa haka, Enough聽 is Enough,聽 bansan meke tsakaninka da Mummy ba, ban damu ba ko ta saka mutun gabas ta yankashi ba,聽 ban damu da sannin zunubanta ba, we all are sinners(dukkan mu masu zunubai ne) ,聽聽 whatever she did she's still my Mother and you will show her some respect,聽 ka barta hakan nan,聽 you can hurt me if you want for all i care,聽 but stay away from my Family, Please,聽 na rokeka don darajan Magabantanka da suka rasu".

Be son meyasa ba,聽 maganganunta sunyi tasiri a zuciyarshi,聽 kanshi yayi nauyi ya dafe kanshi da hannu bibbiyu kafin ya furzar da huci me zafi,聽 "its not worth it" yace ma zuciyarshi, *Ziyada*,聽 yana da ita,聽 matarshi ce,聽 zai aje ta kusa dashi,聽 yayi duk abunda ya ga dama da ita, ba wanda ya isa ya hana,聽 Ajiye Ziyada a gurinshi zai fi bakanta mata rai,聽 zata dandani zafin raba 'ya da Mahaifiya, kamar yanda ta rabashi da nata iyayen,聽 gwara shi ya san sun mutu ba zasu dawo ba,聽 amma ita zata dandani jin zafin rashin diyarta alhalin tana raye, tunanin ya take?聽 Wani hali take ciki?聽 zai kasheta, zai rabasu,聽 ba zata sake ganinta ba.

Da wannan tunanin ya matso daf da Mairo yace "ki tashi,聽 ki tashi ki bar min Gida,聽 kar na sake ganinki kusa da Gidana,聽 ka.聽 naku a Unguwar nan,聽 kika bari wani yazo Unguwar nan,聽 zan sani,聽 and i will come for you all"
Mairo tayi Jim, tace "ka sake Ziyada,聽 na tafi da ita,聽 zamuyi disappearing daga rayuwarka,聽 ba zamu taba showing kanmu a gabanka ba" Murmushi聽 ZAID yayi yace "Ni na nemeku,聽 ba ku kuka nemeni ba,聽 you cant disappear from my life, Sakin Ziyada kike so nayi?聽 Zan saketa a lokacin da naga dama,聽 but for now,聽 she stays with me,聽 so ki bar Gidan nan at once,聽 kafin a fiddaki dole".

Ita ta san gardama da Zaid aikin banza ne,聽 kai shi kotu kamar ta hak'a kabbarinta ne ta shiga da kanta,聽 bata da wani karfi ko wani abun da zai sa tayi going against him,聽 karawa dashi kamar suicide ne,聽 ba zatayi wannan gangancin ba balle da ta san Ziyada na hannunshi,聽 ba zatayi kuskuren nan ba,聽 Kan guiwowinta ta zube tana kuka, Ziyada tace "Mummy ki tashi聽 please" tace "Ziyada,聽 zanyi komai a kanku,聽 durkusawa gabnshi ba komai bane,聽 Zaid ina rokonka, kayi hakuri,聽 ka yafe min, na hadaka da Allah kayi hakuri,聽 kar ka rabani da Diyata,聽 kaji tausyain wannan Uwar,聽 Diyarta kawai take so a kusa da ita,聽 kafi mu karfi,聽 kafi mu iko,聽 ka tausaya mana, zan jure rashin komai,聽 banda rashin 'yayana, komai kake so zan maka,聽 kar ka rabani da ita please".

Anzo gurin, Ran Zaid bace idanun nan sun kada sunyi Jazir cikin tsawa yace "Ashe ba dadi?聽 Iye ashe ba dadi?聽 Ashe da zafi? An rabaki da diyarki,聽 ashe abun da ciwo?聽 To ai abunda kikayi ne aka miki,聽 Tarihi ne ke maimaita kanshi, Ha!聽 Karma issa bitch huh?(K'aikayi ne ya koma kan Mashek'iya ko? ) Thats what u do,聽 in kin manta barin tuna miki,聽 You turn Brothers聽 against Eachother(Kin raba kan yanuwa) , you turn Child against his own Mother (kin juya Da Kan Uwarsa Mahaifiya)聽 You Seperate Child from his parents by killing them(Kin raba Da da Mahaifanshi,聽 ta hanyar kashesu),聽 so don an rabaki da Diyarki i think ba wani abu bane its fair Enough"
Saura kadan fitsari ya kubce mata, wasu abubuwan聽 da suka faru shekaru sama da 20 suka fado mata,聽 cikin sakwan da be wuce talatin ba ta gama nazarin maganganunshi,聽 brothers against brothers yana nufin Abba da Sada kenan, Son Against his own Mother yana nufin聽 ta juya Abba kan Hajjo kenan,聽 da kuma Seperating Child from their parents wato ta raba Zaid da Iyayenshi, amma ita ta san bata kashe kowa ba,聽 wanda taso kashewa kuma ai guduwa-- bata karasa tunaninta ba ta dago rinannun idanunta ta kalleshi, bakinta ta rufe da hannu bibbiyu tana girgiza kai a hankali ta furta *"ZAID. "*

Murmushi ya sakar mata,聽 da sauri sauri ta dinga ja da baya da baya ta fita a guje Ziyada zata bi bayanta yayi saurin chafkota,聽 ya hadata da jikinshi,聽 da sauri ta ture shi tace "Mugu Azzulmi,聽 Allah ka saka mana" ta ruga daki a guje ta sa key聽 ta fada a gado tana cizgar Kukan da bata taba zaton ta taba irinshi ba tunda uwata ta haifeta.

Tafiya take kamar Guguwa,聽 bata san inda take jefe kafarta ba,聽 kamar wata Mahaukaciya sai sambatu take; "Hajiya Ji mana" cewar Mai Napep din da tunda ta fito daga Gidan yake binta,聽 banza tayi dashi,聽 Parking Adaidaitan shi yayi ya fito,聽 ya biyota,聽 pincikota yayi suna fuskantar juna yace "Ko ki聽 ban Kudina wallahi tallahi ko na miki zindir na miki wanka da ruwan kwata a nan gurun" Mairo ta tsura mai ido,聽 bata gane kalaman da ke fitowa daga bakinshi,聽 kawai sai ta juya ta barshi,聽 Mai Adaidaita聽 cikin Zafin nama ya sha gabanta ya dauketa da Mari, nace "ki ban Kudina ko na miki bugun burauba" Hawaye suka shiga sunturi a kunatun Hajia Mairo,聽 ta kalli yaron sama da kasa,聽 ko ya Girma Zaineema聽 da kadan ne, amma sai ya daga hannu ya mareta?" ta girgiza聽 kai tayi gaba,聽 Mai Adaidaita ya sake hasala,聽 ya finciko Mayafinta ya wurgar k'asa,聽 yace "kin zata wasa nakeyi ko? Wallahi zindir zan miki in baki ban kudina ba" nan ya shiga kiciniyar cire mata Riga, daidai nan wata Dalleliyar Mota ta tsaya a gefensu,聽 "kai Assha,聽 Lafiya?" cewar wani Magidanci da ya fito daga Motar,聽 Mairo Kunya kamar ta bude kasa ta shiga,聽 Mai Adaidaita yace "Kawai Alhaji,聽 wannan Matar ta sa na dauko ta daga Sharadda Phase 2 na kawota nan,聽 sai聽 cewa tayi bari ta shiga ta kawo min kudina,聽 na fi karfin Minti 40 tsaye nan ima jiranta,聽 yanzu ko ta fito ta kama gabanta ina cewa ta ban Kudina tayi banza dani" Mutumin ya girgiza kai yace "nawa ne Kudinka?" yace "600 ne" Mutumin ya zaro dubu daya ya bashi,聽 Mai Adaidaita聽 ya ciro dari 4, ya bashi,聽 ya kalli Mairo yace "Allah聽 ya soki wallahi" Mutumin yace "shikenan dai tunda an biyaka" ya shige Napep dinshi ya ja ya wuce,聽 Mutumin ya kalli Mummy yace "Hajia, ya akayi ne?" Mummy ta dago ta kalleshi,聽 a tsorace mutumin ya zaro ido yace "Subhanallah, Hajia Mairo, dama kece?聽 Ya akayi haka?" ta rasa abunyi sai kawai ta fashe mai da kuka,聽 yace "Inallilahi,聽 Hajia,聽 kiyi hakuri kiyi shiru,聽 ina Alhaji Abba?" ta daiyi shiru,聽 ina Abdulmajeed,聽 nan ba amsa,聽 yace "to ki shiga in kaiki Gida" ta tirje taki motsi,聽 da Baban Ikhy ya ga zata bata mai lokaci kuma Jiranshi ake a wani gu,聽 sai ya ciro Kudi dubu 2 ya makala mata a hannu,聽 yace "sauri nake,聽 zan kira Alhaji Abba, ki samu Napep聽 ki hau danAllah" ya shige Motarshi ya tada ya wuce yana waigenta ta Madubi.

Baban Ikhy Makocinsu Daddy ne a lakacin suna Anguwar nan,聽 ko da zasu tashi,聽 ko sallama Mairo bata shiga tayi ba,聽 sai da wata rana Baban Ikhyn ya kira Daddy yace "ya bar ganinsu a Masallaci ko sunyi tafia ne?" cike da kunya Daddy ya gaya mai ai tashi sukayi,聽 abun yazo cikin gaggawa shisa ba wanda ya sani.
Akan hanya Baban Ikhy ya kira Daddy ya sanar mishi da abunda ya gani game da Mairo,聽 Daddy聽 yayi Godia sukayi Sallama, dama Hajia Aynar ta sanar dashi yanda sukayi da Mairo,聽 a ranshi yace "nasan a rina shiyasa naki gaya miki inda take tun farko,聽 ba inda zani,聽 ina nan zaki dawo".聽 Gyara zamanshi yayi ya cigaba da karatun Jarida.

Kusan Awa 2 suka shude Mairo bata dawo gida ba,聽 har Daddy ya soma damuwa, ya gaya ma AbdulMajeed abunda ake ciki,聽 hankalinsu ya tashi,聽 yace "Daddy da tun dazun ka fada da na hau Adaidaita聽 naje,聽 kasan Mummy in abu na damunta" Daddy yace yanzu dai muje, Zaineema da sauran yaran sukace zasu bisu,聽 Daddy聽 yace "aa ku bari muje,聽 ku tsaya a nan incase ta dawo sai ku sanar damu" suka gyada kai cikin damuwa,聽 Zinatu聽 kam har ta fara kuka,聽 Najwa na lallashinta, a daidai kofar shiga da fita聽 Gidan Mummy ta shigo,聽 suna ganinta suka hada baki gun cewa "Alhamdulilah" kamar jira take ta saka Ihu mai karfin tsiya tare da zubewa kasa tana tirjiya,聽 cikin tashin hankali duk sukayi kanta.
鈥⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€⑩€�

Ghen Ghen, To kunga abunda ya faru a Page dinnan,聽 Me zakuce game da karon Zaid da Mairo?
Ko Mairo ta Haukace ne?

Yeah, Yeah I know Zaid baya kyautawa Ziyada,nima ban jin dadi, amma Zaid zai shiga hankalinshi soon i promise,聽 me zai karkato da hankalin Zaid kan Ziyada?聽 Guesses?

Wai ina Labarin Mutanen India?

#NajwaMajeed?

Heheheh i cant wait to start typing the next Page, but i'll type IF naga number of Votes na Increasing.
Vote and Comment Line by Line.

#1love
#ADAY
#Bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode

Biebee Isa.

馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱

NA

BIEBEE ISA

Wattpad:@biebeeisa

Pg3鈨�4鈨�

Bin bayan Motan Baban Ikhi tayi da kallo kamar tana kallon TV har sai da ta daina ganin kurar Motar, kan dakalin wani Gida ta zauna ta rafka uban tagumi ta shiga duniar tunani;
Maganganun Mijin Ziyada marasa kan Gado, yana maganan ta kashe mutane, duk iskancinta ai bata taba kashe rai ba, da yake magana kamar ya santa, ai ko a da ita ta san bata kashe Sada da Yesmin ba, ba zata iya kashesu ba, ta san ta musu Kurciya sun bar k'asar gabaki daya kuma ba zasu taba dawowa ba, Zaidun Yesmin kuma tana da tabbacin mutuwarsa daga bakin Mallaminta wanda shine ya ma su Sada Kurciya, Iyakacin abunda ta san tayi kenan, so bata ga ta inda hakan ya shafe shi mijin Ziyadan ba.
Chapter 85 · 0% Book details