← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 128

Sashe 29

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarta ya sake kira, da tsawa ta dauka da niyyar cimai mutunci, muryan nan dai ne, yace "Nana Nakowa, you'll apologise to me,ba a min ihu, ba a daga min murya, ba a zagina,apologise for calling me stupid, and finally ki gaya min mai Majeed zaije yi Dubai, i wont ask again". Tayi daria tace " i like your confidence, so ka matseni ka sani in fada maka" yayi murmushi yace "ba zan matseki ba, da kanki zaki gaya min, or maybe zaki ba Nimcy ko Salim su fada min". A firgice Nana ta kalli Nimcy da Salim din dake kan Gado suna aikata Alfasha, baki na rawa tace "ina ka sansu?" yayi daria yace "kina nufin ina na san Kwarton ki? Da dadironki Nimcy, duk Kano be isheki ba ke da Salim sai da kukazo Jigawa wurin Nimcy?, what will happen if Majeed gets to know his Wife is a hypocritical b*itch Ehh?". Da sauri tace "No,No, donAllah kayi hakuri,don't tell him, Zan gaya ma all you want to know".

"Good, ina jinki" tace "Majeed zaije yin wani Interview ne a HILAL Construction Company on Monday, shine yazo Abuja neman Visa" Zaid ya jinjina kai yace " in har kina son cigaba da zama da Majeed, dole ki bar akuyancin nan, ki tashi ki koma Kano yanzu, and zan dinga kiranki if i need anything concerning the Abba Abu's,you are to keep me posted kan duk abunda ke faruwa a cikin Gidan, and duk me na tambayeki ina son Ansa, ki ka kuskura kika gaya ma wani kuna communicating da some stranger, consider that karshen zamanki da Majeed, don zan tura mai pictures dinki ke da mutanenki, so go home now".

"Wait donAllah mesa kake son sanin Details din Gidan Inlaws dina, please dont harm anyone, and please kar ka tona min Asiri, na bari, in kudi kake so zan baka ko nawa kake so, dont just harm My MMajeed" Zaid yayi dariya yace"Nana Nakowa, ina da kudin da zan siya Alhaji Nakowa, da duk abun da ya tara, Money aint my problem,so get your p*nties on, and go home". Dif ya katse wayar. Nana sai zufa, Nimcy da Salim na tambayarta me ya faru tayi shiru ta k'yalesu, da azama ta sa kaya ta gyara jikinta ta ja Akwatin ta ta bar Gidan, kwanan da batayi ba kenan.

B A Y A N WASU K W A N A K I

I N D I A

"Najwa Nigeria k'asa ce mai girma, nasan dai be kai birnin Delhi ba, amma akwai Dumbin mutane, kar ki sake ki yarda da kowa, people there are manipulative, zaki gansu kamar na gari, Wallahi kar ki yarda dasu, kar ki sake ki gaya ma kowa sirrinki, kar ki sake kice ke bak'uwa ce kinzo neman Yayanki wani na iya cewa ya sanshi ki bishi ya tafi dake ya sayar dake a banza, I repeat dont trust anyone with your secrets, idan kun isa Lagos, ki siya Ticket din Kano, Kano tadabo, anan zaki fara binciken ki, komai zaizo da sauk'i InshaAllah, yauwa ki siya Simcard, ki saka a waya sai ki kirani, zan gaya miki what to do next". Najwa ta gyada kai alamun ta fahimci komai. Sosai ta mata Godia, don ta taimaka mata Sosai, ta san abubuwa da dama game da Nigeria sanadiyar Aisha.

Gobe tafian Najwa, jirginta zai tashi k'arfe Shidda na Asuban Yau, Tsoro ya dira Zuciyan Najwa, ta rasa sukuni, tun ana Gobe tafian, ba zama, tayi nan tayi nan, ta hahhada Akwatin ta da School bag wanda cikin Laptop dinta ne, ta faki idon Maama ta Kai Shagon Vijhay Bhaiya, har bayan Maghrib tana gidansu Kaveri, Sun yi kuka sosai don zasu missing suna, Najwa ta shaida ma Kaveri kar ta damu, zasu dinga waya kullum. Haka suka rabu.
11pm
Tana jin shigowar Maama da Paapa dakinta, daidai kunnenta suka tofa mata adduar kariya, suka manna mata kiss a kumatu kafin suka gyara mata bargon da ta duk'unk'une dashi, suka fita. Hawaye ya sauko ma Najwa, tausayin kanta, da na Mahaifanta suka diran mata, ina ma ta fasa tafiyar, ina ma ta kasance da Mahaifanta daga gobe har abada? bata da mafita dole taje Nigeria, balle aski ya zo gaban goshi, daren yau ne tafian, duk yanda ta so tayi bacci kafin Alarm dinta ya tasheta k'arfe 4 ta kasa, haka tayi ta juyejuye tana kuka, da ta ga hakan ba zai amfaneta ba sai ta tashi ta dauro Alwala tazo tana nafiloli.

Kirrrr Alarm dinta ya k'ila, ta kashe tare da mik'ewa ta yana gyalenta akai, Wani kwarin guiwa takeji Yanzu, wayar ta ciro ta kira Numbern Vijhay, tace ""kya aap so rahe hain(bacci kakeyi?)" yace "Nahi (Aa)" tace "kaar taiyaar ho jao,main ab baahar aa raha hoon (ka shirya Motan, gani nan fitowa)" yace "Theekhai(Okay)".

Cikin sando ta shiga Dakin da su Maama ke bacci, ta tsura ma Mahaifanta idanu hawaye na bin kuncinta, ta murmusa ta karasa gadon ta zauna gefen Maama, ta lalubo hannunta ta rik'e, cikin hawaye ta fara magana " Maama forgive me! I cant see you in more tears, Zanje Nigeria, i'll look for my Brother, i'll find him and i'll bring him home, I promise". A hankali Maama ta bude idonta, ta kalli Najwa ta murmusa kafin ta maida idanunta ta rufe, Najwa ta durk'usa ta sumbaci Maama a goshi, kafin ta matsa gun Paapa ta mai kiss a goshi tace "ka kula da Maama kafin na dawo kaji? Allah ya hada mu da Alherinsa. Ta ciro farar takkada da tayi rubutu a ciki ta ajiye musu kan bedside drawer. Tayi Bismillahi tawakaltu Alallahi wala haula wala k'uwata ila billah" ta bar Gidan. Ta shiga Motar Vijhay tana kuka, shima idonshi ya kawo hawaye be ce mata komai ba, daidai gidansu Kaveri ta mata text "Byebye meri dosti". Suka kama hanyar Airport.
Bayan sun yi boarding da komai, suka rabu da Vijhay bhaiya, bayan sun sha kuka tare, ta shiga Jirgi ta samu wuri ta zauna, bayab
clearance Jirginsu ya tashi zuwa k'asar Dubai inda zasuyi transit, su chanza Jirgi kafin Jirginsu ya tashi zuwa Lagos Nigeria. Tunda Najwa ta shiga Jirgin nan har suka isa Dubai Kuka take tayi.

D U B A I INTERNATIONAL AIRPORT.

Suna transit wurin 8:25am. Ta je wurin da ake buga International calls, sai da ta kira Kaveri, kafi ta kira Aisha, sannan ta Kira Mamma.
10:40 am suka fara Boarding Jirgi, har yanzu kuka takeyi, fuskarta tayi Ja,duk da wayar da tayi da Maama hankalinta ya kwanta, amma tana cike da tsoro, dagasken dai ta bar Gida, Allah ya taimaketa, har ta zauna kan kujerar Jirgi kuka takeyi, da ta tuno wani Abu sai ta fashe da kuka, alamun zama da akayi a gefenta ne ya sa ta share hawayenta, tashi tayi ta mai Alama da zat wuce ya gyara ta wuce toilet ta wanke fuskar ta, ta bi Mutanen da ke zaune a Jirgin Emirates, yawanci bak'ake ne 'yan Nigeria, ko don kasar su a ka nufa? Oho, ta dawo ta zauna.

Na kusa da ita ta ji yana waya cikin kwanciyar hankali "Hello, ya Exams? Ayyah Allah ya bada saa, No ta lagos zan sauka, kinsan ba ta Abuja na tashi ba, eh, InshaAllah, ki maida hankali ki gama Jarabawan, Allah bada Saa, Ameen Nagode" ya latse wayar ya sake lalubo wani numbern "Hello, yanzu zamu taho, Ameen ya Allah" yana ta waya har aka bada umurnin kashe Waya Jirgi zai tashi, hankalin Najwa ya sake tashi, ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi wanda na zaune da ita sai da yaji karan kukanta, a hankali ya juyo dubanshi gareta, be san meya sata kuka ba, amma bari ya barta. Haka ta cigaba da kuka na tsawon lokaci.

Da ya ga bata da niyyan tsayawa sai ya dan tabo hannunta, ta dago tana zubura baki tana goge hawayenta da tafin hannunta, gani daya sai ta mishi kama da kanwarshi idan tana shagwaba, da ta lumshe idonta ta bude sai ya ga ta mai kama da dayar kanwanshi idan an bata mata rai, sai ya murmusa tare da zaro hanky a jikin Aljihunshi yace "Kin dade kina Kuka, kukan ya isa haka, Oya share hawayenki, biggirls dont cry Ok?".

*******
Hey Fans, what just happened? I cant believe it, Waye wannan? Kar kuce mun sun hadu, su waye suka hadu yanzu, Guess muga ko daidai ne.
Next page zamuji yanda me Najwa da Maama suka tattauna akai da ta kirata waya.

Najwa Welcome To Naija.

Gaskia Akwai Ghost readers cikin masu karatun nan, donAllah ku taimaka, yanda nake faranta muku rai, donAllah nima ku faranta nawa by b and Commenting.

#1love
#ADAY
#bibiliciousfreakingfans
#anatare
#gwslubnasufyan
#Nagode.

Biebee Isa
[12:11, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Wattpad:@biebeeisa

Pg1鈨�7鈨�

Kyafta idanuwanta tayi sau uku kafin ta sauke su fes kan Mutumin da ke kusa da ita sannan ta saukar da dubanta ga handkerchief din da ke rik'e a hannunshi, mika mata ya sake yi, ta sa hannu ta karba, ta goge hawayenta, ya mata nuni da hancinta inda Majina ke zuba, ta dan ji kunya, haka ta goge kafin ta k'wak'ulo murmushi.

Maida dubanshi yayi ga TV din da ke gaban Seat, ya gyara zaman headphones a kunnenshi.
hankali a hankali take jan majina, ba ta damu da kallo ba, abunda ke dawainiya da ita ya fi karfin Kallo, tana sheshek'a, hawaye na bin kuncinta har bacci barawo ya saceta.

I N D I A
5:45am

"Yesmeenah, yau Najwa ko bata Sallah ne? Banga ta zo gaida mu ba" daria Maama tayi tace "Yanzu da gabanta ka fada hakan da taji kunya, wai ko bata Sallah ne, haha, tana yi fa, k'ila ta makara, ko bayan Sallah ta idar bacci ya ci k'arfinta ta koma" ya mik'e tare da cewa barin dubota.

Ko da ya bude dakin Najwa be ganta ba, sai Pooh da ke ta bacci kan Gado, ya dawo yace "ta tashi, tana toilet" Maama tace "Oya kazo ka kwanta kafin na tada ka Shirin Office" murmushi yayi ya haye Gado ya kwanta ya bar Maama kan Gado tana Adhkar.
Chapter 29 · 0% Book details