← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 128

Sashe 72

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaid yayi jim yana kallan wayar,聽 takaicin Baba Ado yaji,聽 don me zai kirashi? Me zaije ya musu? " Idi yace "Oga ka shiga kawai,聽 Allah ya soka Baba Ado ya baka Manyan kaya kasa, lafiya lau ne, ka shiga kawai,聽 remember聽 gaban sirikin ka kake,聽 banda kallonsu cikin ido,聽 kuma a kasa zaka zauna" tsaki Zaid ya buga da karfi ya bude kofa ya ma su Amrstrong banging da karfi,聽 suko suka fashe da daria,聽 cikin Gidan yayi,聽 gidan ba bakonshi bane, takalmominsu ya gani daga waje,聽 yayi Sallam ya shiga suka amsa mai,聽 a k'asa ya zauna kamar yanda Idi yace, murya cikiciki ya gaida Daddy,聽 Daddy da faraarsa ya amsa.

Baba Ado yace "MashaAllah,聽 Alhaji Abba ga Yaronmu,聽 durfane gabanka, yazo neman auren diyarka,聽 be zo a matsayin Gatan Marayu na biyu ba, yazo ne a matsayin聽 Zaid Sadam me son diyarka Ziyada" kan Zaid a kasa,聽 yanda yake magana sai yake jin wani nauyi na sauka a kansa,聽 anya zai iya kuddirinsa? Kafin Daddy ya bada amsa Abdulmajeed ya shigo dauke da Lemuka su coke fanta mirinda a talauce (waya ce maka suna shan irin wanan? lol).

Alhaji聽 Abba yace "ga Baban dana,聽 yayan Ziyada聽 ne,聽 sunanshi Abdulmajeed" Abdulmajeed聽 ya dirr lemukan a k'asa ya sake gaidasu,聽 suka amsa da faraa,聽 Daddy yace "AbdulMajeed,聽 je ka kira min Mummynku da Ziyada,聽 inshort ka kira min kowa da kowa har Mama" Abdulmajeed聽 ya mike a ladabce ya fita,聽 a dakin Hajjo ya iskesu duka,聽 yace "Mummy kuzo Daddy na kira" jiki na rawa Mummy ta zaro聽 mayafin da bata san ko na waye ba zata fita Abdulmajeed聽 ya tareta,聽 yace "tsaya Mummy,聽 gabaki daya zamuje,聽 Zaineema ku muje,聽 Hajjo har ku" duk聽 suka tashi聽 suna neman mayafin sakawa banda Ziyada da ta takure wuri daya,聽 Abdulmajeed聽 ya kallota ya bude drawer ya ciro wani k'aton gyale ya rufe mata jiki yace "come on zuzu, ba zaki bar surikanki suyi ta jiranki ba ko?" ta mike聽 jiki ba kwari,聽 Abdulmajeed ya ja hannunta suka fita, duk suka rufa musu baya banda Najwa da ta ke聽 gyara inda su Muhsin suka 6ata.

Sallama sukayi suka shiga,聽 suka amsa聽 da faraarsu,聽 duk suka samu wuri suka zauna, kan Ziyada a k'asa,聽 Baba Ado ya nuna ta da yatsa yace "ga Amaryanmu nan" ta sake sadda kanta k'asa,聽 Daddy yace "haka ne, nan Iyalai na ne dukkansu,聽 Wannan itace Mahaifiyata,聽 wannan kuma Mai dakina" ya nuna Mairo da hannu,聽 ita ko sai faraa take watsa musu"聽 wannan kamar yanda na gaya muku shine babban da na AbdulMajeed,聽 sai me bi mishi Zaineema,聽 sannan Ziyada,聽 Zinatu ke bi mata sai auta Muhsin" Alhaji Ado yace "MashaAllah,聽 Allah ya ja kwanan zuria,聽 matuka kun burgeni,聽 ka nuna mana dattako da karamci,聽
Hak'ika hankalin mu zai kwanta ganin gidan da yaronmu ya dauko mata" Daddy yace "haka ne, amma bari mu ji ta bakinsu ko?".

Alhaji Bello yace "Zaid, shin wannan itace ka zaba ta zame maka abokiyar rayuwa har karshen rayuwarka?" be san dalilin da yasashi faduwar gaba ba, yayi shiru gabanshi na dukan chalugude, baba Ado yace "Zaid?" da sauri yace "Eh itace". Daddy ya juyo kan Ziyada yace "Ziyada kin amince in bada aurenki ga Zaid? Kar kiji nauyi ko wani abu in ba kya so, sai in basu hakuri, ki fada min ranki, farincikin ku ya fiye min komai" Ziyada ta sadda kanta kasa, Daddy yayi maganan duniya amma tayi shiru ba tare da ta tanka ba, yace "ko ba kya so?" nan ma shiru tayi, Alhaji Bello yace "Ziyada magana zakiyi kinji? Ba zamu gane me ke cikin ranki ba in ba magana ko alama kika mana ba, kina son sa, ko ba kya sonsa?" shiru tayi har yanzu ba tace komai ba, Mummy ji take kamar ta gwala kan Ziyada da bango, Alhaji Sani yace "kun san dai ma'anar shirun budurwar kirki, yana nufin ta amince kenan" Alhaji Kabir yace "aa kar ayi saurin yanke hukunci, duk tambayar da aka mata shiru tayi, ya kamata musan amsarta, muna iya bata lokaci tayi tunanita gaya mana sirrin da ke ranta".

Abdulmajeed yace "Erhm, in zan dan iya magana da ita, zan samo mana amsar da takasa fada" Daddy yace "Eh Abdulmajeed kuje kuyi magana" hannunta yaja suka fita daga Parlorn, Daddy ya musu alamu da su bisu, su Mummy suka tashi suka tafi, be san meyasa yaji gabanshi na faduwa ba, what if tace bata sonsa? Plan dinshi ya zube kenan? Plan kadai? Cewar zuciyarshi, da sauri yace "eh, plan dina ne kawai, be san mesa ba amma sai ya tsinci kanshi da yin adduan Allah ya sa ta amince.

"Zuzu lookat me, talk to me, kina sonshi? " cewar Abdulmajeed, da sauri ta kallo yayanta tace "YaMaji, a cikin halin da muke ciki, maganar aurena shine karshen abunda ya kamata ayi, muna cikin halin ha'ulai, Ya Maji--" ya katseta da cewa "shhhh, ki amsa ni, kina sonshi?" rungumeshi tayi da sauri tana gyada kanta a jikinshi, yayi daria yace "abunda nake sonji kenan" ya juya ya tafi yayi Parlor, ya rada ma Daddynsu a kunne, Daddy yace "to Alhamdulilah, yarinya ta Amince" duk sukayi hamdala suna faraa, Zaid ya sauke numfashi a hankali yana gode ma Allah.

Alhaji Ado yace "Alhaji Abba ka bamu?" Daddy yayi daria yace "na baku" sukayi daria sukace "mun karba kuma mungode, muna so ayi Auren Ran Juma'a me zuwa in Allah ya kaimu" Daddy suka kalli juna da AbdulMajeed, Daddy yace "Alhaji, da wuri haka? Ni ina zaton sai daga baya zaa sa bikin kuma zaa sa a kalla wata 10" Alhaji Ado ya zaro ido yace "Wata Goma dai? Me zaa jira Alhaji tunda yara na san junansu, ka bamu kuma mun karba? Me zaa jira?" Daddy yace "haka ne, amma akwai wata yar matsala da ta auku, ina neman Alfarma a bamu lokaci mu maganceta kafin ayi ma maganar daurin auren yaran" Alhaji Ado yace "nasan kana so kama diyarka kayan daki, nasan kana so nyna bajintarka a matsayinka na Baban yarinya, nasan kana so kamata kayan daki kamar yanda ko wani uba yakr ma diyarsa, amma Ba fin karfi, ba nuna isa ba, ba ma bukatar komai, Yarinya muke so kuma kun bamu, ita ral muke so a daura aure Yaro ya dauki matarshi ya kaita Gidanta" Daddy zaiyi magana Alhaji Ado ya katseshi da cewa" Gatan Marayu na farko ya kan daura ma Yara 100 aure a rana wanda be sani ba fa, ya musu lefe ya musu kayan daki, to me kake tsammamin zai ma Yaronshi in ya tashi aure? Ka na tunanin zai barsu su siya koda kara ne?" Daddy yayi jim kafin ya kalli Abdulmajeed neman shawara, da ido ya gyada mai kai Alamun ya amince, Daddy yace "haka ne, toh Allah ya saka da Alheri, Allah ya kaimu Jumaa din" Alhaji Ado yace "Ameen, ba shishigi ba, amma wata irin matsala ce da kuke son magancewa?" Daddy yace "ba wata damuwa bace, kar ku damu" Alhaji Ado yace "haba Alhaji, tunda ka bamu diya ai an zama daya, ka gaya mana ko menene".

Daddy ya yi shiru kafin yace "Akwai Alhaji Nakowa da muka samu sabani dashi--- tiryan tiryan ya kwashe labarinsu da Alhaji Nakowa zuwa yau" Allahu Akbar, Zaid dai duk wani guiltiness ya kamashi, be taba jin tausayin mutanen nan ba ko kadan amma yau da Daddy ke bada labarin sai yaji wani bangare na zuciyarshi na tausaya musu, da sauri gudan zuciarshi ke mai gargadi da kar ka sake kaji tausayin Azzaluman nan da suka maka katangar karfe da mahaifanka, da sauri ya yakice tausan da ke ranshi, be ankara ba sai ji yayi Alhaji Ado na cewa "Alhaji Abba, tunda yanzu an zama daya zan bada Miliyan 30 din ku biyasu" Daddy yace "gaskia ba zan amince ba, abun ai sai yayi yawa, gaskia ba zan yarda ba, abin da kukayi ma mun gode Allah bada Lada" Alhaji Ado yace "Haba Alhaji Abba, ashe baka yarda an zama dayan ba, to in ba mu ma Zaid ba wa za mu mawa, na gaya maka duk nan ba wanda be ci albarkacin Gatan Marayu ba, duk abunda muka mishi ko danshi bamu fadi ba wallahi" Zaid kamar ya makure Baba Ado, ya sanshi da kafiya, biya musu bashin nan na nufin basu da wata damuwa, meyasa yake da shishigi ne? Tsaki yake ta bugawa a ranshi yana cewa shifa baba adon nan da matsala yake, shi kuwa Daddy ya san cewa in suka rasa tallafin nan ba wanda zai sake tallafa musu, this is the only chance they have, amma be bi san zucianshu ba yace "duk da haka , kuyi hakuri we are not your responsibility, in sunyi aure duk abund zai mata ba me hanashi matarshi ce".

Ganin ba zai amince ba dabara tazo ma Baba Ado, yace "to in ranta maka mana? Da bashi a kan mutane irin Alhaji Nakowa gwara gida ko? Zan ranta maka, in ka samu sai ka biyani" Daddy yace "to ina iya amince ma rance, amma gaskia ba kyauta ba, kuma 25million ne, don mun basu 5, zan dinga biyanka a hankali a hankali" Zaid kamar yayi Ihu don haushi, yasan siyasa Alhaji Ado ya mai, ya san ba zai taba karban kudin ba, shikenan ya yanke musu wahala, kamar yayi kuka, nan dai suka cigaba da tataunawansu cike da mutunta juna, Alhaji Ado yace "gobe zaayi banking a biya Alhaji Nakowa kudinshi, Alhaji Bello yace bayan daurin Aure zaayi gagarumin walima" Alhaji Sani ya ciro rafar 1000 guda uku yace "ga Sadakin Amarya" duk abubuwan da akeyi bakinciki ya turnike Zaid, shifa neman aure yace su zo su mishi ba san iyawa ba, be san lokacin da ya mike ya fita ya bar parlorn ba, ba su damu da shi ba don ba su ma lura da ya fita ba, ba jimawa suka tafi.
Chapter 72 · 0% Book details