← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 128

Sashe 116

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

"PureHeart na fuskanci cewa you are so innocent, and naive, zuciyarki me sanyi ce, in miki na wani Rafeeq Lema, yace "Baki da hayaniya, baki da damuwa" Najwa ta murmusa ta cigaba da kallonsh. Ya cigaba "Abun ne ya zame min biyu, Son 'yanuwantaka, da kuma So mai wuyar fassaruwa, Najwa, ina sonki, ina k'aunarki, akwai abubuwa da yawa da suka faru a baya, kuskuren Mahaifiyarta, ban san ko zaki dinga kallona da abun ba, ina--" katseshi tayi ta hanyar cewa "shhh, Jaaaan, ka bar maganar nan, kamar nace maka maganar nan ta wuce kar a sake dawowa da ita? Nace maka a bar abunda ya faru a baya, a maida hankali kan abunda zai faru a gaba. Bansan irinka ba, irin zuciyarka kadan ne a duniyarmu, kai Namiji ne da ko wace mace zatai burin Aura ko burin Samu, ka hada komai, to me zan jira? Me zai dameni? Ina da kai fa? Meri jaan, tumase pyar kharta---" bata karashe abunda tayi niyyan fada ba yayi saurin rufe mata baki yana girgiza kai, yace "Aa, aa donAllah, wannan Indiyancin na k'warata, karki boye min, ki gaya min da yaren da zan gane, PureHeart, ki fada min, ina so naji donAllah" runtse idonta tayi ta fara magana "Ina Sonka Ya Majeed, wallahi ina sonka, ina so na karashe rayuwata da kai, bansan me zanyi ba in babu kai, ba kyaun fuska kadai gareka ba, kanada kyaun zuciya, ina sonka da duk wata jijiya dake cikin jikina, ina sonka da duk wani Jinin da ke gudana a jikina, ina sonka da duk wata na'urar dake aiki a jikina".

A hankali ta bude idanuwanta ta saukesu fes kan Abdulmajeed da bakinsa a hangame kamar yaga wani abu, mamakin kalamanta yake, be taba zaton tahi hausa har haka ba, babu cikin abunda ta fada wanda be shigeshi ba, sak'on da ta aiko mishi ya k'arba, ya kuma so ya maida mata ta martanin da zai fi baiyanar da abunda yake ji a ranshi, sai ji yayi ma jikinshi yayi sanyi, ya gyada kai, yace "Najwa, Allah shine Shaidana, ina sonki Dominsa" Murmushi me k'ayatarwa ta sakar mai, ya mike jiki ba kwar'i yace "bari naje na dauko Yara" Murmushin dai ta sake mai tace "muje nima ina zuwa" be ce mata komai ba yayi gaba, ta dauko Hijab din Sallahnta ta bi bayanshi.
A parlo suka iske Ziyada tana ta Murmushi ita kadai, abunda ya faru tsakaninta da Zaid dak'iku da suka wuce yana sata nishadi, Abdulmajeed yace "Yadai Zuzu?" shashantar da maganar tayi don ya bata kunya ta hanyar cewa "Ina zuwa?" Najwa tace "Su Zeenah zamuje daukowa a School" Ziyada ta mike tace "nima zanje" yace "Aa, je ki gaya ma Mijinki" shagwabe fuska tayi tace "YaMaji fa yana cikin dakin Mama tun dazun fa" Shiru yayi kafin yace "Keke Napep fa zamu hau, su Paapa sun fita da Motar" Ziyada tace "Ooo, inada Miji kamar ZSA dangi na zasu hau Napep? Muje waje akwai Drivers" Najwa ta kalli Abdulmajeed suka tabe baki a tare suka ce "Ahhh Allah ya baki hakuri Matar ZSA" daria tayi tace "ku fada ku k'ara" muje tayi gaba, suna binta a baya Najwa ta bude murya yanda su Zaid zasu jita tace "Maama mun tafi dauko su Zinatu"..
***

Hannunsa ya cire zai rik'o nata, da sauri ta janye kamar wuta zai tabata, da mamaki ya kalleta, ya k'ara kai hannu zai ta6ata, da sauri ta sake daukewa, nan ya gane abunda take nufi da yin haka.
Ya kalli Driver yace "DonAllah kayi parking ka dan bamu wuri zan yi magana da matata" ba musu Driver ya samu wuri yayi parlking ya fita, Khaleed ya sausauta murya yayi yace "Zainee Nah, kina fushi dani ne?" banza tayi dashi ta kawar da kanta gefe, hannunsa ya sa ya juyo da habarta yanda zasu fuskanci juna yace "ki min masifa, nayi kewan fadanki, ki min" shiru tayi sai ma ta kawar da kanta gefen windown mota.
Dungurin kanshi ya farayi yana marin kanshi, hakan da yakeyi ne ya jawo hankalinta gareshi,
Lankwashe murya yayi kamar ita yace "Don me Dee? Ashe baka yarda dani ba? Ashe in duniya zasu zargeni da mummunan zargi zaka tayasu gurin zargina? Ashe ba son gaskia kake min ba? Baka yarda dani ba? Baka tsaya kaji ta bakina ba? Kayi watsi da komai ka sakeni? Ka wahalar dani? Ka maidani bazawara" ya cigaba da dunguri da marin kanshi har sai da Zaineema ta fara kuka tana dukkanshi a kirji ya daina, be hanata ba, kuka take tana dukkan kirjinshi da hannu biyu tana cewa "Dee, ka wahalar dani" dama zai iya kuka da yayi, yace "Zainee nah, na sani, kiyi hakuri, ki dauka hakan a matsayin ajizanci na dan adam, kowa a matsayina zaiyi abunda nayi, abunda ya wuce ya wuce amma ki min uzuri, nikuma zan nuna miki yanda nake sonki, da yanda nayi kewanki, kinsan ina sonki, and i miss you so much" hawayenta suka k'ara yawa ta gada jikinshi, shiko ya rungumeta, tana kuka a kan kafadunshi, ita tasan tana son Khaleed sosai. Shafa bayanta ya shiga yi yana cewa "Ki bar kukan nan, kinsan banaso" tunawa tayi fa basu da aure yanzu, a hankali ta dago daga kan kafadunsa, yayi niyan sake rungumarta ta yi daurin cewa "Ba fa a daura mana auren ba" Khaleed ya dafe kanshi yace "Ya Illahi, now i cannot even hug my wife" dariya tayi tace "Nope!" turo baki yayi ya dan tashi ya ratsa ta kujerun gaba ya ma driver horn alamun sun gama. Driver ya dawo Motar ya ja ba tare da sanin inda suka nufa ba.
*****

Maigadi ya sanar da Hajia Aynarh tayi bak'i maza, ganin akwai mayafi Jikinta ya sa tace "su shigo" bata fasa filing nails dinta ba suka shigo da Sallama, Murmushin su ya fadada, mazauni suka ma kansu, ita ko ta gyara zama yanda zata fuskanci masoyinta yanda ya kamata, bayan 'yan gaishegaishe, ta mik'e don kawo musu abinci, Daddy ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Aa Hajia Aynarh, mun hutassheki" Zama tayi tana fari da ido. Sada yace "To Hajia, dama so muke ki gaya mana inda zamuje neman aurenki, don ki zautar da Yayana, ko gaban Yara ne maganarki yake" daria tayi, ta sadda kai alamun taji kunya kafin tace "yawancin danginmu suna Kwara, but akwai uncle dina, Baba Abdoulfatah, a Kwanar Ganduje, shine madaurin aurena, shi ke aurar dani, a Gidanshi ma nayi Karatu, ya dade a Kano yana aiki bayan yayi retire be koma chan garinmu ba.
Sada yace "to sai ki bamu Address da numbernshi mu biya mu kai gaisuwa, da kuma Buhun doya nawa zamu kai na neman aurenki?" dariya Daddy ya sa, ita ko throwpillow ta dauko ta wurga ma Paapa "Wallahi Sada ka rainani, da buhun doya zaaje neman aurena?" Dariya suke sosai.
**
Tana dan kishingide taji muryan Daddy, to me yake a nan? Ta tambayi zuciyarta, k'ila yazo maidaki dakinki ne,da sauri ta tashi ta nufi Parlo da Sallama, amma kunnenta ya jiyo mata wani abu kafin sallamarta, "Wallahi Sada ka raina min Aynarta, to dole ka aje wasan k'anin mijinnan, ba zan yarda ka raina min Amarya ba" wani Yammm kanta yayi kafin ta fara jin idanuwansu a kanta, sun lura da ita, da mamaki suke kallonta, banda Hajia Aynarh da ta dauke ido, Daddy ya dan cin face ya kalli Aynarh yace "me takeyi a nan?" a takaice tace "Kwana" kafin waninsu ya k'ara magana tuni Hajia Mairo ta tako har gabanshi "Haba Daddy, haba Daddy, kana Fulanin usul, me jinin shuwa arab, me zakayi da Bayerabiya, Yoruba fa, Daddy dama sonta kakeyi?" duk da ba wai cikin tashin hankali tayi maganan ba, amma sai yaji ranshi ya 6aci, dubi matar nan, har tana da bakin magana, bayan abubuwan da tayi? Lallai bata da kunya, Banza yayi mata, tace "Daddy nafa ce na tuba, donAllah ka maidani dakina, na chanza, zamu zauna dakai da yaranmu lafiya, ba sai ka sake Aure ba, donAllah Daddy" bakinsa ya ta6e, Hajia Aynarh ta mik'e ta kalli Sada tace "Ka gaida Yesmin, ko kallon Daddy batayi ba tayi hanyar daki" meke nan? Kishi ake a kanshi? Daddy wani dadi yakeji amma be nuna ba, yace "kai tashi mu tafi" Mairo tace "Sada DonAllah ka bashi hakuri, wallahi na chanza halina".
Chapter 116 · 0% Book details