← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 128

Sashe 27

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

聽聽 Bayan kwana Biyu Motar kwasan kaya 3 suka kwashi kaya don tafiya da shi Kano, ranar Mairo da 'yayanta sun ci kuka, ganin zasu bar Wannan wurin da sauke kira 'HOME' Mairo ji takeyi kamar rayuwarta na gab da k'arewa, suma suka shirya suka kama Hanyan Kano banda Majeed da Daddy da sukayi branching a Kaduna inda zasu tsaya gun Mijin Zaineema, tunda sun ta kiranshi a waya baya dauka.
*
聽 聽 Khaleed na Parlor yaji Sallaman Amininshi AbdulMajid Abba da Abba, ba yanda ya iya Illa tarbansu a mutunce, bayan gaisuwa, Majeed ya k'are ma Khaleed kallo, sosai ya rame, yayi baki, tausayinshi ya kamshi, ya san yana son kanwar shi Zaineema. Majeed yace"munzo ne muji abunda ya faru tsakaninka da Zaineema,ta rantse mana da Allah, khalid wallahi sai da ta rik'e Izifi Sittin ta rantse da Allah kan cewa bata da masaniyan abunda ya faru" Khaleed yace "AbdulMajid kasan yanda nakeson Zaineema ai? Ba zan mata sharri ba,wallahi da idona na ga kwarto a dakinta kwance kan Gado" Abba ya runtse ido, yace "Mallam Khaleed, kai ka ga abunda Ka gani, ba zamu k'aryata ba, amma tambaya daya da zan ma, shin ka gansu kwance kan Gado tirmi da tabarya?" Khaleed ya girgiza kai Abba yace "Manzon Allah yace Shaidan da ake zargin聽 Mazinata da aikata Zina, shine a gansu kwance turmi da tabarya, Khaleed ba wai na karyata ganinka bane, amma ba ka tunanin akwai abokan gaban da suke son ganin bayan aurenku? Baka san hassadan mai hassada ba? Baka san sharrin me sharri ba?" Khaleed zuciyarshi ta kasu kashi biyu, daya ta na son gasgata Hujjojin Daddy, daya kuma yana hanashi yadda da hujjojin, inda take cewa "Babanta ne, zai iya cewa komai don ganin ka maida diyarshi dakinta" ya dai muskuta yace "Daddy, kasan ba aure in da Zargi, jin nauyinku ko duba Alakata da AbdulMajid bazai sa in kwari kaina ba, tsakani da Allah ban yarda da Zaineema ba, duk da ban taba kamata da wani hali ba kafin wannan, ba zan maida Zaineema daki na ba, sai na ga k'wakwarin hujjan cewa wannan ba ita ta kawoshi ba, kuyi hakuri donAllah, ina son Zaineema amma son ta ba zai sani makancewa ba". Daddy zaiyi magana Majeed yayi saurin cewa "Gaskia ne Khaleed, Allah ya baiyana gaskia duk inda take" Khaleed ya amsa da Amin, ya san Majeed me saukin kai ne, Majeed yace "bari mu tafi, a hanya muke" *nan da Abuja dai?" "Aa mun bar Abuja Kano mu ka nufa" nan sukayi Sallama.
*
Gidan dai na nan yanda yake, ba abunda ya samu gidan, shara kawai akayi akwa wanke gidan don da ma su kanzo hutu, suka jera kayyayakin su, da Majeed suka iso ya samu Zaineema a daki ya mata Nasiha da ban hakuri, Mummy ta gama banbaminta tace "ko shine autan maza ya gama aurenta" Zaineema tace "Wallahi sai dai in be dawo ba" Mummy tace "mara zuciya" Zaineema ta murguda baki tace "naji din".

I N D I A

Maama ta lura聽 da Dadin da Najwa keji, da ta tambaye ta me ya sata farinciki sai tace " kawai dadi nakeji" sai tayi daria tace "Najwa ina son dariarki" ita kuwa sai tayi darian.
Gaskian lamari Waya sukayi da Aisha Danlami, inda take shaida mata zata zo makarantarsu, tace "zan shiga Aji amma 12:00pm zan gama" Jira takeyi 12 tayi ta tafi Jami'ar su Aisha, kafin lokacin ta tsaya sai hotuna take tayi. 12 na bugawa na ma Maama k'aryan zuwa Gidansu Najwa.
聽聽

锟�

Tafian minti 45 Najwa tayi, bata sha wuya ba ta gane Hostel din mata, sukayi waya da Aisha ta gaya mata inda take, Aisha ta sauko suka hadu tare da rungume juna, suka tafi dakin Aisha, Aisha ta dafa musu Noodles sukaci tare, in ka gansu sai kayi zaton sun dade da sanin Juna.
Najwa tace "Aisha tell me About you" Aisha tace "lol, sunan Aisha Danlami, 'yar Nigeria ce, I'm 18years, last 2weeks nazo India, Karatu ya kawoni, i miss home" Sukayi daria sosai, kafin Najwa tace "wani gari kike a Nigeria?" Aisha tace "Katsina" Najwa ta maimaita sunan gari tace "Nikam States nawa ne a Nigeria? Aisha tace "36 states" Najwa tayi shiru ta na wani tunani. Aisha tace "Baki gaya min ba Najwa, ta ya kika iya Hausa, India, English" Najwa tace "Well, Iyayena Yan Nigeria ne, but anan muke zama, as a matter of fact, a nan aka haifeni, so i was born and raised here" Aisha cike da doki tace "Ashe ku 'yan Nigeria ne, yan wani gari ne ku?" Fuskan Najwa ya chanza tace "Wallahi I dont know" Aisha ta kalleta tace "how comes baki taba zuwa bane?" Najwa ta gyada kai tace "i've never been there" Aisha tace "atleast zakiji Mamanki ko Babanki na fada" Najwa da fuskan tausayi tace "they cant remember, kawai sun san su yan Nigeria ne, and ba sa iya zuwa, ko sunyi shirin zuwa, sai su kasa wani abu na faruwa da su one way or the other sai suji sun kasa zuwa, tunda aka haifeni har yanzu." a takaice Najwa ta bata labarinsu da k'uddirinta na zuwa Nigeria, Aisha tayi shiru tana sauraron Najwa da tausayi tuni ta dago bakin zaren, Najwa tace "Shiyasa nazo ki dan yi min Bayanin yanda Nigeria yake, saboda zanje neman Yayana, kinga Kullum Maama na cikin zubar da hawaye take".聽
Aisha ta ja iska ta fesar tace "Najwa, ga yanda naji labarinki, sai na san cewa Aikin Asiri ne ke cin Mahaifanki" Najwa ta maimaita kalmar 'Asiri' tace "menene hakan?" Aisha tace "Sihiri" Najwa ta girgiza kai tace bata san meye hakan ba.

Aisha tace "I really dont know how to explain this to you, But Sihiri is more like Witchcraft, like someone can cast a spell on you, and make you do things you dont want to kingane" Najwa tayi shiru tace "I know Witchcraft, i know people do Cast Evil spell on others, but i dont think such people exist" Aisha tace "Tabdijam,ai Nigeria Gidan yi ma mutane Asiri ne, Let me tell you how聽 most Nigerians are like; da kinji Mijinki zai sake mata sai kiyi Asiri sai maganar auren ya watse, da kin ga Mijinki ya tara abun dunia, sai kiyi asiri ya zama a tafin hannunki, sai yanda kikayi dashi, in Nigeria we call such men Mijin Hajia, da kinga Wani yafi ki kwazo da k'okari wurin aiki, sai kiyi asiri ya zama wani wawa soko, Asiri ke sa Mata ke raba Miji da Matarshi, Baba da 'yayanshi, Asiri ke sa ana haukata mata, Asiri ke sa ka shiga duniya kar ka sake waiwayon gida, no matter how you want to go back home you cant, why saboda an maka Asiri, in Nigeria we call it 'Kurciya' and this is what happened to your parent, an musu kurciya ne, shiyasa duk yanda suke son komawa suka kasa" Najwa da hawaye ya gama wanke mata fuska tace"Meyasa wani zai musu haka?they are too goof to be hurt like this" Aisha ta daga kafada tace "bansani ba, kila Babanki wani mai kudi ne, Abokin aikinshi na mishi hassada ya mai kurciya, it can be anything, su nasu ma is different tunda har suna iya tuna k'asar da suke, har suna tunawa da dansu, wasu ko idan aka musu Asiri, wallahi har sunansu suke mantawa sai dai suyi sabon suna yanda kika san me Amnesia haka ake komawa" Najwa tace "it can be it kam, sabida ba so daya ba so biyu ba sun sha zuwa Airport da sunan zuwa Nigeria sai wani abu ya taso, akwai Lokacin da har sunje Dubai, Maama ta dinga suma, tana ihu da akayi transit sai dai suka juyo" Aisha tace "You see, Sihiri gaskia ne, saboda amma fiyayyen hallita Manzon Allah kuma ya kamashi, to waye a duniya da zaa ma Sihiri be kamashi ba? Sai wanda Allah ya kare" Aisha ta yi ma Najwa bayani Sosai, ta amsa duk wata tambayoyin da ta mata, kafin ta dora da cewa "Yanzu Najwa, you have to think twice, shin zaki iya zuwa k'asa kamar Nigeria? Ke da baki san inda kika Dosa ba, baki san inda zaki fara neman yayanki ba, baki san kowa ba, ya zakiyi, can you do that, can you take the risk ?" Najwa ta hadiye miyau zukut tace "in hakan zai tsaida Hawayen mahaifiyata then yes i'm ready" Aisha ta jinjina kai tana yabon determination din Najwa, tace "yaushe ne tafian?" Najwa tace "saura kwana 8" Aisha tace "kafin nan, zan sanar da ke duk abubuwan da ya kamata ki sani game da Nigeria, you have to be strong, because Naija,we no dey carry last".

Ghen! Ghen! Mairo an yi escape from mutuwa, Zaid terror me zakayi next? Majeed You're too good, Najwa, kinsan ina kike shirin kawo kanki kuwa? Tammm.

#1love
#ADAY
#Bibiliciousfreakingfans
#ana tare
#nagode

Biebee Isa
[12:10, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷

NA

BIEBEE ISA

庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Wattpad:@biebeeisa

Pg1鈨�6鈨�

K A N O

"Ya Majeed! Ni ba wani Makarantan da Zan shiga, ni Funtaj Schools dina nike so, ni bana son Kano, i want to go home, bana so" Zinatu ta karashe maganarta tana kuka.

Majeed ya dafe kai cikin murya me sanyi yace "Zinatu,This is our Home" cikin daka tsawa tace "I dont want it here,i hate this place". "Zinatu Abba Abu,ki san yanda zaki dinga min magana, ni ba tsaranki bane".

Mairo ta shigo dakin da sauri jin Hayaniyansu, Zinatu ta fada jikinta ta rungume, " Mummy Ya Majeed na ta min fada yana min Ihu" Mummy tace "haba Majeed, don me zaka dinga mata Ihu? Nawa Zinatun take? Yarinya ce fa"

Majeed ya Girgiza kai, ba tare da yace komai ya fice daga dakin, ba ya son yanda Mummy ke shagwabar da Zinatu, sam bata da kunya,bata ganin kowa da gashin azziki. Ziyada ya samu a parlor kallo daya ta mai ta san ranshi a bace yake, ba kasafai ake ganin bacin rai a fuskan AbdulMajid ba.
Chapter 27 · 0% Book details