Sashe 42
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajjo ta tattara ledojin da ke tsakar Gida ta harhada su a murhu, da k'yar ta samu Ashana ta k'yasta, Najwa na kallon ikon Allah, Hajjo ta sha wahala kafin ta samu jikkakun itatuwan kamawa, a kwano ta daura ruwan zafin, ta zuba Indomien, cikin minti 15 Indomie ya gama, Ta juyo mata a kwano, tace "Jikata kiyi hakuri, ga taliyar nan ko Mai babu, bare cefane." Najwa ta murmusa tace "ai bansan kamshin Komai, hakan ma yayi nagode sosai, , kizo muci" Hajjo ta girgiza kai tace "Ita ci, wannan cimar sai ku, barni da Zogalata". Najwa tayi daria. PORTHACOURT Dariya Zaid keyi harda rik'e ciki, mantuwa ta mance ranar da yayi dariya haka, a TV yake kallon Network News, rahoton Kano ya dauki hankalinshi, inda Hajia Mairo ta baiyana gaban Filin tanata hauka har Majeed yazo ya janyeta daga gurin, Dad kamar ya kashe Zaid, haka yake son ganinsu, cikin uk'uba, da rashin jin dadi, Farincikinshi kenan ganin bakincikinsu, to in har wannan Rahoton da aka nuno a News ya faranta ranshi, to ya dau alwashin muzguna musu har k'arshen rayuwarsu. Ah dole yayi celebrating Haukan Mairo. Dauko Shisha Pot yayi, ya hada uban flavour ya fara zuk'a, yana busarwa, hayak'i ne, ta hanci ta baki, wata sain harta kunne, Zaid sai da ya zuk'i maishi kafin ya bangas. K A N O "Haba Mummy, wai baki san komai game da rungumar k'addara ba?" Cikin Masifa tace "nak'i in sani, dan ubanka wani kaddara zaa runguma? Kasan me Asarar da muka tafka? Da mu muka saida muka san munci kudin mu, da ba haka ba, bansan me muka ma Allah yake mana haka ba" da sauri Majeed ya bar dakin ganin ta fara sakin layi, yanzu ta tafka sa6o, Mairo dai kamar sabon kamu, sai Ihu, da ZageZage, yaranta sai Kuka suna tausaya ma Uwarsu. * * Wayarta yayi ruri, kamar ba zata dauka ba ta dauka, kamar kullum Muryanshi a dakile yace Matar AA Abu" dadi ya lullube Nana cikin yauk'i tace "Yadai?" Zaid ya murmusa kamar yana gabanta yace "kinsan FIRS?" ta dan yak'une fuska tace "Federal Inland Revenue Service?" Zaid yace "yauwa 'yargari,dama ina da hanya ne, shine nace zan samo ma Majeed aiki a chan" Nana cikin murna tace "kai Haba dai? Dagaske kake?" Zaid yace "Yes, yanzu ki dauko CV dinshi, Credentials din Original Copy, don kinsan verification dinnan sai a hankali, in ba Original Copy ba, ba sa ba mutum offer" Nana bata kawo komai ba tace "haka ne, barin Majeed ya dawo na gaya mishi". Zaid yayi saurin cewa "ke, so kike a ba ma wani offer din? Ke da ma zaki mai surprise? Sai kawai ki bashi offer, ai ina ganin hakan zaifi, kawai kar ki gaya mai, cikin halin da yake ciki, ki ka basho offern aiki, trust me ba zai taba manceki ba, kuma ba zai miki kishiya ba? Kuma Mummy zata k'ara sonki, k'imarki zai k'aru wajensu" Nana cikin jin dadi tace "Allah ko?" Zaid yace "Dagaske" Nana tace bari kaga, na ga inda ya aje Folder dinshi da ya dawo daga Dubai, kamar ka san nayi nayi Daddy na ya bashi aiki yace wai "baya da bukatan sabin maaikata, dama rashin aikin nan ya fara damu na, duk da Mummy tace wai Ziyada zata auri dan Deputy Governor, su zssu taimaka mana, amma ai ba kamar ace Mijinka shima na aiki ko?" . Zaid dai na jinta, har tace "gashi na dauko, a ina zaa kawo ma?" Zaid yace "ba sai kin ba kanki wuya ba, already na aiko da me karba, yana wajen gidanku, ki kai mishi Wajen, kar ki bari kowa ya gan, kinji?"Nana tace ba wanda zai gani, ni da zan musu surprise" yace "Good, Yaron deputy Governor din ina Ziyada zata aura?" Nana tace "na Kano" a hankali Zaid yace "Amjad" tace "me kace?" Yace "Noo, kiyi sauri ki kai mai yana waje yana jiranki" tace "toh". *** Cikin kwanaki 3 dinnan, Gidan Alhaji Abba Abu ba walwala, kowa na cikin damuwa, yau dai Mairo da ta tashi dakin Ziyada ta nufa, bayan Ziyada ta gaisheta tace "Ziyadatu, dama na gaya miki Amjad zai zo ai? To yanzu da safe Her Excellency ta kirani, tace zaizo yau" Ziyada ta dan bata rai, tace "Mummy na gaya miki nu banson yaron, sakatarshi yayi yawa, he's tottaly not my type, gaskia yayi hakuri" Mairo ta hau lallashi, haba Ziyada, ya zaki min haka? Please, kinsan k'in aurenshi barazana ne a rayuwata?" Ziyada da mamaki tace "taya rashin aurenshi zai zama barazana a rayuwarki Mummy?" Add V Start from the beginning "Ziyada kinga dai yanda muke fama da babu babun anan, in kika aureshi kakarmu ta yanke sak'a, kinga rannan Mom dinsa 250000 ta bani, dashi fa nayi mana siyayyar abinci, da ba haka ba da yanzu muna kwana da yunwa" galala Ziyada ke kallon Mummynta, kamar ba zata tanka ba tace "Auren Jari zaki min kenan, da ni kike sonyi Azziki? Mummy? Dama baki damu da farinciki na, wato dama dogon burin da ke ranki kenan? To Mummy, ba zaiyiwu ba,ba Zan aureshi ba" nan Mummy ta hau lallashinta ta, wai ta taimaketa ko gaisawa suyi, irin magiyan da ta ga Mummy na mata ne ya sa ta cewa "ta amince yazo a gaisa". * Hajjo Mace ce da ke zaune a babban Gida amma bata da ko k'wayar shinkafa, Bishiya gareta na Zogale, sai ta hau bishiyan ta katso Zogalen sannan ta gyara ta dafa, ta tsince hakukuwan, ta diba taci, sannan ta saida sauran a Kasuwa, a Kasuwa take siyi k'ulli, ta daka ta hada da zogalen t sayar, duk cinikin ba zai wuce dari Takwas zuwa duba daya ba. Cikin kudin ne take so kuran ruwa, don ba ko ruwan sha a gidan balle a samu na Alwala, balle kuma ayi wanka, in yau kuma bata da lafiya to cikin kudin ne dai zata kai kanta Asibiti ta kuma siya magani. Ba ta zuwa gurin kowa, ba me zuwa gunta, A tsawon shekarun nan, da Zogale ta rayu, shine cimmarta, da yake Magani ne, jikinta gwanin kyau. Zuwan Najwa saidai ta siyo Indomie ta dafa mata, don ta sanar da ita abun da kadai take iya ci kenan.Cikin kwanakin nan, Najwa ta gama karantar Hajjo tsaf, ta san ita k'arin nauyi ne ga Hajjo, ta san Tsohuwar na takura saboda ita, kawai Gabata ne yake sa ta na nunawa kamar ba wani damuwa, to wanda ya kawota ya ajiye be dawo ba, be zo balle ta san nayi, sosai take tausaya ma Hajjo, in har dagaske ne Daddynsu Majeed ne Danta meyasa ya barta haka? Ta san Family dinsu Majeed akwai rudani, amma bata san inda zata sa lamarin Hajjo ba, kawai Addua zata tayi ma Hajjo, kuma ta cigaba da tayata Ayukanta, ta na rage mata nauyin wasu abubuwan, don yanzu dole ta rage cin Indomie din nan, dan a rana Indomien Dari uku takeci, saboda Hajjo zata daure ta fara cin Zogale, kuma abun mamaki inta ci Zogalen bata Amai, sai tace "yau Hajjo ba zanci Indomie ba, yau Zogale zanci" Hajjo sai tayi daria. PORTHACOURT Suna zaune dan sak'o yazo daga Kano kawo Credentials din Majeed, Amrstrong ya karba ya fara bubudewa, ya kalli Zaid yace "bros you wan giveam Job?" Zaid ya murmusa yace "No" Amstrong da mamaki yace "Ha'an, wetin dat guy Original Credentials dey do here?" Zaid be tanka shi ba, ya cigaba da latselatsen waya, Amstrong ya gano me Zaid ke niyyanyi, yana so Majeed ya shiga tashin hankalin rashin Credentials dinshi, baya so yayi aiki a ko ina, shiyasa ya sa aka kawo mishi, Duk rashin Imani da taurin zuciyan Armstrong ya tausaya ma Majeed. Amstrong yace "Bros, Easy, E don do now, mey you leave that Family, e tey where you dey cause them trouble, Abeg E don do(Bros, kabi a hankali, ya isa hakan nan, ka rabu da Family dinnan, Ka dade kana ja musu Matsala)". Zaid yayi daria yace " I never start na(ai ban ma fara ba)". Amstrong ya bude baki "Haa, this one wey you dey trouble the pikin, mo go kill the Mama na, na her beef jam her Son(Kai, wannan da ka ke matsa ma Yaron, Muje Mu kashe uwar mana, dama haushinta ne da kake ji ya shafi dan). Zaid yace " listen Man, This woman is very tough, killing her means ending her sufferings, i love seeing her suffer, i cant bring an end to her sufferings, so i will sit and enjoy every part of it(Saurara kaji, wannan matar Shegiyar kanta ce, kasheta na nufin sauk'aka mata wahalhalunta, ina farincikin ganinta a tashin hankali,so ba zaiyi in kawo karshen wahalarta ba, zan cigaba da muzguna mata ina jin dadi". Zaid ya kalli Amstrong yaga beji dadi ba, yace "Guy, why do you even care?" Amstrong yace "Noo, i dont, just that i dey feel for the guy, him dey pay for him Mama mistakes(Ba wai na damu bane, kawai yaron ke ban tausayi, yana biyan laifikan Mamanshi). Zaid ya jinjina kai a gyara zama kafin yace "One thing about Hajia Mairo is that she loves her Family and Money very much, literally these two things are her Happiness, she's very tough and rough, you cant hurt her easily, hurting what she loves most is the only thing that can break her, that is why i keep on bugging her Children Especially the Older One(Hajia Mairo na san 'Yaya da Kudi, Farincikinta kenan, Mata ce kamar Maza, ba kasafai zaka iya bata ranta ba, taba yaranta ko Dukiyarta kadai ne zai girgizata sosai, shiyasa nake takura ma Yaran, Musamman Babban)" muryan Zaid ya k'ara kaifi wurin fadin "i'm going to take everything she's ever wanted away, i will keep making her life a living Hell, then i'll watch her break till the end of her Pathetic Life" Lamarin Zaid ya fara ba amstrong tsoro, kai kawai ya gyada. K'amshin turarenta ya cika Parlorn Gidan Abba Abu, kanta ta ma gurin zama, tana ta sallama ba a amsa ba, ta shigo da kanta, kamar daga Sama sai ga Daddy ya fito, murmushinta ya fadada, a duk lokacin da ta ga Alhaji Abba Yanayinta na chanzawa,