← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 128

Sashe 50

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta shiga taitayinta. Majeed ya murmusa yace "Najwa bani plate din, i can eat by myself" da sauri Najwa ta ba shi plate din, ya karba, tsaki Nana ta buga ta suri jakkarta ta fita daga dakin ranta bakirkirin. Da spoon ya fara ci, duk da bakinshi ba taste amma yana jin dadin Amalan, yaci Gandan da yake da laushi kamar tsoka, Najwa ta k'ura mai ido, tana kallon yanda yake jin dadin Amala din, tana hadiye miyau. Majeed na lura da yanda take hade miyau ya murmusa yace "Najwa, ki zuba kici" da sauri tace "No na koshi" Hajiya Aynarh tace dont be silly girl, ki zuba kici" a kunyace ta zuba, tana zaton ba zata iya ci ba, amma tana sawa a baki taji wani irin dadi, mara misaltuwa, tunda tazo Nigeria bata taba k'oshi kamar na yau ba. Hajiya Ainau ta na nan har dare, da zata tafi ta ba Majeed 50k. Har bakin Mota Najwa ta rakata, kafin ta koma Daki daga ita sai Majeed ghen ghen. * "Oya come and sit here" ya mata nuni da kusa dashi, cike da kunya ta k'arasa gun, ta zauna, sun dade suna kallon Juna, suna saka abubuwa da dama a zuciyoyinsu kafin Majeed yayi magana "ashe kin damu dani haka? Kina ta kuka? Eh Najwa"tace "uhm?" yace "Uhm" tayo shiru ta sadda kanta k'asa, cikin murya kasa kasa yace "bana son kukanki, alot of times in Mummy ta saki kuka inaji kamar nayi hauka, bana son kina kuka, bana so in maida ma Maama ke tace hawayenki ya k'are" tayi daria yace "Always Smile, Be happy kinji Pure Heart?" ta dago kai da sauri ta kalleshi ya kashe mata ido daya, da sauri ta kawar da kai tana blushing yace "yes, kinji ni da kyau, i just called you Pure Heart, i named you pure Heart because you have a Pure and beautiful Heart Najwa, i like it keep it up". Wani irin abu taji daga kan kanta har zuwa yatsun kafanta, bata san ko meye ba, ba ta san ya zata sa abun ba, kawai ita dai taji wani iri, ta kuma kasa barin Murmushi. Haka Majeed ya dinga janta da fira, tun tana kunya har ta sake ta biye mai suka sha firan da tun da tazo Nigeria bata taba irinshi da kowa ba. STORY CONTINUES BELOW Har akayi Sallahn Isha'i kafin Mummy da Fallalu suka dawo, Mummy ta galla mata harara dama all this while tana tare da Majeed? Ita ta kan manta da itama, Fallalu ya kwashi Baskets din Abinci, zai tafi Majeed yace "Fallalu tsaya ka tafi da Najwa" Najwa tayi saurin tashi ta bi bayanshi tare da cema Mummy "Good Night" Iskar da ya debo Najwa Mummy ba ta kalla ba balle ta sa ran Amsata. BAYAN KWANA BIYU Gaba ki dayan su zaune kan Carpet, Majeed na zaune Kan Gado, shi Wallahi ya gaji da Asibitin nan, ya fa ji sauki, kwana 4? Ba fa abunda ke damunshi, dole yau Dr Hisham ya Sallameshi, kullum kawai yan gidansu sai dai su zo su tare a Asibiti kamar Parlo? Ya gaji dole yau a Sallameshi, da k'yar ya samu Mummy ta bashi wayanshi, yana kunnawa sai ga waya an kirashi, "Hello Aliyu Gadanga ah haba? Ya akayi ka san ban lafiya, Ina Softie Hospital na Dr Hisham, room 9, Okay Sai kazo". Mummy tace "wani Aliyu?" yace "Aliyu Tijjani" "Allah sarki ashe kuna zumunci" yace "Gaskia muna waya sosai, mu kan hadu sometime" tace "ai tun biki da yazo Abuja rabon da mu hadu" yace "yau zaki ganshi" haka Mummy take, duk ta san Kawaye da Abokan Yaranta, sai ta yarda da su suke Abokantaka, Lokacin da Majeed na Turai karatu, har chan take binshi don ganin mutanen da yake hurda dasu, haka kurum Mommy bata hada yaranta da kowa ba. * Sai ga Aliyu ya shigo bayan wasu yan dak'ikai, a ka hau gagaisawa, ya dinga bin Ziyada da kallo, yarinyan ga girma ta kara kyau, haka ya karasa Gadon Majeed, suka chafe hannu da Majeed, inji Majeed"Abokina ya akayi ne, duk naga kayi cool abunka?" Aliyu yace "hmm, Abokin sai a hankali, wai me ke damunka na ganka gadon Asibiti, but you look totally fine" Majeed ya bude Murya yanda yan kasa zasuji shi yace "Kinji ko Mummy, kice Dr Hisham ya Sallameni" Mummy tayi daria. Majeed yace "kasan abubuwan sai a hankali stress ne ya min yawa". Aliyu ya jinjina kai ya na tausayin Abokin shi, Majeed yace " Wai ya kake min Kallon Abun tausayi ne?" Aliyu yace "ai abun tausayin ne kai Majeed" Majeed yayi daria yace "kaifa dan iska ne, menene?" Aliyu yace "hmm, so kake in kara tara ma gajiya? Kana fama da stress? Bari dai sai kaji sauki" duk da gabanshi na faduwa, be san da me Aliyu yazo ba, amma ya samu karfin guiwan sonjin me ke tafe da Aliyun, don ya lura bakin shi akwai magana Majeed yace "haba abokina, gaya min ya akayi ne?". Aliyu ya ja numfashi yace " kasan ina aiki da Trust fund? So sai akayi hosting meeting a tourist lounge Conference hall" Majeed yace "Ehen nagane" "so bayan Meeting din ne, na bi ta reception na kama ma wasu Clients Daki, naga Matarka daga nesa, sai da na duba Hoton dinner dinku a wayana kafin nayi confirming itace, so i thought kuna tare ne, sai na k'arasa gunta, na mata sallama nace kamar matar AbdulMajeed Abu, hali da yanayin da take ciki ne ya bani tsoro matuk'a". AbdulMajeed ya sauke Ajiyar Numfashi yace "Hmm, cikin halin Maye ka ganta ko Aliyu?" Aliyu yace "dama kasan tana k'walewa?" Majeed yace "i thought ta daina, ashe tanayi, she do drugs and all, abun Nana sai ita, Allah ya shirya" Aliyu yace "thats not all" Majeed ya zaro ido yace "Aliyu, me takeyi a Tourist lounge?" Aliyu ya zaro waya daga Aljihunshi yayi playing recording din ya ba Majeed ya ji. Majeed Murmushin takaici yayi ya lumshe idanuwanshi ya bude a hankali, bakinshi na maimaita "Inallilahi wa ina ilaihir rajiun" sai da ya samu natsuwa ya cire baki yace "Mummy" Hajia Mairo ta dago kai tace "yes son" da hannu ya mata Alama da tazo, da sauri ta tashi tana tambayanshi me yake so? Wayar Aliyu ya mika mata bayan yayi playing mata recording din, lokaci guda ta shiga mummunan tashin Hankali, Allah yasa bata goga maka wani mugun ciwo ba, ma shiga uku ni Mairo, Daddy ya taso da sauri tare da su Ziyada, Mairo ta mik'a musu wayar sukaji sakin layin da Nana take tayi, duk suka dauki Salati. Ziyada tace "Mummy tun farko sai da Yamaji ya gaya miki halinta kika ki yarda, you see what you caused?" Majeed yace "I told you so Mummy, i told you so" cikin tashin hankali tace "this is not the time to blame me, Daddy ka nemo Dr Hisham ya zo ya mai awon HIV, dole ake ma Majeed test". Da sauri Daddy ya fita duk tsuka tsure suna tararrabin me zai faru. * Bayan 2 hours sai ga Nana ta shigo dakin Asibitin tana yauk'i, a dage take kallonsu, saboda abunda Hajia Aynarh ta mata shekaran jiya bata zo Asibitin jiya ba sai yau, ko kallonsu batayi ba ta wuce " straight Gadon Majeed" Mummy zata tashi Ziyada ta rike mata hannu, Daddy ya mata alaman da abarta da Majeed. "My Majeed ya jikinka?" Murmushi yayi yace "Nana, na taba musguna miki? Ko na miki hainci? Ko na cutar dake ta ko wani fanni, daga Aurenmu zuwa yau?" ta kalleshi da mamaki tace "me ya faru my Majeed?" yace "ki amsani" tace "No, baka taba" yace "to Alhamdulilahi, Nana kije na sauwake miki, na sakeki saki daya, Nana na yafe miki da abunda kika min Allah ya yafe miki, ki nemi tuban Allah" ai bata gane me yake cewa ba, cikin tashin hankali tace "Me kake cewa My Majeed?" Yace "na sakeki saki daya" tace "Kutumar, wallahi baka isa ka sakeni ba, uban me na maka da zaka sakeni, auren zobe mukayi mutu ka raba takalmin kaza" Mari Mummy ta dauke ta dashi, tace "Mutu ka raba dawa? Shegia yar iska, yar codein, yar madigo, mazinaciya, kinji kunya, karuwan Babanta, Hajia Sayluba anyi asarar haihuwa" Mummy ni kika mara? Uban wa ya kala min sharri?" Mummy ta wawuro wayarta, Aliyu ya tura mata recording din, ta ma ta playing, muryarta tace, amma bata san ta saki layi haka ba, ranan she was super dozed off, sai ta fashe da kuka, tana kururuwa wai sharrin shaidam ne, a yafe mata ba zata sake ba, amma kar Majeed ya rabu da ita. Igiyar Charger din dake chargy Mummy ta ciro, kafin kowa ya ankara sai jin ihun Nana sukayi, Mummy ta daddage ta shandara mata, Majeed yace "Mummy stop" ina Mummy bata ji ba, Mummy ta cigana da shandara ma Nana, duk yanda Daddy da su Ziyada suka so hana Mummy amma abun ya faskara, har sai da Nana ta arta waje da gudu, Mummy ta bi bayanta, har kasa tana zaneta, Mutane sai taruwa suke ganin ikon Allah, kafin kace kwabo yan jarida sun zo, kafin zuwa Polisawa, da k'yar aka kwace Nana daga hannun Mummy, bayan Mummy ta fallasa Asirin Nana gaban duniya don playing recording din tayi kowa yaji, wasu suka mata adduar shiriya, wasu kuwa suka tsine mata, abu dai beyi dadi ba. PH Nigeria. Tsaki ya buga karo na ba adadi, ya san zaman Nana zai k'are a Gidan Alhaji Abba, amma beyi zaton abun zaizo da wuri haka ba, yaso ta mishi task daya, wadda shine final task dinshi,Mallakan Gidan da ta mishi haka shi da kanshi zaiyi sanadiyar barinta gidan, amma ta kwafsa mai, ta bata mai Budget, komai na tafiya as planned, Nana ta bata mai lissafi, ya sake sakin tsaki, Amstrong na kallonshi, yanda ya ga Zaid ya lumshe ido, a daura kanshi kan kujera ya san cewa tunani Zaid yakeyi, tunanin mugunta kuma, tunanin da Zaid yake ba Alheri bane, what is he planning this time around, yana kallon bakin Zaid na murmushi, yana ganin yayi smirking yasan cewa ya sama ma kanshi mafita, Zaid ya bude lumsasun idanuwanshi, a hankali
Chapter 50 · 0% Book details