← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 128

Sashe 114

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

Khalid na mai kallo daya ya shaidashi,  ba zai taba manta fuskarshi ba,  shine katon da ya gani kan Gadon Aurensu, Armstrong yace "Mallam,  i am sorry,  i just did as my boss Said(Kayi hakuro,  nayi abunda Oga na yace ne)" Zaid yace "Khalid in kana kallon Zaineema a matsayin mazinaciya,  ko maha'inciya, to wallahi ka bari,  laifi nawa ne,  zan dauki ko wani hukunci,  amma wallahi tallahi ba ta da masaniya akan abunda ya faru,  yanda ka ganshi kan Gado, itama haka ta ganshi" Khalid ya jinjina kai yace "Ka Zalunce mu Zaid,  ka haince mu,  ka cutar damu,  Muna son Junanmu da Zaineema,  muna Matukar son junanmu,  Lallai Albasa bata yi halin ruwa ba,  baka biyo halin Marigayi Gatan Marayu na farko ba,  kuma ka ci sunanka Azzalumi, saboda kana da kudi da Arziki,  shine kake tunanin zakayi komai, ka ci bulus? Ba zan iya Shari'ah da kai a duniyan nan ba, amma akwai buwayi gaggara misali,  Gatan talaka,  babban Alkali" Murmushin takaici Zaid yayi "Ni Azzalumi ne,  na amsa sunana,  kuma ban biyo daya daga cikin kyawawan halayan Gatan Marayu na farko ba,  amma ba don ni ba,  donAllah,  i want you to forgive me, banda abunda zan siya Yafiyanka dashi,  ina dashi,  amma bazan yi hakan ba, amma kayi hakuri ka yafe min, nayi nadama,  donAllah khalid" durkusawa yayi kan guiwowinshi, be damu da mutanen da ke kallonshi ba,  Armstrong yazo zai daga shi Zaid ya dakatar da shi,  Arm ya kalli Khalid yace "i've never seen him kneel before anyone(ban taba ganin ya durkusa ma wani ba)".

Haka Allah ya ma Zaid kwarjini, haka Allah ya darsa  Tausayin Zaid a zuciyar Khalid, yace "Shikenan,  tunda gaskia ta baiyana,  kuma nagode Allah da ba wani abu da ya shiga tsakaninsu, to  Alhamdulilah, ni dai na yafe maka,  saura Zaineema" wani sanyi ya ratsa zuciyarshi,  yace "Nagode kwarai,  Allah ya saka ma da Alheri" Khalid ya murmusa yace "bakomai" Zaid yayi Murmushin yake da ya tuna Zaineema bata furta mai ta yafe mai ba,  amma yayi yak'e yace "Khalid, Gobe zamu tafi Nigeria please,  akwai wani abu da nake so a warware ma mutane" Khlaid yace "No its not possible, nan da kwana takwas zan fara Jarabawa, dana gama zan zo Nigeria, i promise" hankalin Zaid ya tashi yace "Ka gane Khalid,  ina karkashin fushi da barazanar  tsinuwar Mahaifiyata in har ban gyara laifuka na ba, ka taimakeni, wallahi da munje gobe, Friday,  Saturday zan saka a dawo da ku harda Zaineeman,  donAllah ka taimaka min" Khalid ya danyi tunani kafin yace "To Shikenan ba matsala,  Nagode".
*A Gurguje*

Bayan Kwana Biyu.

Convoy din Zaid ya shigo Harabar Gidan Alhaji Sada Abu, Already kowa ya halarta banda Hajia Mairo da Maama da ke chan cikin dakin ,  su Zinatu da Muhsin Daddy ya sa Abdulmajeed dauko su daga Gidan Hajia Aynarh, amma yanzu suna School.
Kafin ya shigo k'amshin turarenshi ya sanar da yan Parlorn Isowarshi,  Manyan kaya ke jikinshi wanda rabonshi da su tun ranar Daurin Aurensa da Baba Ado ya tilasta mai ya sa,  duk da Janpan da ya sa hakan be hanasu gane ramar da yayi,  Zaid na isowa ya nufa kujerun da Daddy da Paapa ke zaune ya durkusa ya gaishesu cike da girmamawa,  suka amsa mai cikin sakin fuska.
Karasawa yayi ya gaida Hajjo, ya nufa Abdulmajeed, Majeed ya mike tsaye ya mika mai hannu da niyyar su gaisa,  Zaid ya rungumeshi tare da cewa "I am so sorry brother, ka yafe min" Abdulmajeed ya gyads kai yace "komai ya wuce brother".  Zaid ya murmusa ya kalli  inda yan matan ke zaune,  ya karasa gunsu ya kalli Najwa yace "Namaste Baby" daria tayi tace "Welcome Bhaiyy" ya kalli Zaineema cike da jin kunyarta yace "Hello Sister" ba yabo ba fallasa tace "Hi Bro" yanda ya lura shes sad yace"Everything is going to be fine,  i fixed everything" a zuciyarta tace "fix everything  a ina? Bayan ka rabani da. Mijina" amma a fili murmushin yak'e tayi, Finally Idonsa ya sauka kan Ziyada,  wanda ta ke jin tsoron ya k'i mata magana, tana cikin wannan zulumin kunnenta ya jiye mata muryashi na fadin "My Forever" a hankali ta dago ta kalleshi suka hada ido,  da baki ya mana nuni da 'i love you' ita kadai taji,  da sauro ta sauke idonta k'asa.

Daidai shigowar Maama da Sallama,  bata yarda sun hada ido ba ta zauna,  don wani abu janta yake ta nufeshi ta rungumeshi,  nan da nan Zaid ya shiga taitayinshi,  zai karaso gunta da sauri ta daga mai hannu tace "Kwana Biyar sun cika,  kayi abunda nace?" cikin  rashin karfin jiki yace "Eh Maa,  nayi duk abunda kika ce" tace "Ehen,  kai muke saurare,  ka maida komai muhallinshi" fita yayi da sauri ko minti uku ba ayi ba sai gashi dauke da wata jakka, Khalid kuma na bayanshi,  Khalid ya musu Sallama,  Zaineema na ganinshi ta damki hannun Ziyada gabanta na faduwa,  Khalid ya durkusa ya gaidasu a mutunce,  suka amsa mai,  ya  karasa inda Abokinshi yake,  suka gaisa,  kafin Zaid ya fara magana.
"Maaa,  Wannan shine khalid Mijin Zaineema, yana wani course a America,  da naje Kaduna na samu labarin yana America,  so sai naje America na mishi bayanin abunda ya faru,  na bashi shaida,  ya kuma gamsu da abunda na gaya min, shima ya tabbatar min da cewa dama ya fahimci komai,  jira yake ya dawo daga America yazo ya dauki matarshi,  na tambayeshi gafara ya yafe min,  a gabanku zan sake tambayansu Yafiya,  Zaineema, Khalid don Girman Allah ku yafe min,  na tuba" a kusan tare sukace "mun yafe maka, Allah a yafe ma Mana" Zaineema harda Murmushinta.

Ya bude jakka ya ciro Wasu Takardu,  da Key,  ya k'arasa gun Baba Abba yace "Daddy,  ina neman yafiya da Albarkarka,  ka yafe min duk wani bakinciki da na k'unsa maka, ba don ni ba" Daddy yace "Zaid,  na yafe maka wallahi,  ban rikeka ba,  ban ga laifinka ba dama" Zaid ya jinjina kai ya mika mishi wani Folder yace "wannan Takardun Mallakan Furnishing Company ne da na saka aka rushe, wannan Mukulin *Abba Abu &Sons Furnishing Company* ne na saka an gina ma,  a halin yanzu an saka kayan aiki, an kuma dauki Maaikata" Daddy yace "Zaid,  Asali *Sada Abu $Sons Furnishing  Company* ne,  kamar yanda ka sani,  nashi ne,  it was never mine" Zaid yace "To Daddy wannan kuma tsaakaninka da danuwanka ne,  nidai a haka na gani,  kuma a haka zan danka mai" ya mike,  Daddy ya kalli Paapa zai yi magana Paapa yace "Aa Yaya,  Dont Start Please,  Naka ne" Wani irin farinciki ya ziyarci zuciyan Daddy,  wanda ya sashi rungume danuwanshi.

Zaid ya dauki sauran Takardun ya karasa gun Abdulmajeed yace "Brother, wannan naka ne, wannan mukulin Motarka ne da su Arm suka kwace a hanyar Zuba, ga kuma Credentials dinka, na san na cuceka, bazan gaji da fadin na Zalunceka, amma kayi hakuri,  ka yafe min,  donAllah"Abdulmajeed ya bude hannu ya rungumeshi yace "My Brother" hawaye suka fara yi a tare kafin Zaid ya zauna a k'asa. Ran Maama Fes Zaid ya wanke kanshi,  ya bata mamaki yanda ya tafiyar da komai cikin dabara,  shes proud of him.

Daddy yace "Toh Alhamdulilah, Allah mun gode maka daka kawo mu wannan rana,  mun gode maka da kawo mana karshen wannan takadamar,  ina me kara karkatar da hankulan mu kan Hakuri,  yafiya da juriya" nan Daddy ya bata lokaci gun musu nasiha me ratsa zucia, kafin Papa ya daura da nashi sukayi Adduan zaman lafia da so da kaunar junansu,  suka shafa, aka tambayi inda akwai me magana Abdulmajeed yace yana da, Paapa yace "Yi Magananka Abdulmajeed".

Abdulmajeed yace "wani Bukata nake dashi gun Danuwana da kuma Daddy" Zaid yayi saurin cewa "ka fadi ko meye Bro,  InshaAllah zan maka" Abdulmajeed yace "i want you to find it in your Heart to  forgive our Mother" dan jim Zaid yayi,  kowa ya zuba mai ido yana kallonshi kafin da karyayen muryarsa yace "Duk laifukan da na muku duk kun yafe min,  ni waye da ba zan yafe mata ba? Allah ya yafe mana gabaki daya" Farinciki ya darsu kan zuciyar yaran Mairo, barin ma Ziyada,  Abdulmajeed yace "Daddy, on behalf on ni da kannena,  muna baka hakuri akan laifij da Mumny ta maka,  munsan ta ma babban laifi,  amma kayi hakuri,  ka yafe mata,  ka maidota dakintaz na rantse maka Mummy ta gane kuranta,  Daddy Please" su Ziyada da Zaineema harda Najwa suka durkusa suna rok'on Daddy ya yafe ma Mummy,  Daddy yayi dan Jim yace "Allah ya sani ina son Maryam sosai,  ina kaunarta,  ta min laifi,  amma wanda ta fi ma laifi sun yafe mata,  kuma shima ubangiji muna mai laifi Ya yafe mana, kamar yanda Zaid yace mu su waye da ba zamu yafe ba in aka mana laifi? Na yafe ma Maryam,  amma na barta ta koyi zaman duniya,  zan dawo da ita,  bayan Aurena da Aunty Aynarhnku".
Chapter 114 · 0% Book details