Sashe 52
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nakowa zai dauko Attorney. PH Nigeria Dadi yaji da labarin ya iso gareshi, a fili yace"The Nakowa's and The Abba's are against eachother? Intresting(da Iyalan Nakowa da na Abba suna ganin Hanjin Juna? Abu yayi dadi)" Amstrong yace "what are you planning Oga(Shirin me kakeyi?)?" Zaid ya Murmusa kawai, ba kasafai yake furta abunda yake shirin yi ba, ya fiso a ga Action kawai, a ranshi yace; 'zan bari su fafata a tsakaninsu, me kudi shike Nasara a k'asar nan, idan Alhaji Nakowa ya gama dasu Hajiya Mairo, nikuma zan cigaba daga inda na tsaya, yanda breaking dinsu ba zai min wuya ba' Amstrong ya bishi da ido, yanda Zaid ke lumshe idanuwa ya san cewa wani muguntan yake kullawa, Zaid ya san lungu da sak'on Mugunta, ya sake tambayarshi kan shirin me yakeyo, sai Zaid ya shashantar da maganar ta hanyan cewa "Get me an Appointment with Rita Phillips" da mamaki Amstrong yace "Rita Phillips why?" murmushin Mugunta Zaid yayi yace "I need me a Makeup Artiste" da mamaki Amstrong yace "Why?" Zaid ya fashe da Daria yace "Watch the Master and learn" ya zaro wayarshi ya latso wata numbern a wayarshi, ba zai iya tuna ranan da ya kirata da hannunshi ba, amma yanzu da yake bukatar hakan ya taso, dole ya kirata. * Tana kwance tana dogon tunani, anya akwai asararriya a duniyan nan kamarta? Ta banzatar da rayuwarta ta kan Namiji daya, ba don Azzikinshi ta ke sonshi ba, sonshi take tsakanin ta da Allah, tana Aji Biyu a France, da zai dawo Nigeria saboda sonshi ta bar karatun ta na chan ta dawo UNIPORT don kawai ta kasance tare dashi, gashi shi be son iskar ya debota ba, kwatakwata be bi takan ta, tana cikin wannan tunanin ne wayarta yayi ruri, kamar ba zata daga ba ta duba, ganin me kiranta ya sa ta daka wani tsalle tare da kafan wayan a kunne "Hhhello?" muryar da tafi ko wanne dadi a gurinta taji yace "Na'eelah" cike da shauk'i tace "Zaid" yace "Errhm, kin tuna lokacin da kikace idan ina son wani abu a wurinki in gaya miki?" da sauri tace "Eh, ka gaya min ko meyene, nikuma zan makashi with all my Might" ya murmusa kamar tana gabanshi yace "This is somehow complicated" tace "kar ka damu i'll do it, anything for you" ya gaya mata abunda yake so ta mishi, ta danyi jim tace "idan na maka haka zaka aureni?" kai tsaye yace mata "Aa, amma zanji dadi idan kika min hakan" taji ba dadi, ta so tace ba zata iya abun da yake so tayi ba, amma ta na son Zaid, his happiness comes first, a hankali tace "Okay, I'll do it" murmushi yayi yace "Good, comeover now" ya kashe wayar, Naeelah ta jima zaune, tana mamakin Izza da nuna isan Zaid, ita zata mishi abu amma not even a thanks, tashi tayi ta gyara jikinta ta fita don zuwa gidan Zaid. KANO Tun Sallamar Majeed daga Asibiti, suna zaune lafiya da junansu, saboda Majeed Mummy na kawar da kai bata kyara da tsangwaman Najwa, bayan idonshi tana harararta da hantararta. Tun a Asibiti Najwa bata sake bari sun kebe da Majeed ba, sai in sun hadu a Parlor, shima gaisheshi takeyi ba tare da ta kalleshi ba, saboda wani irin kunya da yanayin da takejin kanta a duk lokacin da suka ke6e da Majeed. Da daddare Zasu hadu gabaki daya su ci Abinci, Mummy ke dafawa, bak'in cikinta ta dafa Abinci Najwa taci, da ta lura Najwa bata son Kifi, sai ta dinga yin Abinci da Kifi, Najwa ko da taga Abinci da Kifi sai tak'i ci, sai tace ta k'oshi, sai Majeed yace "me kikaci? barin dafa miki Indomie" sai Mummy tayi saurin cewa "haba, barta ta dafa da kanta zata fi jin dadinshi ko Najwa?" sai ta gyada kai ta shiga Kitchen ta dafa Indomie dinta, Muhsin yace "Ya Najwa, me zai sameki in kika ci Fish?" tayi murmushi tace "I will fall sick" Muhsin ya kalli Mummy yace "Mummy, ki daina abinci da Fish, Ya Najwa will fall sick idan taci fish kinji Mummy?" duk suka kafe Mummy da ido suna jiran me zata ce, Yak'en dole tayi tace "na bari" har ran Majeed yaji dadi. A ranta ko ta aiyana sai ta sa kifi yanda Najwa ba zata gane ba taci ta ga me zai faru da ita, yarinya sai shegen Iyayi, wai bata iya cin Kifi, Washegari da rana tayi abinci da Man Kifi, ba zaka gane ba in har ba gaya ma akayi ba, sun hadu gabaki daya zasuyi lunch, two spoons kadai tayi numfashinta ya fara daukewa, Majeed ya fara lura da ita, "Najwa are you Ok?" duk hankalinsu ya dawo kanta, cikin shesheka take cewa "abin abinci, ki-fi" Majeed ya tashi da sauri ya tsiyayo juice ya bata tasha, Muhsin rai a bace yace "Mummy kinyi Abinci da kifi?" baki na rawa Mummy tayi karya tace "aa, banyi ba, da kun gani ai" "YaMaji mu tafi Asibiti" cewar Ziyada, Daddy yace "she needs a first Aid treatment" kamar zata shide ta fara magana a hankali, "FresssshTomato" Majeed yace "me kika ce?" da kyar ta maimaita, da gudu Ziyada ta shiga kitchen ta dauko Tumatir guda biyu, Majeed ya Amsa hannun Ziyada, da bakinshi ya fasa tumatirin ya kafa mata a baki, ya juye mata ruwan tumatir din a baki, ta dinga tsotsa, haka ya fasa dayan ya juye mata, a hankali a hankali numfashin ta ya fara dawowa daidai, Daddy yace "Muje Asibiti" tayi murmushi ta girgiza kai tace "i'm fine Daddy" "are you sure?" "Eh, ba wani abu, dama idan haka ya faru dani, Tomato Maama take bani, dana sha sai in dawo normal" Hajjo ta jinjina kai tace "haka fa mutum zaiji beson wannan abincin, kamar Sada, shima beson Kifi" Damm gaban Mairo ya fadi, ya akayi Hajjo ta iya furta sunan Sada?hakan na nufin ta iya tunashi? Shin Abba ma ya tuna? Kafin kowa ya fahimci abunda Hajjo tace tuni Mummy tace "bari a dafa maki Indomie Najwa" duk da sunyi mamakin sudden change din Mummy amma ba su ce komai ba" Najwa tace "No Mummy, sai anjima, yanzu i lost taste" ta tashi ta wuce daki duk suka bita da ido, Majeed ji yake kamar ya bita, duk yabi ya damu, wannan shi ake kira da reshi ya juya da majuyi, tayi don kuntata ma Najwa, gashi ta k'are da k'untata ma yaranta don har fuskar Zainee ta karanci Damuwa. * Hajjo tayi ja ta k'ara kyau abunta, tana samun kula yanda ya kamata, duk da Mummy bata gama sakewa da ita ba, amma jikokinta na sonta, don har Zaineema na zuwa dakin ta zauna ta dinga jin firarsu da Ziyada in kadaici ya isheta, Zinatu ce dai ba ruwanta da Hajjo da Najwa, Jiya ma Aunty Ainarh ta kawo ma Hajjo Garan Abinci, tuwon shinkafa miyan Kubewa danye sai Farfesun Ganda, Hajjo tayi ta shi ma Aynarh Albarka, abunda ya kashe Mairo ganin duka yaran Gidan sunci Abincin Hajia Aynau, bakinciki kamar ya kasheta. Wasan buyan da suke da Najwa ya fara damun Majeed, aika Muhsin yayi dakin Hajjo yace "ka karbo min Wayan Ya Najwa" da ya isar mata da sakon ta tashi ta dauko wayar ta bashi, Wayar da tunda aka siyota bayan tayi charging ta saka a drawer, ba kwanciyar hankali lokacin Majeed na Asibiti balle ta kira Maama, ta so kiransu yau amma tasan ba kudi, kuma ba zata iya rokon kowa ya sa mata Kudi a waya ba. Majeed ya duba wayan ya ga batayi komai dashi ba, waje ya fita ya mata activating Sim din ya mata recharging da katin 1500, ya mata saving Numbers din yan gidan, harta Whatsapp sai da ya mata logging. *MONDAY* Yara sun tafi Makaranta, Daddy ya fita 'yan bugabuganshi, Mummy ma ta fita wurin Lawyer dinta, har yau bata sanar dasu Majeed kan cewa ta kai su Nana kotu ba, ta bari sai ana gobe zaa shiga Kotu sai ta gaya musu don kar yanda zasu sa ta janye k'arar. Zaineema kamar kullum tana daki tana kwance, Hajjo itama na daki tana jan chasbi, Ziyada ko Majeed ya tafi kaita School kasancewar yau zata fara karatu a NorthWest University. Najwa ta dauki wayarta, ta zagaya boysquaters, ta ja dogon numfashi kafin ta furzar, dialing numbern Paapa tayi, ringing uku ya dauka. I N D I A K'afar shi da sauk'i, suna dai Asibiti ba a sallamesu ba, duk abubuwan duniya ya damesu ya ishesu, ko wannensu karfin hali kawai yakeyi don karfaffa ma danuwanshi guiwa, suna zaune a dakin Gadon Asibitin jugum Wayar Paapa tayi k'ara, jone yake a Chaji, Maama ta tashi ta cire wayar daga charge, tana ganin numbern +234 location ya nuna Nigeria ne tayi saurin dauka ba tare da mik'a ma Paapa wayanshi ba. "Hello, Najwa beta" zumbur Paapa ya tashi, shima yana kiran "Najwa" Maama na jin hucin numfashinta a kunnenta, tayi amanna Murmushi Najwa keyi, cikin sanyin murya tace "Maama" a tare suka fashe da kuka, nan aka shiga labarin yaushe gamo. K A N O Maama ta dauki wayar, "Hello Najwa Beta" hawaye suka fara suntiri a idon Najwa, yanda Maama tayi maganan kamar dama tuntuni wayarta kadai suke jira, ba su san ko waye ba amma tana dauka ta kira sunanta, cike da doki tace "Maama, i'm so sorry, na san na saku cikin damuwa, ku yi hakuri, wallahi abubuwa da dama ne suka faru, shiyasa kuka jini shiru, please Maama kuyi hakuri" Kuka Mama ta fashe dashi, tana jin kukan har ranta, Maama tace "Najwa, are you Alright? Ina fatan lafiyar ki lau, ki gaya min diyata" "I'm fine Maama, ina Paapa?" He's fine saidai- ji tayi an karbe Wayan, "Hello Najwa" a hankali tace "Paapa, are you OK? Are you taking care of my Maama? Kuyi hakuri na barku without a word, i know you are sick worried about me, a Airport ne nayi loosing Everything" nan ta labarta musu abunda ya faru, suka jajanta mata, abu beyi dadi ba, Maama tace "Najwa, kina ina yanzu?" Najwa tace "Ina Kano" ba wai don sun tuna ina ne Kanon ba tace "Kano a ina, gidan Wa?" "Erhhmm Gidansu