← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 128

Sashe 48

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

AbdulMajeed Damuwa? Ya Salam, how Old is he?" charaf Mairo tace "He'll be 29 nextweek" Dr ya jinjina kai, yace "29 years amma yana fama da * High Blood Pressure?* tun yanzu ya fara fama da BP? Ko 40 fa be kai ba, meye damuwanshi?" duk sukayi shiru, Dr ya shiga fada yace "He's too young da zai fara shan Wahalan Hawan Jini, sam Hawam Jini ba ciwon Samari ba, Imagine BP dinshi ya haura 200, wannan in ya cigaba da yanke Jiki yana fadi yana suma, Zuciyarshi bugawa zatayi ba tare da bata lokaci ba, and you'll lost him for good" . STORY CO Mairo tace "God Forbid, Dr, bari, gaya min how's my baby now? Ina fatan ya dawo daidai?" Dr ya kalleta yace "hmm, mun samu jinin ya sauka, but he's stressed out, na bashi bedrest for one week, kar ku dameshi da abunda zai saka shi cikin damuwa, and abar bashi Abinci mai gishiri, in ya farfado nurse zata bashi magani, he's very weak, ku barshi ya huta please, in ya tashi komai zai zama normal, amma zan rikeshi anan for a week". Mummy taja numfashi, sai yanzu ta dan samu natsuwa tace " ai Dr, gwara ka barshi a Asibitin, wallahi shike stressing kanshi, Yaro baya nan baya chan, InshaAllah zamu kiyaye" Dr ya kalli Najwa ya murmusa yace "You must be his Wife, Alhaji ya gaya mun AbdulMajeed yayi aure" Najwa baki ya mak'ale takasa cewa komai, Mummy ta balla mata harara, tace "Noo, ba ita bace, she's--" ba ta karashe ba, Ziyada ta k'arasa da fadin "Family, Shes Family" Mummy ta bude baki, Daddy ya murmusa, Dr ma ya Murmusa yace "Mallama Ziyada ina su Zinatu?" ta amsa mai, Dr ya mike yace "bari ya tafi rounds, suka mai godia ya fita daga Office din. PH Ng "Whoa! Wait is he Alright?" tambayar da Zaid yayi ma Amstrong kenan da ya sanar dashi an kwantar AbdulMajeed a Asibiti, Amstrong ya tsura mai ido, yana son ya san wani yanayi Zaid yake ciki, idan beyi k'arya ba, zaice ya ga damuwa a idon Zaid, amma bari ya tabbatar da hakan, gyaran Murya yayi yace "Why are you worried?" Zaid ya dan yi Jim, chan kuma da sauri yace "Ofcourse Not, i careless what happens to the Abba Abu's, serves them right" yayi sauri ya tashi ya shige daki don gudun ma tambayoyin Amstrong, sai dai me? Yana shiga daki ya rasa sukuni, ya rasa meke damun shi, baya son zuciyar shi ta tabbatar mai da damuwa ya shiga, Shisa ya kunna amma sam ya k'asa zuk'a, hankalinshi ya gaza sukuni, ba wannan yake sonyi ba, chan k'asar Zuciyar shi, akwai abunda zuciyar ke son sani, tsaki ya buga da k'arfi ya ciro Wayan yayi dialing wani Number, chan k'asan Mak'oshi ya fara magana; "Mallam Musa, je Softie Hospital din Dr Hisham, ka binciko min, meya samu AbdulMajeed, make it Quick" dif ya latse wayan, ya dafe kanshi da hannu biyu, ya buga tsaki karo na ba adadi, a fili yace "bawai na damu da halin da kake ciki bane, ya ma zaayi na damu? I pray Condition dinka yayi tsanani" sai dai a cikin zuciyanshi be fatan hakan. KANO Cike da Maye ta wuce Tourist lounge, kallo daya zaka mata kasan cewa ta k'wallu, sai da ta biya Gida ta kwashi Kwayoyinta masu gusar mata da Hankali, k'wayoyin da ta bar sha duk saboda Majeed, yau hadin da tayi yafi k'arfin ta, yau Mummy ita ke ma barazanar rabuwa da Majeed? Mummy ta bar sonta. So take ta huce takaici, duk da yanzu jin kanta take a sama, ba wani shege kamarta, a gaban Entrance din ta kira Saleem Waya muryarta cike da maye tace "Kana ina ne wai? Kasan bansan Jira, in bata min lokaci zakayi ka turo min Nimcy, kace mata ina jiranta" tsaki tayi ta kashe wayan. Wuri ta samu tana mari ta na mayenta hade da sambatu, ta gaji, har ta fara daukan hankalin mutanen wurin da Sambatun ta. * Sallama taji ana mata, da rinannun idaniyarta ta dago ta kalleshi da k'yar, "Nana matar Abdulmajeed Abba ko?" kallon alamun rashin sani ta mai tace "yeah?" yace "Ina Majeed?" cikin layi take magana tace "yana Asibiti" Subhanallah meya sameshi?" "kawai don na bada Credentials dinshi a neman mai aiki ya Suma, daga taimako fa" daga yanda take magana ya gane cewa akwai matsala, kamar a buge take, yace "to me kikeyi a nan?" a tak'aice tace "ina jiran Saurayina da Girlfriend dina" Gabanshi ya fadi, kar dai abunda yake zargi ne, da sauri ya ciro wayarshi ya lallatsa, a buge take, zai iya getting information daga kanta ba tare da tayi k'arya ba, da sauri yace "What?" ta dake maimaita mai kafin tayi dariyan 'yan bariki tace "kaima dan k'auyen ne ko? Lol, Majeed ba zai iya dani ba, Salim da Nimcy kadai suka san yanda suke wadatas dani" baki na rawa yace "Erhm Nimcy din Mace ce?" Ehmana sun fi dadin harka, kaima in kana so akwai guys din da zan hadaka dasu" baki na rawa yace "no karki damu, ina da su" "hahaha kace kai dan hannu ne, sha, samun numbernka zan kiraka" karban wayanta yayi ya sa mata number, yace "gashi na miki saving" tace "yauwa, ga Salim nan zuwa, wuce donAllah kar ya ganmu tare yayi Zuciya, Kishi gareshi, da My Majeed kadai ne be Kishi saboda ya san son da nake mishi, yi sauri sai na kiraka" jikin shi duk yayi Sanyi ya wuce yana mamaki. Duk sun hadu a dakin Asibitin, sai dai ba me magana, zaune suke Jugum kamar anyi Mutuwa, shi Majeed be son ganinsu cikin damuwa, ya kalli wannan ya kalli wanchan, chan sai yace "Zeenah meyasa bakuje School yau ba?" cikin Muryan Shagwaba tace "ba kai bane baka da lafiya?" ya Murmusa yace "lafiyata lau, Fallalu yazo ya maida ku gida, 2 nayi ku wuce Islamiya, nima yau zaa sallameni, kafin ku dawo ina Gida ko?" kafada ta mak'e yace "Pleaseee, kije Islamiya, naji sauk'i" da k'yar ta Amince, Muhsin yace "YaMajeed inci Apple dinka?" Majeed yace "Eh Muhsin kaci" da tsallenshi ya dauka yana ci, Majeed ya kalli Ziyada yace "Oya Zuzu, je ki duba Fallalu na waje? Duk ya zo ya kwashe ku ku koma Gida, yanda kuka tsura min ido kamar ance muku na mutu" Ziyada ta ja hannun Najwa don ta rakata amma Najwa ta tirje, hakan ya sa Ziyada tafiya ita kadai, Majeed ya ga abunda tayi, sai dai kawai ya Murmusa, a bakin K'ofa ta ci Karo da Nana da ta shigo hannun nik'i nik' da kayan Abinci, raba Juna sukayi suka wuce. Ba tare da ta gaida mutanen da ke zaune wurin ba, Iyayen Majeed da Kakarshi, Nana ta wuce kai tsaye Gadon Majeed ta fada kanshi tare da rungumeshi, ido ya runtse kafin ya bude a hankali, "My Majeed are you Alright?" da k'yar ya iya daga mata kai, ta taba nan jikinshi ta taba nan, wai ita tana duba in akwai inda ke mai Ciwo a jiki, haka zata dauko Pear ko Apple, ko grapes tace yaci, Murmushi ya ke k'wakulowa ya girgiza kai, a hankali yace "Nanah, ina Credentials din an kawo?" dimmm tayi, Mummy tayi karaf tace "wani Credentials?" baki na rawa, Nana tace "Aiki na bada a samo mishi" Mummy ta kalleta tace "a ina?" a takaice tace "Inland Revenue" Mummy tace "Allah ya sa a dace" Majeed yace"Nana please, kice a yo sauri in a kawo, if there are busy ni ki gaya min inda suke inje duk nisan su, i need that Folder, My Whole life is in it". Mummy tace "Tsaya, Original Copies din ta dauka?" Nana ta sunkui da kai, Mummy ta dan bude Murya tace "ke Original Copies kika dauka?" a hankali ta gyada kai, Mummy ta rafka Salati tace "Danubanki ke jahilar inace? Ina kika taba ganin an nemi aiki Da Original Results? Yi Maza Maza yanzu ki kira, a kawo, ko ni inje in karba" kwalla ta fara tace "yace Zai fa kawo min" Mummy tace "ayi Maza a kawo, don Wallahi in wani abu ya samu Credentials din nan, Wallahi ko Alhaji Nakowa ba zai iya kwatarki daga hannuna ba, Sakara Mara Amfani kawai". Daddy ya tare ta yace "Maryam Easy mana, ance kar ayi Hayaniya har yanzu fa kwance Majeed din yake, kiyi hakuri ayi komai a hankali, tace zaa kawo, ki bari a kawo din" huci take kamar Zakanya, ta samu wuri ta zauna tana karkada k'afa, Majeed ya sausauta murya yace "Kiyi hakuri Nana, donAllah a kawo min Credentials dina kinji?" tausayi ya bata, ta daga kai tace "Kar ka damu za a kawo" ya gyada kai ya koma ya kwanta. Shiru dakin yayi kowa da tunanin da yakeyi a Zuciyar shi, Ziyada suka shigo da Fallalu, ya ma Majeed ya jiki, Majeed ya amsa da Murmushi, yace "Fallalu ka kwasar min tsohuwan nan da Jikokinta kai min su Gida" Hajjo ta wurga mai harara tace "kai Abdallah ba ka rabo da ba'a" yayi daria tace "to yan jikoki mu tafi ko?" Muhsin ya rik'o hannun Hajjo, Daddy yace "Umma ayi mana Addua daga nan zan dawo Gida" hajjo ta murmusa tace "Allah ya hadaka da Alherin Mai Alherin, ya kuma nisantar da kai daga Sharrin Mai Sharri"duk suka amsa da Amin,"Amin Umma nagode" banda Mummyn da ta wurge su da harara tana sak'a ma ranta wani abun da ita kadai ta sani. * Daddy ya tasa k'eyar Muhsin da Zinatu a gaba, zai raka Hajjo bakin Mota, Zaineema ta matso kusa da Gadon Majeed, ta mai kiss a goshi tace "Kaji Sauk'i" kai ya gyada mata tare da mata murmushi, ta juya ta bi bayansu Daddy. A haraban Asibiti suka ci karo da Motar Hajia Aynarh, ta fito cikin shiga ta Alfarma, mai aikinta ta fito rike da katon Basket, suka karaso gurin da Motar su Fallalu ke parke suna niyan fita Asibitin "Alhaji Abba baka kyauta min ba, ya ba zaka gaya min Abunda ya samu yarona ba tun jiya sai dazun? Haba" Daddy yayi Murmushi yace kiyi hakuri ko? Ai dai na gata miki yau din, tayi dariya cike da Kissa tace "to na
Chapter 48 · 0% Book details