← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 128

Sashe 36

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Parlorn inda kowa yake zaune. Addua sukayi suka fara cin Abinci, duk yunwa sukeji, ba kamar yaran, Najwa na kallonsu, don kasa bacci tayi, sosai Majeed ya burgeta, yanda yake son Family dinshi, yanda ya hado kansu bayan sunyi fushi dashi, yanason Family dinshi, hawaye masu zafi suka zubo mata, ina ma ace Sun tashi da Yayanta, zai so su kamar yanda Majeed ke son Family dinshi?, Kuka ta farayi da ta tuno Mamma, kuka ta farayi da ta tuno rayuwansu a India, shiru tayi don ta fara jin magana sama-sama. "Munyi Aptitude test din, InshaAllah akwai nasara, don komai ya tafi daidai,akwai wani dan Nigeria a cikin Manyan, tunda ya ganni yake ta kyautata mun, yace lafiya lau zai min hanya, zasu neme mu sukace" Daddy yace "Allah ya sa rabo ne" duk suka amsa da "Amin" duk yanda zaiyi yayi dodging maganan Najwa sai da yayi, be bari sun sako zancenta ba balle Mummy ta burkice masu, hakan suka gama da cin Abincinsu,suna fira jefi jefi. Nana taji wayar ta na ringing, da sauri ta tashi tayi daki da gudu, da mamaki Majeed ya bita da ido, k'arfe 11 fa wake kiranta a daren nan?. PH Ng Kasa sukuni yayi, fargabanshi daya, a yi employing Majeed, in har Majeed ya samu Aiki ai Plan dinshi zai ruguje, ba zaiyi acheiving komai ba, all his efforts will go in vain, ba zai bari hakan ya faru ba,Majiyanshi ta shaida mai, Majeed ya duro Nigeria,amma abunda be sani ba, meyi matsayin Majeed a Hilal Investments, yana kuma so ya sani, Mutum daya zai fayyace mai biri har wutsiya, ya duba Agogon wayanshi, k'arfe 11:10 na dare be damu me zai je ya dawo ba, ya latso Numbern Nana Nakowa. Da tsaki ta dau wayan "Hello, meyasa kake kirana da daren nan? Bashi kake bina?" Murmushi Zaid yayi, yace "Mijinki ya dawo,so howfar?" tsaki tayi tace "donAllah ka daina bibiyata, you wont hear a thing from me" Zaid ya dara yace "Is that so?" hakan da yace Nana ta gano abubuwa cike da "is that so?"din, sai ta tsorata da lamarin mutumin nan, kar fa ya tona mata asiri, da sauri ta kwashe duk abunda Majeed ya sanar dasu Yanzu. Zaid yace "Good Girl, sai na sake nemanki" da sauri Nana tace "kayi wa Allah kar ka sake kirana" tuni Zaid ya kashe wayan. Daidai da shigowan Majeed, lokaci daya ta shiga taitayinta, Majeed yace "Wa ke kiranki da daren nan?" da sauri tace "Mom ce" yanda tayi maganan ta san bai yadda ba, amma tayi saurin isa gareshi don mantar dashi wani tunanin. Washegari. Mummy da kanta ta shiga kitchen ta hada breakfast, Tea and Bread ne da K'wai, lallai rayuwa ya chanza musu, da breakfast dinsu abun kallo ne, masu aiki sai suyi mus kalaci kala kala, amma yanzu da chanjin yanayi yazo, Tea Bread and Egg kawai zasuci, ba kuma masu Aikin, itace zatayi dole, indai zasu jira Nana ta musu breakfast sai dai su yini da yunwa, bata tunanin ko ruwan Zafi Nana ta iya dafawa, ita kuma bata yarda ta bar yaranta da yunwa ba. Fitowan Majeed kawai sukeyi suyi Karin kumallo, yana fitowa yayi dining din tare da gaishesu duka "Ina kwananku" sam Majeed be da girman kai, har dan karami yana iya gaidashi, har ya zauna kuma kamar an tsikareshi ya tashi, duk suka bishi da ido, dakin Ziyada ya nufa, ya k'wankwasa tare da Sallama, Najwa ta amsa tare da bude mai, Murmushi suka sakar ma Juna, kallo daya ya mata ya san ta sha kuka Daren jiya, don fuskarta tayi ja, idonta yayi luhuluhu, gaishe shi tayi, ya amsa da murmushi yace "muje muyi breakfast ko" murya a dashe tace "Your Mummy" ya murmusa yace "Bakomi, muje" kanta a kasa ta bi bayanshi har gaban kowa a dining table. A hankali tace "Ina kwananku?" Daddy kadai ya amsa,Majeed be damu ba ya ja mata kujera yace "sit" zama tayi, ya dauko Mug ya hada mata Tea mai kauri, ya ajiye gabanta, zai dauko mata egg a cooler Mairo tayi daurin cewa "saura daya, kuma naka ne" murmusawa yayi yace "let her have it then" Mummy ranta bace, idon Nana kamar ya fado saboda harara, cikin natsuwa Najwa ke shan Shayin nan da kwai tana hadawa da biredi har taji muryan Mummy na cewa "Najwa, zo ki kara min Ruwan Zafin nan" zata tashi da sauri Majeed yace "barin kara mata" Mummy tace "Majeed". Najwa ta mai alamun ya bari, zata zuba mata, tashi tayi ta dauki flask din dake kusa da ita ta k'arasa gun da Mummy ke zaune. Bude flask din tayi ta fara zubawa a Mug din dake hannun Mummy a hankali don gudun kar ta k'onata da ruwan don akwai zafi sosai, kawai Mummy sai sakin Kofin tayi k'asa, kofi be dire ko ina ba sai kan kafar Najwa, wani Ihu Najwa ta saki da k'arfi tare da zubewa k'asa sumammiya, Majeed be san lokacin da yayi sauri ya dauketa daga wurin ba, kuka takeyi Sosai, Kofi daya na ruwan zafi ya zube a k'afarta, Daddy yace " Majeed, k'una ne sosai, ka kaita Asibiti" Daukanta Majeed yayi tsam a jikinshi ya fita da ita, da sauri ya dawo daukan Key, nan ne yakejin Daddy nace ma Mummy "Don me zatayi haka? Ya ga lokacin da ta sake ma Najwa Cup a k'afa kuma da gangan" kallon Mummy kawai Majeed yayi cike da 6acin rai, har Mummy taji gabanta ya fadi, amma don bai da lokaci ya sa kai ya fita. Nana cikin 6acin rai tace "Mummy kina kallon yanda yake rawan jiki kan karuwan nan ko? Mummy har daukanta yayi fa" Daddy ya ji takaici, ya tashi ya shige Daki, Mummy tace "Daughter inlaw barni da shi, har ita shegiyar yarinyar, ni na san yanda zanyi da ita, da kanta zata rarrafa ta koma inda ta fito don ubanta, ku dai trust me and keep watching" Nana ta jinjina kai, Zaineema ta ta6e baki tace "kila bata barshi haka ba, yanda yakeyi mata akwai ayar tambaya" Mummy tace "Aiko da bak'ar Ja6a take tsafi sai ta bar gidan nan, mu dai je zuwa". INDIA Kukan da Maama keyi har ya fara ba Paapa tsoro, shima dai yayi kukan don hankalin shi ya gama tashi, babu yanda zasuyo, tun jiya suke tsumayin kiran Najwa amma shiru bata ba alamunta, "is she Ok?"Tambaya dubu da Maama ke tama Paapa kenan, be da amsan da zai gaya mata, be da halin sanin ya Najwa take? Sun kira number wayarta ya kai so nawa dukda suna da tabbacin cewa number ba zai shiga ba amma basu daina dialing numbern ba. "Najwa ta salwanta kamar yanda Zaid ya salwanta, shikenan ni Yesmin tawa ta k'are, ya zanyi Papi? First it was Zaid and now Najwa? Ya Illahi, i cant take it" sai ta fashe da kuka. Pappa sai ya rungumeta, yasan be da bakin lallashinta, shima hankalinshi tashe yake rashin kiran da Najwa batayi ba, Ubangiji Allah yasa tana lafiya, Allah ya sa tana hannu nagari, da ya samu k'arfin guiwa, sai ya hau lallashinta da cewa "Yesmeenah, kar ki tada hankalinki please, yana iya yiwuwa cewa Ta isa, ko wayarta ba chaji, ko kuma bata siya Simcard ba, maybe shes settling, donAllah ki kwantar da hankalinki, she is fine da izinin Allah". Ta tsagaita kukan tace " amma tun Jiya ta tabbatar mana zata kiramu,me ya hanata in komai daidai ne, da ta na Dubai ai da wani number ta kiramu? Meyasa sai a Nigeria ne ba zata kiramu ba? yanzu karfe 3 fa anan, gari ai ya waye a chan, ina jin Tsoro Papi". Shima ya san gaskia ta fada, addua kawai yakeyi a zuciyanshi. PH ng Wani farinciki ya lullube zuciyan Zaid da ya tuna firansu da Alhaji Haruna Mafeci na Hilal Constrution Company Dubai. Tun safiyar yau be sha wahalar Contacting din Alhaji Haruna ba saboda shi din mai Connections ne, a k'asar nan yanzu wa ka sani wa ya sanka ne. Ga yanda firarsu ta kasance; "Assalam Alaikum, My name is Zaid Sadam Audu, i'd like to speak to Alhaji Haruna Mafeci" haba ko ba komai Alhaji Haruna yasan Young multibillionaire Zaid Sadam Audu, tuni Alhaji Haruna ya chanza harshe yace "Ranka ya dade" Zaid yayi Murmushi kamar yana gabanshi yace: "Nasan you are busy, so am i, so lets go straight to the point, shall we?" "Yes please" Zaid ya fara magana "Akwai AbdulMajid Abba Abu dan Nigeria da yayi Aptitude test din Hilal Constructions ran Monday haka ne?"Da sauri Alhaji Haruna yace " Tabbas, wani dan Kano, follow up kake mai? Ai tun rannan nayi assuring dinshi zaa bashi offer InshaAllah, anayin wasu verification ne first kafin nan". Zaid yace "No, ba follow up nake mai ba, actually bana son ya samu aikin nan, he was my employee, so yayi betraying trust dina ne shisa nayi firing dinshi, whatever happens he must not get that offer kagane?" Alhaji Haruna yayi shiru yana nazari, be ga wani illah a tattare da Majeed ba, duk cikin yan Nigerian da sukayi test din, Majeed yafi burgeshi, amma saboda yana so wata rana Zaid Sadam ya mishi Alfarma, ba zaa su dauki Majeed aiki ba. Zaid ya sake cewa "Alhaji Haruna ka fahimta?" yace "Eh ranka ya dade, he wont work with us, kar ka damu" a takaice Zaid yace "Ban damu ba" ya kashe wayan. Ko Minti biyu baayi ba Alhaji Haruna ya mai text message inda yake cewa "kayi hakuri ba wai nace kar ka damu da wani manufa bane, Allah ya huci zuciyarka, AbdulMajid Abba Abu's offer is declined". Murmushi Zaid yayi ya mai reply da "Noted, you wont regret this".(Ikon Allah, wato haka abun yake wa ka sani? Wa ya sanka? Muma Allah hada mu da manya lol). K A N O Emergency aka karbi Najwa, bayan an samu ta farfado, akayi dressing kafan da ya suntume ya kwaye ya kuma yi Jazir, aka rubuta mata maganin shafawa, Majeed ya shiga bata hakuri, tayi assuring dinshi cewa bakomai it was an accident. Haka suka koma Gida da taimakon Majeed take tafiya. Har daki ya kaita, ta fara baccin wahala. Straight dakin Mummy ya wuce, Ita kadai
Chapter 36 · 0% Book details