Sashe 88
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
聽 聽 Kafin safe kafar Ziyada ya ja ruwa ya tashi, ita kadai ta ja kafarta toilet don hawayen sin dauke, tayi alwalar asuba, a zaune tayi sallah saboda sujada, da kyar ta kasa komawa tayi bacci saboda kafanta na zugi, har wurin karfe 10, ganin yunwa zai mata lahani ya sa ta fitowa tana jan kafa, daidai nan Zaid ya fito da jakka me kama da School bag, idonshi kan k'afarta, tana ganinshi ta kara saurin tafiyarta tana cije baki ta shige kitchen, tsayawa yayi na kusan minti 2, kafin yayi tsaki ya wuce ya shiga Motarshi inda Driver ke jiranshi, zai tafi Airport inda jirginsu zai tashi karfe 11 zuwa bauchi.
B A U C H I
6PM
Duk wasu reports din da ake karanto mai hankalinshi be gun, burinshi ya ganta, be san halin da take ciki ba, be san ya k'afarta yake ba, mikewa yayi kamar an tsunguleshi, zumbur yayi hanyar fita daga conference room din, da sauri Manager ya bishi, yace "Sir, you cant leave now, we are in the middle of a meeting(ba zaka iya fita ba, muna tsakiyan meeting)" Zaid cike da damuwa yace "sorry, i cant do this, i've got to go(yi hakuri ba zan iya ba, tafiya zanyi)" Manager yace "Turawan nan are already here, be kamata ace an tara su ba kuma a ki gabatar da taron, babanka ya so kwangilar nan, sai yanzu ta samu, da ya na nan, bana tunanin akwai wani uzurin da zai hanashi aiwatar da taron" Zaid ya kalleshi, haka mutanen nan suke, in har suna so yayi wani abu sai su fara sako Babanshi a ciki, yace abunda zanje yi "Baban ne ya sani yi" Manager yace "Me kenan?" Cigaba da tafiya yayi Manager na binshi a baya Zaid yace "ka koma kace musu nace i'm sorry i cant hold the meeting, there's been an emergency, i need to go home to my wife, kasan su turawa yanda suke so da girmama matayensu, i'm sure they'd understand" ya cigaba da waya聽 "Hello Faisal, book me a flight to Kano" Faisal yace"anya akwai jirgin Kano yanzu kuwa?" Zaid ya buga tsaki yace "Never Mind" Faisal yace "Ya zakayi kenan? Sai gobe?" a takaice yace "Nope, zan tuk'a kaina zuwa Kano" Faisal yace "DonAllah aa, dare yayi, ka jira inzo na kaika, kasan Baba be son kana tuk'i in har ba cikin gari bane" Dif Zaid ya kashe wayan yana Mitan "komai Baba Komai Baba Arrgh" daidai nan ya isa gaban entrance din Reception Company, Motoci ne kala 5 a jere suna jiran fitowarshi, Zaid ya nufa inda ya shiga da zaizo ya mika ma Driver hannu Alamun ya bashi Key, zai mai Gardama Zaid ya buga mai Harara, ba Arziki Driver ya ciro Key ya bashi, ya shiga Mota ya kalle su yace kar wanda ya biyoni, ya burka motan ya fita a Sittin.
Yanda Hanyar Bauchi zuwa Kano a ke samun gargada, haka Zaid ya dauka hanyar nan bayan ya kashe wayoyinsa don ma su Faisal kar su ishe shi da kira, kwarara gudu kawai yakeyi, ya dade beyi tuki da nisa ba, saboda tsaron lafiyanshi ba a bari yayi tuki da kanshi, iyakanshi cikin Gari, kuma duk fitan da zaiyi da convoy dinshi yakeyi, in ya fita personally to da Armstrong ne ko Idi, saidai in yanaso yayi basaja sai ya basu umurnin kar su biyo shi sai yayi nisan 100km, Zaid beyi Sallah Maghrib da Ishai ba sai da ya iso Ningi, komi beci ba ya sake daukan hanya, Tafiya dai na Allah ne, shi ya kawoshi Lafiya. Sai karfe 11:27pm iso garin Kano.
Jami'an tsaro sunyi mamakin ganinshi a wannan lokacin, be iya jira su bude mai Gate ya fita ya shiga Gidan sauri sauri gudu gudu, ya sa mukulli ya bude parlorn ya shiga dakinta a kwance ya ganta tana rawan sanyi duk da bargon da ke jikinta.
A baiyane yace"what have i done?" da gudu ya hau kan Gadon,ya yaye bargon, wani irin hucin zafi ya bugeshi, ya sa hannu ya tattarota gabaki daya jikinshi, bata da karfi da kasala, amma cike da karfin Hali take tureshi daga jikinta tana cewa "ka sakeni, kar ka tabani, ka barni in mutu ni" kara rungumota yake sakeyi聽 ita ma bata fasa tureshi ba, cikin wata irin Murya yace "Ziyaaaaaa"
....
Late night Post, Sorry, kuyi Blaming NEPA,
*Zaid back to his senses?*
*Ta ya kuke son Zaid yayi nadama?*
*Me zuzu zatayi in ta san cewa shine sanadiyar duk wani hawayen da ita da family dinta suka taba zubarwa?*
*Me kuke ganin zaiyi da zata yafe mai da irin cin fuskar da yayi mata da Family dinta?*
*Meye zai faru da Zsquare in kwai ya fashe?*
*Me zai faru da Mairo in kwai ya fashe?*
*Najwa zata amince da Jaan dinta in ta san cewa Mahaifiyarshi ce Ummulabaisin duk wani abunda ya faru da Mahaifanta*?
*Duk zaku samu answers dinku in less than 6 pages to come(yesso ADAY is coming to an end)*.
You know what to do with the Star down there right?
#1love
#ADAY
#Bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode
Biebee Isa.
馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱
NA
BIYasme
Wattpad:@biebeeisa
Pg3鈨�5鈨�
Cikin wata irin Murya yace "Ziyaaaaaa, Keep Calm Please" tureshi tayi da duk wani karfin da Allah ya bata, ta mik'e zaune, tace "meye haka?" kallanshi tayi cikin ido kafin tayi wata dariar takaici, tace "Damuwa a idonka? Karya ne, parts of your tricks? (Wasu daga cikin shirin ka? ) I wont fall again, Allah ya tsarei ni" ta kwanta tare da k'udundunewa.
Girgiza kai yayi da sauri, yana so ya mata bayani, amma be san be zaice ba, yana so ta fahimci abinda ke ranshi, be damu ba in ta sani, be damu in Armstrong zai kalleshi yayi daria yace "I told you so Boss" be damu ba in zai sauka kasa yayi gravelling don ta amince dashi, ba tricking dinta zaiyi ba, daga Bauchi fa yayi risking rayuwarshi and all don kawai yazo ya ganta ya ga ya take, amma abubuwan da ya mata a yan kwanakin nan, yasan ba zata amince da shi ba, tsaki yayi, ya shiga toilet ya dibo ruwan sanyi a dan bowl, ya fito, fita yayi ya dauko hand towel a dakinshi, ya dawo dakinta, tana nan yanda ya barta.
Riga da Skirt na atamfa ke jikinta, Saboda Fever din da ya kamta bata samu kuzarin cirewa ba, ya juyota cikin zafin nama tace "nace kar ka tabani, in ba yankani zakayi ba so kar ka tabani" be kulata ba ya kama zip din rigarta zai zage, tayi saurin buge hannunshi, ta koma ta kwanta, ranshi ya fara baci, meye haka takeyi? He only wants to help, ba wani abu ba, yace "ina so na goge miki jiki da ruwan sanyi don kiji dadi" idonta runtse tace "bana so" a ranta kuwa tace "sai kace ya damu" yace "am not trying to see your body, i just want to help" murmushin takaici tayi, a ranta tace "so yake in amince dashi ya samu damar wulakanta ni a fili kuwa sai tace "I dont want your Help" Zaid ya gama kai koluluwa gurin k'ulluwa yace "Ziyaa, ko ki bari na taimaka miki, ko in je Gidanku in ma Family dinki wani abunda ba zasu taba mancewa ba" idonta a runtse hawaye na bin kuncinta tace "in ka tashi ka kashesu".
Da mamaki ya kalleta, she's in pain abunda ya sani kenan, kar yayi taking advantage ya kara mata wani pain, tashi yayi ya fita daga dakin rai ba dadi, da ta san daga inda ya taho a mota don ita, da ta san risk din da ya dauka yayi tafian dare, da bata mishi haka ba, sha zafin ciwo ne, ya koma dakin shi, saidai ya kasa bacci, waje ya fita ya dauko Laptop dinshi da aka shigo mai da Motarsa, ya dawo Parlo ya kunna yana latsawa, saidai hankalinsa be san abunda yake yi ba, tsaki yayi ya tashi zai koma dakinta, sai ya fasa, sunturi yake a parlo, har wurin karfe 1 yana abu daya, ya yanke hukunci komawa dakin, kila tayi bacci.
Yana kuna wutar dakin ya ganta ta na kaukau da jiki, da sauri ya karasa gunta yana fadin "Ohhhh, Ziyaa, yoi are soooo stubborn" hawa yayi kan gadon ya jawo Bowl din ruwan da ya ajiye kan mirror da towel din, dagota yayi ya kwantar kan cinyarshi, ya sa hannu ya zuge zif din, sosai jikinta yayi zafi, tana jin hannunshi a fatar jikinta, bata yi yunkurin hanashi ba, don bata da karfin hanashi, tana ji tana gani ya dinga tsoma towel din nan yana matsewa ya daura mata a jiki, tun daga kanta, zuwa wuya, baya da kirjinta, tashin hankalin da yake ciki ba zai bari ya kare ma surar jikinta kallo ba, Drawer dinta ya bude ya duduba akwati, ba Sweater ko wani riga me kauri, da sauri ya nufa daki ya dauko Wani Sweater dinshi Hoody, da Wayarsa, sai da ya samata Sweater dinshi kafin ya latsa numbern Dr Emran, ya tambayeshi maganin da ya kamata ya ba Ziyada, ya mishi texting, be da lokacin aiken wani, gani yake ba zaa mai sauri ba, haka ya dauka key ya fita da sauri yace "ku bude min Gate" daya yace "Oga 1am fa" Zaid be tanka shi ba ya karasa gun Mota ya kunna, ganin haka aka bude mishi, Wasu securities suka shiga wata Mota suka bi bayanshi.