← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 128

Sashe 110

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaro wayarshi yayi daga Aljihu,  kamar wani tababbe,  ita ko Najwa ta kasa cewa komai sai kallonshi takeyi, ta tausaya mai. "Yeah Idi,  kira  Francesca,  tell her to book me a Flight now to Ind--" be karasa ba Najwa ta karasa gunshi ta zare wayan da ke kunennshi ta girgiza kai, da Murmushi a fuskarta tace "Ba sai kaje India ba" da mamaki da tsoro yace "Meyasa?" Murmushin ta kara sakar mai tace "Because they are all ready here in Kano" wani irin Ajiyar zuciya ya sake me karfi baki na rawa yace "Baby, shine  muke ta 6ata lokaci?" Daria tayi da ya ja hannunta da k'arfi,  ganin Ziyada tsaye fuskarta tayi Ja da alama kuka taci kuma taji komai  ya sa Najwa turus,  wani kallo ya watsa mata da ya sa Cikin Ziyada murdawa,  kamar tsanarta ta hango a idonshi.

Najwa zata ma Ziyada magana  taji muryan Zaid "Muje Baby" ya jata da k'arfi bata da wani choice da ya wuce binshi a baya, suka bar Ziyada tsaye,  tun daga nesa ya ke kwalawa Driver kira,  da sauri ya karaso "ban key" Zaid ya umurta, Drivern ya dan nok'e,  ganin Oganshi a rude fuskarshi kamar yayi Ja ya san cewa ba lafiya,  yace "Oga,  muje na kaika duk inda zaka" ganin zai bata mai lokaci yayi sa hannunshi a aljihun Drivern ya ciro remote, dannawa yayi yaga ta Benz ce,  har yanzu be sake hannun Najwa ba janta ya cigaba dayi,  driver ya bi bayanshi yana cewa "Oga DonAllah ka rufa min Asiri,  Oga Idi yace kar na barka kayi driving" Zaid be tanka shi ba har ya dangana da mota ya bude dayan side din Najwa ta shiga,   da sauri driver ya zagaya ya bude mai, yana magiyan kar yayi tuki,  Zaid be bi ta kanshi ba shima ya shiga.  Ya danna horn da karfi Mai
Gadi ya wangala gate yana mamakin yau Oga ne da kanshi,  hannunshi ya sa ya lallubo hannun Najwa ya damke kamar zaa kwace mai ita,  Murmushi ta sakar mai na komai ya zo karshe. Nan ya samu karfin guiwa ya tada key,  ya danna kan Motar Wajen Gidan. 
Daga Waje masu tsaro da lafiyan Zaid suka ganshi da kanshi yana tuki, suma suka tada Motar suka bi bayanshi,  don orders ne kar a bar Zaid on his own.
Driver daga ciki ya yi sauri ya shiga dayan Motan zai bisu,  Ziyada ta rugo da gudu tace "jirani" ciki ta fada don dauko mayafi.
Jim kadan ta dawo sanye da Zumbulelen Hijab Odile ya bude mata ta zauna baya,  suka  bi bayan Zaid a guje.

A parlo ta iske Hajia Aynarh na rubutu a wasu tarkadun files, zama tayi kujerar da ke kusa da ita,  tace "Hajia Aynarh,  donAllah Address din Gidan Sada nike so" Hajia Aynarh tayi banza da ita kamar bata ji ta ba, sake maimaita mata tayi, kafin ta aje biron hannunta ta kalleta, a takaice tace "bansani ba" Hajia Mairo ta sanyaya murya tace "Hajia Aynarh,  ki taimaka ki bani adireshin Sada,  donAllah akwai alfarman da nake so ya min" Hajia Aynarh ta kalleta galala tace "wallahi baki da kunya Hajia Mairo,  bayan abunda kika musu,  har kina da idon zuwa gunshi ki rokeshi wata alfarma? Lallai kam"donAllah ni dai ki bani,  banda wani zabi da ya wuce zuwa gunshi,  shi kadai zai magance min matsalata, ki taimaka,  kina yi kamar kin tsane ni,  amma wallahi na dan baki tsane ni ba,  da kin tsaneni da baki taimakeni ba, da bakiyi dawainiya  da ni da su Zeenatu na,  nidai ki taimaka min" Hajia Aynarh tayi jimm,  kafin ta dauki paper da biro tayi rubutu ta mika mata a wulakance tace "Na sha gaya miki,  ba don ke nake miki abubuwa ba da ana abu don ke,  da baayi ba wallahi" ta wuce ta barta zaune. Da sauri Mairo ta mike ta  shiga dakin da take kwana ta dauko dubu biyun da Abdulmajeed ya bata da yazo,  ta zura Hijabinta ta fita tare da ce ma Maigadi "In su Zinatu sun dawo daga makaranta kace na je na dawo" Adaidaita Sahu ta tsaida tace a kaita _Tarauni_.

"Hello Najwaty" muryan Najwa ya karade kunnuwan Paapa "Paapa kana ina? Gida?" yace "ga mu nan daidai kwanar Gida ni da Daddynku,  da AbdulMajeed,  yanzu zamu isa Gida,  Kuna Gidan Hajjo ko?" hakan da yace ne ya nuna mata wani Gida zasu,  "OK,  sai na iso, a ajiye min Appreciation gift" daria yayi yace "Na Mene?" itama darian jin dadi tayi,  tace "wait for it, sai nazo gida" dif ta kashe waya tana kallon Zaid da ya ke tuk'i ta mai murmushi tace "Komai yazo karshe Bhaiy" jinjina mata kai yayi cike da amincewa.
********

Suna Isa Gidan suka shiga da Sallama,  Maama ta musu sannu da zuwa,  ta kawo musu Abinci dining tace bari taje tayi Sallahr laasar, Abdulmajeed yayi serving dinsu Daddy da ke kan Kujerun table din,  shi kuma ya dauki nashi ya koma kan carpet yana ci,  Sallamar sukaji, duk suka amsa suna me kallon k'ofar shigowa,  Mummy ce,  kallo daya Daddy ya dauke idonshi, Abdulmajeed ya mike tsaye yana kiran "Mummy..." yanayinta ya sa sun gane tans cikin wani hali,  duk da ba wai ya son k'ibarta ba, amma,amma ya san cewa ta yi rama ba kamar randa suka dawo Nigeria ba, Paapa yace "Ahh,  Hajia sannu da zuwa Bismillah" zama tayi a kujera idonta fes kan Daddy, durkusawa tayi tace "Ina wuni" ganin Daddy ba amsawa zaiyi ba yasa Paapa cewa "Ina wuni, muna lafiya?" ba ta daddara ba tace "Daddy ina wuni?" dauke kai yayi kamar be san da ita ba,  bata daddara ba fa,  ta mike ta tako inda yake ta zube guiwa biyu a k'asa,   "Daddy, DonAllah ba danni ba kayi hakuri,  ka maidoni dakina,  wallahi na daddara, ba zan sake ba,  ka bani chance,  zan gyara komai, donAllah Daddy" banza yayi da ita ya cigaba da cin Abinci. 
Papa zaiyi magana yaji muryan Najwa na kiransu Maama,  Paapa da k'arfi, mikewa yayi da sauri yana tunanin lafia Najwa ke musu irin kiran nan, Abdulmajeed zai fita ya ga lafia, ta karaso da gudu tana murmushi tana haki,  kafin ya tambayeta meya faru Zaid ya shigo cikin   Parlorn, yana raba ido inda zai ga Mahaifanshi,  Mairo ta kalloshi tana mamakin me ya kawo Mijin Ziyada nan? Nan ta ga Ziyada ta shigo,  tace a ranta"oh ashe tare suke" ba ta damu da ta mik'e tsaye ba,  ta cigaba da durkusonta.

Idon Zaid ya sauka kan Dining Table inda Alhaji Abba da Alhaji Sada ke tsaye, hawaye masu zafi suka soma suntiri a idon Zaid da ya hango Mahaifinshi tsaye, da alamu shi din be ganeshi ba, takawa yakeyi da saurisauri har ya k:arasa gunsu,  be ma kowa Magana ba illah rungume Paapa da yayi, riko na gaskia ya mai,  shi ko Papa Murmushi yakeyi,  ba wai don ya san waye wannan ba ko dalilinshi na rungumarsa ba, zai dago Zaid ya sake matseshi,  su dai yan parlorn sai kallon ikon Allah suke,  Najwa ta ruga daki taga Maama na Sallah, zama tayi kusa da gadon,  ba zata katse mata Sallah ba,  Zaid ya dawo, zai iya jira ta gama Sallah.
A nan kuma Hajjo suka shigo da Zaineema kasancewar Najwa ta kirata tace "ta sa Hajjo a Napep su zo Gida yanzuyanzu". Halin da suke ciki ne ya sa ba wanda ya amsa musu Sallamarsu.
Paapa ya fara kokarin raba jikinshi da na Zaid,  ganin abun ya fara yawa,  kuma yana jin hawayen Yaron a jikinshi,  Zaid ya sake matse shi yanzu kukan harda sheshek'a, Paapa da jikinshi yayi sanyi ya bude baki yace "Bawan All--" Zaid ya katseshi da muryarshi da bai fita sosai yace "Babana" da karfi Papa ya raba jikinshi da na Zaid gabanshi na dukan uku uku ya dago ya kalle Zaid sosai, duk da idonshi a rufe yake don kika yake kamar zai shide, be hana ganeshi ba, amma don ya tabbatar ya sa hannu ya shafa idonshi,  a hankali Zaid ya ware idanunshi,  Papa ya girgiza kai cike da farinciki mara Misaltuwa yace "Zaidu na".

Mairo ta tashi Zumbur cike da zare idona,  kafafuwanta na rawa,  dukkansu na gurin Mamaki ya rufe su banda Ziyada da ta san komai,  Daddy kamar an dasashi yake kallon Zaid, Sake Rungumar Juna sukayi Zaid yace "Baba,  ashe kuna da rai? Ashe zan sake ganinku?  Ina Mamana?" Papa ya rik'e hannun Zaid ya bude baki "YESMEENAH" daga chan daki Najwa tace "tana Sallah" Zaid ji yayi kamar ya ruga dakij ya katse mata Sallahr amma sai ya tausashi zuciyanshi da ya barta tayi Sallahrta su kasance tare.
Paapa murna yace "Zaid aka ce ka mutu, amma ga ka nan,  Me ya faru?" Idonshi ya sauka a kan Mairo,  wata jijiyan saman kanshi ta mike tsaye,  be son ganinta ko na sakwan daya runtse ido yayi yace "Baba,  nima a zatona kun mutu, bansan kuna da rai ba,  da ban bata lokaci ko daya a nan ba,  da na biku chan Indian"
Papa da murna yace "Komai sai da ikon Allah,  Zaid ga Yayana, Baba Abba sunanshi,  ga--" Zaid ya katseshi da cewa "Na san su,  na san su duka"
Paapa yace "Dagaske?" Daddy cikin sanyin Jiki yace "shine Mijin Ziyada ne,  Gatan Marayu na ii" Papa yace "Allahu Akbar its a small world after all,  amma duk ta kare be san yanda kuke dashi ba " Zaid ya runtse ido cikin wani yanayi yace "nasan Komai Baba,  nasan komai"
Da mamaki Abdulmajeed da kowa na Parlorn suke kallon Zaid, wato abunda ya ma Mairo kwanakin da suka wuce yana sane kenan,
Daddy ya jinjina kai yace "Zaid kayi hakuri da yanda ka tsinci rayuwarka,  ka ga wanchan Matar?" ya karashe yana nuna Mairo da yatsa,  ita ko ta sadda kai irin na marasa gaskia. "Itace ta shiga tsakanin ka da Mahaifanka,  wanchan matar Ibilisun dunia ce"
*
Chapter 110 · 0% Book details