Sashe 22
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Nakowa yace "To Alhaji Abba, maganar auren yaran nan, ina nufin AbdulMajid da Nana, ya kamata a zo kan Conclusion, gwara a musu auren tunda sun daidaita kansu, kan AbdulMajid ya sara, sun daidaita kansu? Inji wa? Kuri ya ma Babanshi da ido don yaji me zaice, shima Alhaji Abban, Hajia Mairo ya kalla, da sauri ko tace " Zaa fara maganar" Hajia Sayluba tace "Yaushe? Baby Nana fa ta matsu, gaskia gwara ayi auren, ko cikin satin nan ne, tunda ba wata matsala" Idon Hajia Mairo ya raina fata, to ina ma suka tsaida magana da Majeed, amma don kar ta bata alak'ar su da Hajia Sayluba tace "Shikenan sai ayi bikin k'arshen Sati" ba tare da ta kalla AbdulMajid ba".
Nana ta hau murna harda tashi tana rawa don murna, takaici ya cika Abdulmajeed, rashin kunyarta yafi 6ata mai rai, ace bata kunyar kowa? Gashi gaban mutanen da ake kirarin zasu zama sirikanta take rawa? Be san lokacin da yace "Ba zan Aureta ba, ba zan taba Aurenki ba Nana" dim Parlorn yayi, Baki Hajia Mairo ta bude cike da mamaki, bata taba tunanin Abdulmajid zai watsa ta gaban Mutane haka ba, kafin tayi magana Nana ta fashe da wani irin kuka mai kama da Ihu, Hajia Sayluba da Alhaji Nakowa hankalinsu ya tashi, Alhaji Nakowa na hargowan "Mai zan gani haka Hajji Abba?, ya Danka ke tada hankalin Diya?" Alhaji Abba yace "Decision dinshi kenan, we cant force him in baya so" ran Alhaji Nakowa ya 6aci, zaiyi magana Hajia Mairo ta tareshi da cewa "kuyi hakuri Alhaji, ku ban Miniti Goma, i'll talk sense to Majeed, donAllah kar kuyi fushi, just 10 mins" Jiki na rawa taja AbdulMajeed zuwa dining section, Alhaji Abba da Ziyada suka rufa musu Baya.
Hajia Mairo ta tallabo fuskar Majeed da ya kada yayi Jazir yana huci kamar Zaki tace "Yaro, meyasa kakeson kunya tani a idon jamaa? Meyasa kake son tona min Asiri?" da mamaki yace "Mummy ki gaya min hanyar da nake son kunyataki, taya zan kunyataki?" AbdulMajeed rashin Auren Nana na nufin ka kunyanta ni, ka tozartani, ka sa nayi karamar magana, na mata Alkawarin Aurenka, ka taimakeni, bana son Alak'ar mu da su ta yanke, ka kalla yanzu, Millian 20 suka bamu, don rashin da mukayi, waye zai dauki zunzurutun kudi har miliyan 1 ta baka a wannan maran ta buhariyya? Wa zai baka miliyan 1 kyauta? Amma ji kyautan Miliyan 20, an ninka maka abunda aka karbe ma, ai ko don wannan dole ka Auri Nana" Alhaji Abba yace "Aa Maryam, ki bishi a hankali, in fa yace baya so ba zamu tilasta mai ba" Hajia Mairo ta fashe da kuka "Kaima ko Abba? Yanzu in sukace zasu kwace kudin fa? In suka datse wata Alak'a da mu fa? Ai asirin mu ya tonu, Majeed ka kasa ganewa, auren Nana Alheri ne, ba zamu ta6a karayar azziki ba, yanzu daba su tallafa mana da kudin nan ba, ba ka tunanin zamu fada kwata haba Majeed" Ziyada ta kalli Hajia Mairo sama da k'asa tace "Mummy You Sold Ya Majeed's happiness for 20million? I'm not suprised Mommy, kin fi san kudi kan yaran cikinki" da sauri Hajia Mairo ta juyo ga Ziyada tace "Haba Ziyada, kar kice haka, Wallahi kune farincikina, i want a better future for all of you" Kukan da takeyi ne ya sa Ziyada shiru, Mairo ta cigaba "na maka abunda kakeso tun kana ciki, nayi abubuwa da dama don saboda kai da k'annenka, nima kamin just this one thing, please Majeed, in sonta ne bakayi da anyi auren za ka soma sonta" cikin daga murya yace "wai kinsan wacece Nana Nakowa kuwa? Yarinyar da bata da tarbiya, yarinyan da ake mata kirarin 'Nancy mai maza da mata?' yarinyar da ke shan kayan maye? Is this the kind of girl you want to call a daughter inlaw?" Hajia Mairo ta dauke wuta dif, da ido ta ma Alhaji Abba magana da ya tausasa danshi.
Alhaji Abba yace "AbdulMajeed, kana da shaidan tana aikata wadannan abubuwan da ka lissafo? Ka yarda ran kiyama a tsaidaka a muku hisabi? Ka taba ganinta da idonka ko gaya maka akayi?" jiki a sanyaye yace "ban taba ganinta ba, ji nayi ana fada" Alhaji yace "to kayi saurin yin Istighfari, yana iya yuwa sharri ake mata, kuma ko ba sharrin bane, kai ba ka gani ba, muma bamu gani ba mu dinga aiki da zahiri, kar ka manta zato zunubi ne ko da ya zama gaskia". Istighfari yayi a zuciyar shi, Mairo tayi karaf tace " Ai mutane akwai shaidar zir, don an ga Ubanta na da Azziki shisa ake mata Hassada" a dake Majeed yace "Whatever dai, Nidai ba zan aureta ba". Kafin su ankara sai jin Ihun Hajia Sayluba sukayi, da gudu suka baiyyana a Parlorn, Nana ce rik'e da wata irin zuk'ekiyar wuk'a.
*
Kanta suka yi duka, hankalin Alhaji Nakowa a tashe, yace " Nanana, kiyi hakuri, ki ajiye wukan nan, ba a wasa da wuka" cikin karaji tace "wasa da wuk'a? Kana tunanin wasa da wuk'a mikeyi?" wukar tasa daidai saitin hannunta ta yanka, a lokaci guda suka sa ihu, Jini ya far fita daga hannunta, ta nuna su tace duk wanda ya matso kusa dani zan chaka mai, AbdulMajid yana matsowa tace "Wallahi zan kashe kaina idan har baka amince zaka auren ba" ta karashe tare da daura wuk'ar kan wuyanta, Hajia Sayluba ta zube gaban Majeed tana kukan ya taimaketa, ba zata iya rasa Nana ba, ita kadai gareta, Alhaji Nakowa ma magiya yake mishi, Hajia Mairo a kidime, kowa hankali tashe. Nana tace "Majeed ka ban amsa, na baka nan da 15seconds, idan baka ban amsa daya ba Wallahi zan lumama cikina wuk'a". Irge ta fara.
Yanda Majeed yaga yanayinta ya ga tana bulayi yasan ta sha wani abu, tana iya kashe kanta a banza, ga jini na zuba ta hannunta, tana kawowa 5 da sauri yace " Na amince Zan aureki" murmushi tayi tace "ka rantse" ba watawata yace "na rantse da Allah zan aureki" tace "ranar juma'ah" guntun tunani yayi yace "gobe ne jumaar fa" wukar ta kara dadirawa a hannunta, da sauri ta fasa ihu shima yace "Na rantse gobe zan aureki Nana, donAllah kar ki k'ara illata kanki" murmushi tayi ta sake wuk'ar tare da zubewa k'asa,da sauri duk sukayi kanta.
Asibiti suka kai Nana akayi dressing hannun, tasha bacci na kusan awannin 5, tana farfadowa ta sa aka sallameta, a cewarta Amarya ce ita, bai kamata ta kwana Asibiti ba. Majeed fa??.
Tunda ya kulle kanshi a dakinshi bai sake budewa ba, kanshi yayi zafi, wai shi ya amince da auren Nana? Kuma gobe? Wai Nana? Kanshi ya rik'e sakamakon sarawan da yakeyi, yana ji Mummy na k'wank'wasawa yayi banza da ita, tayi tayi ya bude har ta gaji, haka zata koma jiki a sabule.
Sai da akayi Sallahr Maghrib AbdulMajid ya fito yaje Massalaci, ko da ya dawo daga Massalaci ya iske Mummy a dakinshi, fuska ya daure, ya samu guri ya zauna, da sauri ta dawo gunshi, ta rik'o hannunshi tana kuka "AbdulMajid, nasan yanzu katsaneni, me zanyi ka fahimci duk abunda nakeyi don kai ne? Kana tunanin zan taba cutar da kai? I want the best for you, Nana isnt bad, tana da kyanta, da gatan ta, donAllah ka kwantar da hankalinka" da ya ga zata matsa mishi yace "Mummy just walk out" kuka ta fashe mishi dashi, AbdulMajid sarkin tausayi tuni Zuciyarshi ta karaya, nan ya hau lallashinta ya tabbatar mata da zai Auri Nana..
*
Amsa kiran wayar tayi da "Hello" muryan da ta ji ne ya sata tuno da mutumin da suka hadu shekaranjiya a Silverbird, murmushi tayi kamar yana gabanta, ji tayi a tak'aice yace "fill me in" da murna ta fara koro bayani tace "ai in gaya maka, komai yayi daidai, nabi shawararka, gashi ya amince, gobe zamuyi Aure" "Good,kiyi insisting kan ayi muku dinner a goben, a beautiful girl like you deserve a Wonderful wedding" murmushi tayi wanda har ranta taji dadin kodata da yayi,a fili tace "zaka zo ko?" yayi murmushi yace "i wont miss" duk da bata sa ko waye shi ba, amma tana jin kanta da bin duk wani umurni nashi, dole kuwa a musu Dinner Party, bari ma ta kira Wedding Planner.
Bayan Sallahr Jumaa aka daura auren Abdulmajid Abba Abu da Amaryarsa Nana Asmau Nakowa bisa sadaki Naira Dubu 100, mutane ke cincindiron yi ma Alhaji Abba murna, AbdulMajid yak'e kawai yakeyi yana gaisawa da mutane.
Abunka da masu kudi, tuni aka hada wani Dinner a The Sheraton Abuja Hotel.
锟�
聽聽 *
聽 Amstrong ya kalli Zaid yace "All set sir, we can go into the mansion now"kafin ya juya ga yanmata biyu da ke zaune bayan motan sanye da Atamfa riga da skirt, yace "get ready girls"Zaid ya furzar da iska tare da danna horn a gidan,Maigadi ya bude k'ofa ya karasa gaban Mota tare da lek'awa, Zaid da ke gefe yace "Mallam Hadi ya aiki" Mallam Hadi ya yashe baki ganin an ambaci sunanshi "Aiki alhamdulilah" daya daga cikin matan dake bayan mota tace "sun wuce gurin Dinner din ko?" Mallam Hadi yace eh sun fi Awa daya da tafiya, Zaid yace "Abokan Abdulmajid聽聽 Ango ne daga Lagos, mun kirashi a waya yace yana wurin dinner ya aiko mana da key din part dinshi yace muzo mu shirya kafin mu iske su a Hotel din, ya ma ce in mun gama Falalu ya kai mu gun dinner" Zaid ya karashe tare da daga Makullan, Mallam Hadi yace "ai kuma Falalu ya tafi gun dinner shima, nikadai aka bari" dayar tace "ba Sheraton Hotep bane? Ai nasan gun, muje mu shirya kafin a tashi" Mallam Hadi ya wangale Gate suka shiga ciki zuciyarsu fari k'al.