Sashe 47
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mummy tace "kai wani irin sakarai ne? Cutarka takeyi wallahi, yaudararka takeyi" Majeed ya kalli Najwa ya kalli Mummy yace "Allah ya san da Zuciya daya nake zaune da ita, inta cuceni ita da Allah, zata cigaba da zama damu har sai randa tayi niyyar tafiya Gida, So Mummy please, this should be the last time, Enough is Enough" Mummy ta bude baki cike da mamaki, Najwa kuwa taji ba dadi, anya Majeed ya chanchanci haka? Kallonta yayi yace Zo Najwa, yayi gaba, da sauri ta bi bayanshi. * Mota ya shiga ta bi bayanshi, horn yayi aka bude musu gate ya fita daga gidan, ba me ce ma danuwanshi k'ala, sun danyi tafiya kafin ya shiga wani katafaren guri, daga sama ta karanta *Farm Center* ya dan kalleta yace "i'll be right back" duk da hawayen da takeyi sai da ta murmusa, ya fita, ba a fi minti 20 ba sai gashi ya dawo da leda a hannu, ya mik'a mata ta kalleshi, yace "karba mana" ta sa hannu ta amsa, ta bude, kwallin waya ta gani *Gionee P2* ta dago kai ta kalleshi, ya murmusa yace "You can call Maama whenever you feel like, simcard din sai after 24 hours zai zama active, kiyi managing, na san its not like your Iphone6, amma--" katseshi tayi tace "Allah ya saka da Alheri, Allah ya biya, Nagode, i cant thank you enough" Murmushi yayi, ya kunna mota suka dau hanyar Gida, sai da ya tsaya Eatery ya siya ma su Ziyada Snacks, a hanya yake ce mata "Najwa, ki k'ara hak'uri Kinji? Everything will be Alright" farinciki takeyi, ta ma mance da abunda ya faru, wannan wayar ya share duk wank bakinciki Mummy, ba zata iya gode ma Majeed ba, anya ta mai adalci kuwa? Bari dai ta gani, if he's worth her trust. WASHEGARI Kallonta yayi da takaici, baya tunanin ko Asuba tayi, gari ya gama Wayewa, 8 saura, tun dazun ya ke ta neman Credentials dinshi amma ba alamun su, ba inda be bincika ba, da ya ga ya kusa zautuwa da nema, ya sa shi buga Nana"Nana nah, tashi donAllah" bacci be isheta ba, syrup din da ta kwankwada jiya ba su saketa ba, cikin magagin bacci tace "My Majeed, ka barni donAllah, kaina na ciwo" sausautar da murya yayi ace "Ki daure ki tashi kiyi Sallah" ko motsi bata k'ara ba, zuwa yayi ya dagata Sama ya sada ta da toilet, yana jin tana mishi mita yayi mata shiru. Sai da ta idar ya ke ce mata "Nikam Nana baki ga inda na ajiye folder din Credentials di na ba?" gabanta ya yanke ya fadi, in-ina ta soma yi "aa, aa wallahi, bani na dauka ba" jin yanda tayi maganan ya sa shi dakatawa ya kallota sosai, jijinta ya fara rawa, mamaki ya rufe Majeed, me ke sa Jikinta na rawa? Sai kace mara gaskiya? Majeed ya danyi nazari, ji yanda take wuk'i wuk'i da ido, anya kuwa?. * Dabara ta fado mai yace "Kin kaima Daddynki ne ya nemo min Aiki?" baki na rawa tace "Aa" Majeed yace "to wa kika kai mawa?" bakinta na karkarwa "Wani ne yace in bashi Credentials dinka zai sama maka aiki a Inland Revenue" Majeed yayi k'uri yana kallonta, ji yake kamar ya fadi don wani jirij da ke dibarshi, a hankali yace "Nana sai ki bashi Original Copies? Ina kika taba ganin anyi haka? Haba Nana, ba wannan ba, kirashi yanzu kice mai zanzo in karba Original Credentials din, in yaso sai in bashi photocopy, Nagode". Tayi shiru, ko motsi ta kasa, ya sake cewa " kirashi Nana" baki na rawa tace "banda Numbernshi, da Private Number yake kirana" ruf ruf idon Majeed ke kullewa yana budewa, baya son yarda da abunda kunnuwansa suke jiye mai, yayi kamar beji me tace ba, ya sake tambayarta, "Nana, ki kirashi yanzu inje in karbo Folder na" da tsoro ta sake maimaita mai "Banda numbernshi, ban san da me zan sameshi ba, shi ke kirana ba nike kiranshi ba, yace in aikin ya samu zai gaya min, suprise nake son yi maka, shiyasa ban gaya ma ba" jin shiru be amsa ta ba ya sata kallonshi, ganinshi tayi a k'asa, a kidime ta karasa gunshi, ba ta san yanda akayi ya yanke jiki ya fadi ba. Ihu ta sake da k'arfi tare da fashewa da Kuka, kukan da takeyi ne ya hada kan 'yan Gidan Gabaki daya a dakin. Mummy kamar tayi hauka, ta tataro Majeed jikinta tana kiran Sunanshi, Hajjo kadai tayi tunanin dauko ruwa ta yayyafa mai, ina be ko mosta yatsa ba, Ziyada da sauran Yaran sai kuka suke tayi, Najwa ma fuskarta yayi Ja, duk cikin tashin hankali suke, Daddy yace "Ziyada kira Fallalu akai shi Asibiti" da gudu Ziyada ta fita. Chan sai ga Fallalu nan yazo, aka Cicibeshi akayi Asibiti dashi. Daddy yace "su tsaya a gida" shi da Mummy da Nana suka tafi Asibitin. ****** Masoya ga Wani Babin, ya kuka gani? Spoiler Alert; Zaman Nana ya kusa k'arewa a gidan Abba Abu, kuma akwai sabon Member a gidan, Guess who?. Har yau ba zan fasa gode muku da kuke kasancewa tare dani ba, na san bana muku update akai akai, Wallahi i've been busy ne, in nace zan dinga yi a kai akai zanyi shine fiii sha a wuce gurin, kuma ba zai yi dadi ba, kuma ba zaku so hakan ba, Nafiso na natsu na muku a tsanake, da haihuwar yuyuyu gwara daya kwakwara. Ku cigaba da kasancewa tare dani. Ehen Wattpadians! You know i love you ko? Show me love Vote and Comment line by line please. #1love #ADAY #bibiliciousfreakingfans #anatare #nagode 馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱 NA BIEBEE ISA 庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Wattpad:@biebeeisa Pg2鈨�2鈨� Ka sa sukuni tayi, duk yanda ta so ta daure ta kasa, toilet ta ta kunna pampo shige tare da fashewa da kuka, kuka take sosai kamar an aiko mata da sak'on Mutuwa, bata san ta shak'u da Majeed ba, bata san zata shiga damuwa haka ba, me ya sameshi? inalillahibwa ina ilaihir rajiun, Allah ya baka lafiya, ban san ne zanyi ba if anything should happen to you Ya Majeed". Sheshekar da takeyi ya fara k'ara, Hajjo da Ziyada da ke cikin damuwa suka k'ura ma K'ofar Toilet din ido, Hajjo tace "Ziyada, kamar kuka nakeji" Ziyada ta dan kasa kunne tace "Najwa ce" ta mik'e don dubota. K'wan k'wan ta kwankwasa mata, "Najwa bude K'ofar" Najwa na jin muryan Ziyada tayi saurin wanke fuskanta, ta fito, bata san sunji Kukan da take tayi ba, ta murmusa cikin rashin gaskiya, Hajjo tace "zo nan Najwa, menene abun kuka? Addua ya kamata ki mishi, zaiji sauk'i da yardan Allah" kamar jira take yi ta sake fashewa da Kuka. Ziyada ta ga Najwan ma tafita shiga damuwa, ba zata yi mamaki ba, don Yayanta akwai shiga rai, balle ita da ya taimaka, ya fiddo ta daga rana ya sata inuwa, kamo hannunta tayi, tace "Najwa, kar ki karya min Zuciya donAllah, ba abunda zai sameshi, he'll be fine, kar ki damu" Najwa ta rik'e hannun Ziyada gam, tace "Mu bisu" Ziyada ta zaro ido tace "what?" Najwa tace "Mu bisu Asibitin, muje muga halin da ya ke ciki, hankalina ba zai kwanta ba, please Ziyada" Ziyada tace "Daddy yace mu zauna a gida har su dawo" Hajjo da take sauraronsu ta hadiye yawun da ya k'afe a bakinta, ta karanci soyayya da shak'uwa tattare da Najwa, chan sai tace "tashi kuje Ziyadatu, nasan kema kina son zuwa, tashi kuje in kin san Asibitin". Ziyada tace " Na sani" tuni Najwa ta saka Hijab, Ziyada kuma ta yafa mayafi, suka fita daga dakin, Ziyada na karantar Najwa, duk ta fita hayyacinta, ta rasa sukuni, sai da Ziyada ta rik'e mata hannu don ta k'arfafa mata guiwa, A daidaita sahu suka samu, suka fada mishi Asibitin da zasu, suka shiga, ba me magana, kowa da abunda zuciyarsa ke sak'a masa. Asibitin fa?. * Suna Isa Asibitin akayi da Majeed Emergency, nan da nan Maaikatan Asibitin suka karbe shi a ka dukufa aiki, Mummy, Daddy da Nana sai safa da marwa suke, Mummy ta kalli Nana rai bace tace "meya same shi, me kika mishi?" Nana jiki ya hau rawa, bata taba ganij Mummy ta mata magana a irin yanayin nan ba, cike da bacin rai da fada, to me zata ce mata ya faru? Tsoro duk ya kamata, tace "nima ban sani ba" Mummy ta dan kura mata ido tana san karantar abu daga ciki, tace "in wani abu ya same Yarona, I will kill you Nana, na san duk kece, bari ya tashi, dama ba sonki yake ba, wallahi in ya gaji da zama dake sai ya sake ki, ni ban kashe Yarona ba, kema ba zaki kashe minshi ba " Nana ta tsorata matuk'a ta rasa abun yi, ta tsura a guje kamar Mahaukaciya. Daddy ya dafa kafadun Mummy yace "Easy Maryam, ba abunda zai sameshi, bari muga fitowar Likitocin". Haka suka dinga sunturi, daga reception zuwa gaban dakin Emwrgency, kusan Minti 15, sai ga Ziyada da Najwa kamar an jefosu, Fallalu Direba suka gani waje ya nuna musu inda su Nana suke. Mummy na ganin su bata yi magana ba, don bata da energy din magana, ita hankalinta kachokam yana gurin Yaronta, bata san halin da yake ciki ba, ya zatayi?. Daddy ne yace "Yadai Ziyadatu? Ba nace ku tsaya gida ba?" Ziyada tace "Sorry Daddy, hankalin mu ya kasa kwanciya ne". Daddy yace "ba abunda zai sameshi da yardan Allah, ina su Zinatu?" a hankali Ziyada tace "suna gida" Daddy ya jinjina kai, idonshi ya sauka kan Najwa da ko magana ba ta iya yi, kallo daya yayi mata ya san cewa taci kuka sosai, fuskarta yayi Ja Sosai, idanunta sunyi luhuluhu, haka kurum yaji tausayin Najwa, Daddy yace "Its Okay Najwa, he will be fine" kai kawai ta iya daga mai, Mairo bata da lokacin kallonsu balle ta tanka musu. Suna hakan ne Dr's din suka fito, gabaki daya sukayi kansu, Dr Hisham yace "ku muje Office" da sauri suka yi hanyar Office din, saida Mairo ta rigasu duka, sai da Dr Hisham ya zauna ya kalli Daddy yace "Alhaji Abba, Meke sa