Sashe 67
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 7 min read
Har wurin 9 suna tare,聽 da zai tafi ta kirasu Aunty聽 don聽 su mai Sallama, ya ciro rafar dubu daya ya ba su Zinatu su siya Chocolates,聽 dadi da murna suna tsalle suna cewa "thank you Uncle Zee".
Washegari, Alhaji Labaran da wasu mutane biyu suka zo mansion din,聽 Majeed da Alhaji Abba suka tarbe su hannu bibbiyu,聽 suka shiga nuna musu kai聽 ina na Gidan, Hajia Mairo kamar ta fashe don takaici,聽 sai huci take kamar zakanya,聽 Alh Labaran yace "Ahh gida yayi kyau sosai,聽 nawa aka ma gida kudi?" Alhaji Abba yace "Miliyan arbain" Alhaji聽 labaran yace "in baka talatin mana" Alhaji Abba yace "ka dai bada arbain din" haka sukayi ta ciniki har suka Amince a milliyan talatin da biyar" nan take Alhaji Labaran ya basu kudinsu cif ta hanyar cheque, aka bashi Takardun gida duk sukayi signing gaban shaidu,聽 ya kuma basu sati daya su kimtsa don zai tare聽 da Iyalanshi shima,聽 Alhaji Abba yayi godia聽 suka rabu cikin mutunta juna.聽
Daddy ya mik'a ma Abdulmajeed Cheque din yace suje suyi cashing a bank,聽 hajia Mairo ta fashe da kuka duk suka juyo suka kalleta,聽 Daddy聽 yace "yadai Maryam?" cikin kuka tace "yanzu shikenan聽 kun sayar da gidan nan? Yanzu shikenan聽 mun rasa gidan nan?聽 Yanzu shikenan?" Daddy yace "Maryam,聽 kin fiye rigima,聽 yanzu in ba a sayar da Gidan nan ba,聽 ta ya kike so a biya Alhaji Nakowa hakkinshi?聽 Wannan ruwa fa ke kika ballo mana shi, kuma da kike tada hankalinki,聽 ai muna da rufin asiri,聽 Allah ya sa muna聽 da gidan Mama, ba abunda gidan yayi,聽 Abdulmajeed ya tabbatar da hakan,聽 shara kadai Gidan ke bukata, barin gidan nam ba karshen rayuwarmu bane, da sauran kudin miliyan biyar sai mu fara bussiness duka,聽 mu rufa ma kanmu asiri ba sai munyi karya ba,聽 so banga abun tada hankali ba" sukayi gaba ita kuma ta dinga cizgar kuka.
Suna isa Bank suka bada cheque bayan verification da komai aka musu cashing kudadensu, a cikin largest sized Ghana Mustgo guda uku, da taimako jamian banki suka fito聽 suka sa a booth, suka juyo,聽 a cikin Mota Majeed ke cema Alhaji Abba "Daddy,聽 ina ga a kira Alhaji Nakowa yazo a je Kotun,聽 barin kudin a hannu hadari ne" Daddy yace "haka ne, bari in kirashi" Majeed ya cigaba da tukinshi, yana sauraron Daddy na waya da Alhaji聽 Nakowa;
"Eh聽 Alhaji,聽 ga kudin nan a shirye,聽 sai ka shirya kazo kano a je kotu mu biyaka a gaban shari'ah" Alhaji Nakowa be kai ga bashi amsa ba,聽 Majeed yaci wani wawan birki k'iiii, "inallilahi wa ina ilaihir rajiun"cewar Daddy聽 ganin wasu garada majiya karfi sun fito daga wata mota fuskarsu rife da mask,聽 hanyensu rik'e da Bindigogi, Majeed be ankare da me ke faruwa ba sai da ya ji bindiga kan kwakwalwar kanshi,聽 cikinshi ya bada k'ululu,聽 da kaukausar murya yaji ance "ku fito" da karfin hali Majeed yace "saboda聽 me?" da hargowa mutumin yace聽 "saboda me? Zaka fito ko sai na tarwatsa maka kai da bullet din cikin bindigata?" zai sake magana Daddy jiki na bari yace "Shiru Majeed,聽 fita" jim Majeed yayi kafin ya fita hannunshi kan bayan kanshi, haka ma Daddy,聽 sauran su ka shiga bincikar Motar,聽 har suka fito da manya manyan jakunkuna Yunkuro Majeed yayi don tsaida su,聽 babban cikin ya harbi k'asa don tabbatar mai da cewa akwai Bullet ba bindigar bogi bace,聽 Daddy yayi saurin聽 kama Majeed,聽 duk jikinsu rawa yake,聽 suna ji suna gani suka shige motarsu da kudaddensu,聽 Majeed ya fashe da wani kuka mai karfi,聽 ya zube a k'asa,聽 Daddy聽 kasa motsi yayi,聽 mutane don rainin wayau sai lokacin sukazo suna lallashinsu,聽 wani yace "saboda聽 ya ga suna da bindiga ne shiyasa beyi yunkurin taimakonsu ba" basu ce musu uffan ba,聽 Daddy ya cicibo Majeed ya tura shi cikin Mota, shima jiki a sake ya shiga driver聽 seat ya ja motar ba me cema kowa komai tsakanin shi da Majeed, nearby Police Station Daddy yayi.
Suka fita don zuwa bada report,聽a cikin Police station din ne Daddy ya nemi ganin On duty,聽 duk ciki ba wasu police din kirki, a tsiyace polisawan ke kallon Daddy, Daddy yace "Oga, danAllah ku taimaka mana,聽 yanzu yan fashi suka tare mu suka karbe mana kudadenmu" da rainin聽 wayau suke kallonshi,聽 har wani inspector yace "kuje ku siyo paper da biro wanda zaayi report dashi" Majeed ya dago rinannun idanuwanshi yace "mu siyo paper聽 da聽 biro? Seriously? Wasu irin聽 maakaita ne ku? Kuji tsoron Allah" wani kofur ya daga musu murya ta hanyar聽 cewa "Kai Yaro,聽 ka iya bakinka" ganin zasu bata musu lokaci聽 Majeed ya riko hannun Daddy聽 yace "mu tafi Daddy,聽 wadannan mutanen聽 ba abunda zasu iya mana,聽 ku kuma kuji tsoron Allah" ba su jira komai ba,聽 suka fito jiki a sanyaye,聽 sukayi hanyar Gida.
Da kyar suka koma Gida,聽 kafan su na nauyi suka shiga gidan,聽 Mairo na ganinsu gaban ta ya fadi,聽 a jikinta taji wani abu ya faru,聽 da sauri ta karaso gunsu tana tambayar abunda ya faru,聽 cikin sanyin jiki Daddy ya karanto mata abunda ya faru,聽 Ihu ta kwallara da karfi kafin ta zuve k'asa sumammiya,聽 duk suka yo kanta, Najwa da ke daki ta fito a guje, Majeed聽 ya cicibota ya rungume yana hawaye,聽 daddy tsaye yayi kansu,聽 Najwa na ganin聽 haka tayi fridge ta dauko ruwa,聽 ta bude ta fetsa mata,聽 Attishawa Mummy tayi,聽 tana farfadowa ta sake tantsawa ihu,聽 Majeed ya rikota,聽 ya rungumeta yana shafa bayanta har sai da ta natsu,聽 cikin kuka take cewa;
"Wallahi karyan Manahuki, karya kake Alhaji Nakowa,聽 nasan aikin ka ne,聽 nasan yin聽 ka ne haka,聽 karya kake ka Aiko聽 a mana fashi,聽 in ba haka ba wa yasan da kudin?" Daddy yace "aa Maryam,聽 banda zargi, na dai kirashi lokacin聽 da muka fito daga聽 bank nace yazo kano aje Kotu,聽 kafin ya ban amsa sukazo,聽 so ban tunanin shine" Mummy tace "kaiya Daddy, baka san waye Alhaji Nakowa ba,聽 ba a shaidarshi,聽 mutumin nan Shaidan ne me suffan mutune,聽 Wallahi聽 Gobe聽 zan ma Abuja dirar Mikiya".聽 Daddy yace "aa Maryam, kar ki zarge shi,聽 ba muda wani hujja,聽 i think zanje chan Police Headquater, muga ko za a dace"
Majeed yayi saurin cewa "Ba abunda zasu iya聽 mana Daddy,聽 ai yanzu mu ba kowa bane,聽 bamu da kudi,聽 yanzu ai talaka be da wani k'ima a idon dunia,聽 talaka baida wani gata sai Allah,聽 shikenan mun rasa kudin nan, Daddy kudin nan sun tafi,聽 Allah in wani abu mukayi maka kake hukunta mu ta wannan hanyar,聽 Allah ka yafe mana,聽 Allah ka Iyakance mana,聽 Allah ka kawo mana Sauk'i,聽 Allah ka bamu ikon cin jarabawar nan" Daddy ya dan matse kwallah,聽 yace Ameen Abdulmajeed,聽 Allah Ameen Ya Rabb". Najwa tayi saurin shigewa daki tana kuka,聽 tausayinsu ya rifeta gabaki daya.
Bayan wasu yan kwanaki
A yau suka dawo Gidan Hajjo da zama,聽 bayan an kai ruwa rana da Mummy,聽 a cewarta ba zata dawo ba,聽 Alhaji labaran da Alhaji Nakowa聽 suka hada baki suka ha'ince su,聽 har gaban Kotu,聽 Alhaji聽 Nakowa yayi rantsuwa kan be da masaniyar abunda ya faru,聽 Alhaji Labaran ma haka,聽 da haka Kotu ta kara musu聽 lokaci har wata 5 kan su聽 biya Alhaji Nakowa聽 kudinshi don yace be yafe ba,聽 Gida聽 kuma su tashi don Alhaji聽 Labaran na da bukatar tarewa da Iyalansa.
Hakan yasa聽 Daddy da Majeed sukayi ta lallaba Mairo har ta yarda suka koma Gidan Hajjo,聽 kallo daya zaka聽 musu ka san cewa suna shan wahalar rayuwa,聽 komai na babban Gidan,聽 harta Motocin su biyu sun saida,聽 gadajensu da komai suka聽 saida,聽 kudin ko miliyan shidda be rufe ba,聽 haka suka damk'a ma Alhaji Nakowa sukace gashi su fara rage bashi da miliyan biyar, duk da suna da tabbacin nan da shekara 5 ba zasu iya hada Miliyan 25 ba,聽 amma ana so su hada miliyan biyar cikin kwanakin da basu kai shekara ba? Amma basu san gaibu ba,聽 Allah Aalam,聽 shi kadai ya san yanda zaiyi dasu,聽 but聽 for now,聽 dole聽 su aje komai a gefe su kama sana'a,聽 su gina sabuwar rayuwarsu.
Tafiya ta kama Aunty Aynarh,聽 zataje Abuja inda zaa mata Promotion Aptitude test,聽 ta kira Daddy ta sanar mai,聽 da karfin hali ya mata addua yace "zai turo Majeed ya kwashi yaran,聽 mungode Allah ya saka聽 da Alheri" tace "Aa Alhaji Abba,聽 ba wai ina nufin azo a dauke su bane,聽 na gaya mane don kawai ka min聽 Addua,聽 amma menene don nayi tafi na barsu?" Daddy yace "ba wani abu bane,聽 amma ina ganin ya kamata聽 su dawo Gida hakan nan,聽 komai聽 ya lafa da yardan Allah, mungode Allah ya bar zumunci" ba yanda batayi ba amma yace "aa gwara su dawo su rungumi聽 kaddararsu,聽 gwara su dawo su ci damaran zama聽 haka har karshen聽 rayuwarsu har sai Allah ya kawo mana sauki" numfashin ta ta ja ta sakar tana me tausyinshi,聽 ta ji labarin yanda suka sayar da Motocinshi da duk wata kaddarar Gidanshi,聽 ta na ganin zata聽 iya taimaka聽 mishi ta hanyar rage mishi dawainiyar Yaranshi,聽 amma kuma gaskia ne abunda聽 ya fada tace "zan kawo su bayan Maghrib InshaAllah" ya mata godia sukayi Sallama.
*
***