← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 128

Sashe 37

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

ce zaune Daddy ya tafi bugabuganshi. Kallo daya ta mishi ta dauke kai "Mummy, what were you doing? Mummy nasan da gangan kika saki Cup dinnan, Mummy me ta miki kika tsaneta? Idan baki yarda da ita ba then fine, but please dont hurt her, yarinya ce, just like Ziyada, ya zakiji in wasu sukayi maltreating Ziyada kamar yanda kikayi? Sai inda karfin ki ya kare ai? Zaki taka wanda ya taka yaranki Haka kike cewa Mummy, So Mummy Consider Najwa's Mom, ya zataji? Itama zataji kwatankwacin abunda kika ma diyarta, donAllah Mummy ki bari, abunda baka so a ma danka kar kayi ma dan wasu, Mummy please, zata cigaba da zama da mu for sometime, zata koma gidansu, kinji?". Galala take kallonshi, wato Majeed saboda wannan tsinanniyar yarinyan ne yake mata Waazi? Lallai kam, ba abunda taji, illa ya shiga ta nan ya fita tanan,sai ma Wutar kiyayar Najwa na ruruwa a zuciyarta. Tsaki ta buga da k'arfi tace" Majeed kar kaga Ina abubuwan da kakeso kace zaka dinga yanda kakeso dani, daga kallo daya naji wani irin tsanar yarinyar Mai karfi, you cannot change that, kuma in zata zauna wallahi sai dai boysquaters ba dai cikin Gida ba, ganinta na k'ona min rai, ta fitar ma Ziyada a daki" haka Mummy ta dinga surfa Masifa. Ina Majeed bata kanta yake ba,be tare da ita hankalinshi ya karkata ga Email dinsa da akayi notifying din shi ta Wayarshi, "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" yace tare da dafe kai. Da ta lura hankalinshi be gareta sai cewa tayi "Wato 'yar iska ka maidani ko Boy? Ina maka magana kana latsa waya, don nace kanwar Uwarka ba zata zauna a cikin Gida ba ko? Anya Majeed Karuwar nan ta barka haka kuwa? Anya bata wanke ta baka kasha ba?". Da k'arfi yace "Mummy". Kallonshi tayi sosai, tana so ta gane yanayin da ya shiga cikin Seconds din da ba su wuce hamsin ba,ta karaso kusa dashi ganin hawaye a idonshi ta dan tsorata tace "Yadai Boy?" cikin sanyin jiki yace "Mummy i've not been accepted, banci test din da nayi a Dubai ba, Mummy, nayi depending kan Aikin nan, Mummy i've failed you all" be san lokacin da hawaye ya soma kwaranyo mai ba. Nan da nan Mummy ta shiga hankalinta ta tattaro Majeed jikinta, duk da tafi shi shiga tashin hankali amma sai ta fara lallashin shi ta hanyar cewa "Majeed, ba kayi failing dinmu ba, You are all i've ever wanted, ina Alfahari da kai, i'm really proud of you Boy, yanda ka tsaya ma Family dinka, ka kwantar da hankalinka, Mummy wi find a way, its Gonna be fine" da sauri Majeed ya tashi ya share hawayenshi, ya kamata ya zama karfinsu, ya yi Murmushi yace "Its gonna be fine InshaAllah, Allah ya sa Hakan yafi Alheri, kila ba Alheri bane shiyasa Allah ya kaddara ba zan samu ba, Allah ya musanya mana da abunda yafi zama Alheri" ya juya ya bar dakin, Galala ta bi bayanshi, halin Majeed na bata Mamaki, yana abu kanar yafi uban kowa sanin Allah ji wani addua, ta buga tsaki, wai Allah sa hakan ne yafi zaman Alheri, rashin samu aikin shine Alheri? Tab, har yanzu akwai kuruciya a tare da Majeed. Tashi tayi Zama be ganta ba ,dole ta tashi ta nemo musu Mafita. ***** Hello Masoyan Asali, Ga babi na sha Takwas. Put a smile on my face by Voting, and commenting line by line. #1love #ADAY #bibiliciousfreakingfans #anatare Kamata yayi ace ya kadaita kanshi a halin yanzu da zuciyarsa ke mai zafi, Samun kanshi yayi da shiga dakin Ziyada inda Najwa ke Bacci, kujera ya samu ya kafa gaban Gadon ya k'ura mata ido. Abunda ya bashi mamaki shije irin tsantsan kaman da Najwa keyi da Kanwarshi Ziyada, dama ana samun irin haka? Ba ku hada jini da mutum ba amma kaga kama har haka? How can they look this alike? Ko da yake ance kowa a duniya yana kama da wuni, so it happens. Zuciyarsa ta karkata ga rashin samun aikin da beyi ba, sosai be ji dadi ba, amma ba yanda zaiyi, Musulmi na kwarai shine wanda yake rungumar k'addararsa a duk yanda tazo mai, a fili yace "Allah ka bani ikon cin Jarabawar nan". Yana kallo Najwa ta bude ido a hankali, yayi saurin tashi tare da mata nunin ta koma bacci. Yamutsa fuska tayi tare da yunkurin tashi, yayi saurin cewa " Najwa ki koma bacci kinji?" girgiza kai tayi tare da cije baki. Sannu ya mata yana tambayan ta in kafan na ciwo, gyada kai tayi tare da digon hawaye, har ranshi take bashi tausayi. A hankali tace "Zanyi fitsari" cike da tausayawa yace "ba zaki iya tafiya ba ko?". Ta gyada kai yace " Yi hakuri ina zuwa, da sauri ya fita Najwa ta bishi da ido. Nana ya iske a dakin baccinsu, yace "Nananah, donAllah zo ki kama Najwa ki kaita toilet" Nana ta wurga mai harara tace "dazun da ka rungumeta a kirjinka fa ka fita da ita fa? Ai yanzuma sai kaje ka dauketa ka kaita toilet" ya dan rausayar da kai yace "dazun ai laluri ne, k'one kafa tayi, a sume take fa Nana, donAllah kar ki zama mara tausayi muje ki kamata" yanzun ma ai laruri ne sai kaje ka dauketa ka kaita ka jirata tayi abunda zatayi in yaso kai mata tsarki". Ranshi ya baci, ya juya ba tare da yace mata komai ba, bari yaje ya rok'i Zaineema kila ta zo ta taimaka ma Najwa. Yana fita wata zuciyar tace ma Nana, kar fa yaje ya dauketan, da sauri ta bi bayanshi da ya kara ta6a Najwa gwara ta kai zuciyarta nesa ta taimaka mata, Majeed naganin tabishi daki yaji dadi ya tsaya a waje, wata uwar Harara Nana ta buga ma Najwa sai da hanjinta suka kada, tashi Karuwa in kamaki ki shiga toilet" duk da Najwa bata san maanar kalmar 'karuwa' ba, amma tayi amanna ba kalmar arziki bace. Kamata tayi sukayi toilet, dan gayya Nana ke janta, Najwa tun cikin wando ta fara fitsarin saboda Azaba, bata ga Amfanin kamota da Nanan tayi ba, don riketa tayi kamar tana kyamarta, Najwa ta fara hawaye, tayi tsarki ta zuba ruwa a inda fitsarin ya taba, Nana ta sake kamota ta jefata kan Gado, da gayya ta kuma take kafar da ya k'onen. Najwa ta sa hannu ta gumtse bakinta da sauri gudun kar ta sake Ihu, hawayenta ya yawaita, Nana ta buga tsaki ta sursurfa mata zagi kafin ta wuce. Majeed na ganinta yayi saurin cewa "tayi ko?" Ba tare da jiran amsan Nanan ba ya sa kai dakin, Nana tayi saurin rik'oshi tace "Tace Bacci zata koma" Majeed ya dan dakata yace "Is that So?" tace "Yes" ta ja hannunshi suka shiga dakinsu. Nana na karantar damuwa a fuskar Majeed, kar dai ace ya damu da wanchan karuwar ne, gaskia ita ta gaji, daurewa dai tayi tace "My Majeed, you look worried? Don ko don yarinyar nan ne?" gabana na dukan chalugude don gudun amsar da zai bata, iska ya furzar kafin yace mata "Nana, ban ci Test din da mukayi a Dubai ba Ba su ban aiki ba". Nana ta rausayar da kai tace " shine ka damu haka? donAllah share, zan ma Dad dina Magana, zai kula da mu duka" Majeed yayi murmushin takaici ya daiyi shiru be ce komai ba, nan Nana ta fara soki burutsun ta, da ya ga zata matsa mishi sai ya mike ya shiga Toilet. Bayan Kwana Biyu. Ba laifi tana taka k'afar da kanta ba tare da an kamata ba, a cikin kwanaki biyun nan ta gama karantar Halayyen Abdulmajeed. Mutum ne mr kirkin gaske, yana da kawaici da kauda kai, yana kula da ita yanda ya kamata, ganin ana kyararta in ta fits cin abinci yasa shi dinga kawo mata Abincinta daki. Kafarta ya fara bushewa don maganin hausa ya amso mata gun wani Sarkin Baka (likitan fatar Gargajiya) Wannan Kenan. * "Maryam kin tuna Aina'u Habib?" Mummy ta ta6e baki don ta ganeta tsaf, Abokiyar Aikin Daddy ne tun shekaru 18 da suka wuce lokacin yana Koyarwa, Sosai Matar ke bata haushi, haka kurum bata mata ba, shirun da tayi ne ya fahimtar dashi ta ganeta, ya cigaba da magana, amma wannan karon hankalinshi na kan Majeed. "Abokiyar Aikina ce in the 90s, after a long time mun hadu dazun a traffic, ta tambayeka, nace mata you've grown alot har kayi aure, she was suprised, tace kayo saurin girma, ta tambayeni inda kake aiki, na gaya mata ba aikin nan, so tace ina gaya ma ka kai mata CV dinka, InshaAllah zata nemo ma Lecturing a WUDIL, don yanzu she's a Dean. Karaf Mairo tayi tace " Lecturing? Majeed din ne zaiyi lecturing? Daddy Mallamin Makaranta fa, Allah ya sauwake, kawai sai a ga Yaro yaje wani makaranta koyar da Dalibai, Yarona ya fi k'arfin wannan, so tell your Old Friend bama bukata" Majeed zaiyi magana Mummy ta dakatad da shi ta hanyat daga mai hannu, beyi shiru ba, yace "Mummy Lecturing fa, meye aibin zama Lecturer? They pay Good, atleast zamu rage ma kanmu wasu nauyin". "No Son, bama bukatar taimakon wannan Bayerabiyar, ba donAllah zata neman maka aiki ba, tun kana karami take bin Daddynka, so bama so, bamu san me take shiri a kanmu ba, besides i have plans for you, just be patient". Majeed yayi shiru, Daddy yace " Maryam--" Mummy tace "Allah Daddy Majeef ba zaiyi Lecturing ba, akwai abunda nake mai hange" Tashi Majeed yayi zai bar Dakin Mummy ta tsaidashi a hanyar cewa "Ya maganarmu, inace kafan nata ya warke? Yaushe zata tafi?" Rausayar da kai yayi yace "Mummy ki dan kara mata lokaci" kafin ta ce wani abu ya bar dakin da sauri. * Tashin Hankalinta be wuce tafiyar da Majeed yace mata zaiyi ba, taya zata rayu da Mutanen da k'irik'iri suke nuna mata tsana? Anya zata iya zama har yayi wasu kwanaki baya gidan? Amma da ta tuna kalaman Majeed inda yake ce mata "Kwantar da hankalinki zakiyi, ba dadewa zanyibba, k'anwata kawai zan dauko daga makaranta, sai in dan bincika in akwai offer din Aiki but ba dadewa zanyi ba, befi 2-3days
Chapter 37 · 0% Book details